Ko tallafin da Wike zai bai wa ‘yan PDP a Sokoto na da alaƙa da takarar 2027?

    • Marubuci, Isiyaku Muhammed
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Yanzu za a iya cewa kallo ya fara komawa sama bayan rikicin cikin gida na jam'iyyar PDP ya ɗauki sabon salo a daidai lokacin da jam'iyyar ke ƙoƙarin shawo kan matsalolin da suka dabaibaye ta.

A jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin ƙasar, wasu ƴaƴan jam’iyyar ne suka suka nuna goyon bayansu ga ministan Abuja Nyesom Wike, sakamakon shirinsa na tallafa musu da kuɗaɗe da kuma kayan abinci a ƙananan hukumomi 23 na jihar.

"Wike ya neme mu a nan Sokoto domin mu yi tafiyarsa, sannan ya ce mu kira ƙungiyoyi a duk faɗin ƙananan hukumomi 23 domin ya riƙa tallafa musu kafin lokacin zaɓe," a cewar Ahmadi Abdullahi Oil and Gas shugaban ƴan PDP da suka nuna goyon baya ga Wike.

"Wike ɗan PDP ne ko ɗan wata jam’iyyar daban? Ko a wane ɓangare yake idan dai a PDP ne za mu karɓe shi. Kuma tafiyar ta samu karɓuwa sosai," in ji shi.

A nasa jawabin, Yusuf Bunuchekehe wanda ya jagoranci shirya taron na magoya bayan Wike, ya ce "mutane da dama sun samu tallafi, kuma za a tallafa wa wasu, amma ba a ce a yi wariya ba".

BBC ta tuntuɓi sakataren yaɗa labaran PDP a jihar Sokoto, Hassan Sahabi Sanyinnlawal, wanda ya ce ba su da masaniya kan batun, kuma ba za su ce komai ba a yanzu.

Me ya sa Wike yake neman kutsawa wasu jihohin?

A watan Satumba ne Nyesom Wike ya yi barazanar rura wutar rikicin siyasa a jihar duk wani gwamna da ya sa baki a rikicin siyasa tsakaninsa da Gwamna Fubara na jihar Rivers.

Wike ya bayyana a lokacin cewa: “Ina tabbatar muku cewa matuƙar muna raye babu wanda ya isa ya ƙwace PDP daga wajenmu a Rivers. Na ji wasu gwamnoni na so su shiga rikicin domin ƙwace shugabancin su miƙa wa wani. Ina tausaya musu domin zan kunna musu wuta a jihohinsu."

Tun a lokacin ne shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP, Gwamnan Bauchi Sanata Bala Mohammed, ya mayar masa da martani cewa “babu wanda ya isa ya kunna wuta a Bauchi. Muna da isasshen ruwan kashe duk wata wutar da za a kunna mana".

Wike ya yi barazanar ce bayan yunƙurin ƙungiyar gwamnonin na goyon bayan Gwamna Fubara domin mayar masa da jagorancin jam'iyyar a Rivers bayan ɓangaren Wike ya samu nasara a kan na Fubara yayin zaɓen shugabannin PDP a jihar.

Bayan haka kuma, ana ganin da ma akwai jiƙaƙƙiya tsakanin Wike da tsohon Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal kuma sanata a yanzu, waɗanda tsofaffin abokai ne tun daga zaɓen fitar da gwanin shugaban ƙasa na jam'iyyar da aka yi a watan Mayun 2022, inda Tambuwal ya janye wa Atiku Abubakar.

Wannan matakin na Tambuwal ya sosa ran Wike, inda ya ce bai kamata a bar Tambuwal ya fito ya yi jawabin janye takararsa ba domin bayyana goyon baya ga Atiku Abubakar.

Ko tallafin Wike na da alaƙa da zaɓen 2027?

A wani ɓangaren, wasu na ganin wannan matakin na Wike na da alaƙa da shirye-shiryen zaɓen 2027.

Farfesa Kamilu Sani Fage malami a tsangayar nazarin siyasa a Jami'ar Bayero ta Kano. Ya ce: "Akwai alama Wike yana so ne gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa a PDP, don haka suna neman wanda zai mara masa baya ne daga arewa domin suna so a mayar da takarar PDP kudancin Najeriya".

Ya ƙara da cewa: "Idan an zo zaɓen na 2027 za a samu rabuwar kai, domin ƴan kudu irin su Wike za su dage sai an ba su tikiti, idan kuma ƴan arewa suka dage - kamar idan Atiku ya sake fitowa - to wannan zai kawo rabuwar kai. Idan ba sa’a aka yi ba zai iya kawo rarrabuwar ita PDP ɗin."

Farfesa Fage ya ce tun daga zaɓen 2015 ne aka fara samun haka, inda wasu ƴan jam'iyyar suka buɗe sabuwar PDP.

Ko akwai hannun APC a rikicin?

Game da zargin da wasu ke yi cewa akwai sa hannun APC, Farfesa Fagge ya ce biri ya yi kama da mutum.

"Ko da APC ba ta da hannu wajen kitsa rikicin, da alama tana da hannu wajen rura wutar rikici shi," in ji shi.

Kazalika, masanin yana ganin Wike zai iya yin nasara wajen kunna wutar da ya yi alƙawari a wasu jihohi.

"Zai iya, domin lokacin da PDP ta faɗi zaɓe a 2015, kusan duk manyanta ba su yi mata wani abin kirki ba. Shi Wiken ne ya riƙe ta har ta je zaɓe na gaba. Don haka yana da masu goyon bayansa a jihohi daban-daban. Kuma ko shakka babu kamar yadda ya je Sokoto, zai je wasu jihohin."

A game da hatsarin hakan ga PDP, Farfesa Fagge ya ce dole ne manyan da sauran ƴaƴan jam'iyyar su ɗauki mataki, domin a cewarsa tun bayan zaɓen fid-da-gwani na 2022 ne aka fara jan daga.

"Wannan al'amari babban hatsari ne ga PDP, da ma ita dimokuraɗiyyar baki ɗaya domin irin wannan rarrabe daga ƙarshe jawo fitintinu da tashe-tashenn hankula suke yi. Irin waɗannan rikice-rikicen ne suka jawo rugujewar jamhuriya ta ɗaya da ta biyu."