Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Rashford ya amince a rage albashinsa don raba gari da Man U, Chelsea ta shiga zawarcin Nunez
Chelsea ta bi sahun Newcastle United wajen neman dan wasan Uruguay Darwin Nunez. Dan wasan gaban mai shekaru 26 ya rasa damar bugawa kungiyar Al-Hilal ta Saudiyya wasa, bayan da ta dauki dan wasan gaba na Faransa mai shekaru 38 Karim Benzema. (Chronicle Live)
Manchester City za ta biya fam miliyan 70, don siyan dan wasan bayan Ingila Tino Livramento, mai shekaru 23, daga Newcastle United. (Teamtalk)
Kwantiragin dan wasan tsakiya na Jamus Nico Schlotterbeck a Borussia Dortmund zai kare a shekarar 2027 kuma dan wasan mai shekaru 26, wanda aka alakanta da Liverpool, yana daya daga cikin manyan 'yan wasan da Real Madrid ke nema a lokacin bazara. (Mundo Deportivo)
Sunderland da West Ham suna sha'awar ɗan wasan gaban Mexico mai shekaru 24 Santiago Gimenez, wanda za a iya barinsa ya bar AC Milan. (AS Spanish)
Ana sa ran mai tsaron gidan Manchester United Altay Bayindir zai bar ƙungiyar a lokacin bazara, inda ake sa ran dan wasan na Turkiyya mai shekara 27 zai iya komawa Besiktas. (Football Insider)
Dan wasan gaban Ingila Marcus Rashford, mai shekaru 28, ya amince a rage albashinsa, sannan a rage wasu kudaden garabasa da yake samu duka dai don ganin ya bar Manchester United, sannan ya zama dan wasan Barcelona na din-din-din. (Teamtalk)
Crystal Palace za ta toshe duk wata kofa ta ganin ta hana dan wasanta Dean Henderson barin kungiyar, yayin da Tottenham da sauran ƙungiyoyi ke nemansa. Ɗan wasan mai shekaru 28, wanda ya buga wasanni huɗu a Ingila, ya kasance wani muhimmin ɓangare na nasarar Palace a ƙarƙashin Oliver Glasner. (Football Insider)
Juventus na iya shirin sayar da dan wasan tsakiya na Holland Teun Koopmeiners amma tana son akalla Yuro miliyan 30 (£26m) ga dan wasan mai shekaru 28, wanda aka alakanta shi da Galatasaray da Roma. (Tuttosport)