Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
PDP ta keɓe wa kudancin Najeriya takarar shugaban ƙasa a 2027
Babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta ware kujerar ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2027 ga yankin kudancin ƙasar.
Jam'iyyar ta tabbatar da haka ne a babban taron majalisar zartarwarta karo na 102 da ta gudanar ranar Litinin a Abuja, babban birnin ƙasar.
Haka kuma jam'iyyar ta tabbatar da Umar Iliya Damagum a matsayin shugabanta na ƙasa a hukumance.
Damagum - wanda ya shafe fiye da shekara guda a matsayin shugaban riƙo na jam'iyyar a yanzu ya zama shugaban jam'iyyar mai cikakken iko gabanin babban taron jam'iyyar na ƙasa da za a gudanar a ranakun 15 a 16 ga watan Nuwamba a birnin Ibadan na jihar Oyo.
A watan Maris ɗin 2023, PDP ta naɗa Damagum a matsayin shugaban riƙo, bayan dakatar da shugabanta na wancan lokacin, Sanata Iyorchia Ayu.
A baya-bayan nan dai an ga yadda wasu ƴan jam'iyyar suka zafafa kiraye-kiraye ga tsohon shugaban ƙasar, Goodluck Jonathan ya yi wa jam'iyyar takara a zaɓen 2027.
Haka kuma jam'iyyar ta yaba wa ƙungiyar da ta ce ƙungiyar gwamnoninta na yi tare da kwamitin amintattunta, da kwamitin gudanarwa da ƴan majalisarta na ƙasa da saura masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da gudanar da babban taron nata cikin nasara.
Jam'iyyar ta kuma ta karɓi rahoton kwamitin tsara taron wanda ya bayar da shawarar cewa:
Duka masu riƙe da muƙamai a matakin jam'iyyar da suka fito daga arewacin ƙasar za su ci gaba da riƙe muƙamansu, haka ma masu riƙe muƙaman daga kudancin ƙasar su ma za su ci gaba.
''Don haka kasancewar yankin arewacin ƙasar zai ci gaba da riƙe muƙamin shugaban jam'iyyar, kujerar takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2027, ta koma yankin kudanci'', kamar yadda sanarwar bayan taron da jam'iyyar ta fitar ta nuna.
Haka kuma taron na PDP ya zargi jam'iyyar APC, mai mulki da abinda ta bayyana da ƙwace mata jihohi ta hanyar tursasawa da maguɗi da tilastawa.
''Musamman yadda APCn ta ƙwace mana zaɓuƙan cike gurbi da aka yi a sassan ƙasar nan a baya-bayan nan'', in ji sanarwar ta PDP.
Jam'iyyar PDP ta faɗa rikici tun gabanin zaɓukan 2023 bayan da tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Aubakar ya samu nasara a zaɓen fitar da gwani na jam'iyyar.
Jam'iyyar ta PDP ta kuma zargi APC mai mulki da yunƙurin mayar da Najeriya mai bin tsarin jam'iyya guda, wani abu da ta bayyana da barazana ga tsarin dimokraɗiyya.
Daga ƙarshen taron nata PDP ta kuma saka ranar Laraba 15 ga watan Oktoba a matsayin ranar gudanar da taron majalisar zartaswarsa na gaba na 103.
APC ta goyi bayan Tinubu a 2027
Batun keɓe wa wani yanki takara na ci gaba da ɗaukar hankali a siyasar Najeriya.
A yanzu haka shugaban ƙasar da ke jam'iyyar APC, wanda shi ma ɗan yankin kudancin ƙasar ne - Bola Tinubu - tuni jam'iyyar ta ce shi za ta mara wa baya a zaɓen 2027.
A yanzu kallo ya koma kan haɗakar ADC, wadda ita ma ke da jiga-jigan ƴansiyasa dage kudanci da arewacin ƙasar, kan yankin da za ta keɓe wa takarar shugabancin ƙasar a zaɓen 2027.