Yadda aka gano ƙasusuwan dabba mai shekara miliyan 100 a Nijar

    • Marubuci, Mamadou Faye
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Afrique
  • Lokacin karatu: Minti 5

Wata tawagar masu bincike da ke aiki a yankin Sahara na Jamhuriyar Nijar sun sanar da gano ƙasusuwan dabbar dinosaur wadda ta yi rayuwa sama da shekara miliyan 100 da suka shuɗe.

Wasu masu bincike 20 ne daga jami'ar jihar Chicago karkashin jagorancin Dr. Paul Sereno suka gano ƙasusuwan, kuma sun ce abu ne mai muhimmanci: zai zama ɗaya daga cikin hujjoji na ƙasusuwan wata dabba da aka gano a cikin sama da ƙarni.

A karkashin tsananin zafi da ake yi a yankin na Sahara, masu binciken suka gano sauran ƙasusuwan dabbar ta dinosaur, wadda ake ɗauka a matsayin wata dabba ta daban a tsawon ƙarni.

Tafiyar da masu binciken suka yi karkashin jagorancin masanin halittu Dr. Paul Sereno, na jami'ar Chicago, ya sake haifar da muhawara kan wanzuwar dabbar dinosaur a Afirka kuma ya bayyana abin da ya daɗe a ɓoye a cikin Saharar.

A tsakiyar Sahara da babu kowa...

Tawagar masu binciken sun shafe tsawon kwanaki suna yawo cikin Sahara ba tare da sun san inda za su nufa ba, ga ƙura da ƙishirwa - sai dai ba su sani ba a ce akwai babban abin da za su gano a gaba.

A 2019, sun koma Jamhuriyar Nijar domin bincike a wani wuri da aka yi musu bayani a kai.

A lokacin ne wani abu da suka gamu da shi ya so kawo musu cikas.

"Wani mutun ne ya shiga sansanin mu. Ya yi kama da mutum-mutumin ƴan kabilar Tuareg. Yana ɗauke da adda a bayansa kuma yana zaune kusa da wata mota ƙirar Honda. Yana magan da yaruka daban-daban. Ya faɗa mana cewa zai kai mu wani wuri mai nisa," a cewar Dr Paul.

Ba tare da wata-wata ba, tawagar ta aminta da shi. Sun yi ta keta sahara na tsawon kwana ɗaya da rabi har mai ɗin su ya kusa kare wa. Daga karshe, mutumin ya jagorance su zuwa wurin da ƙasusuwan suke a tsakiyar Sahara.

"Muna da sauran rabin sa'a kafin nan muka juya don tsira," kamar yadda mai binciken ya bayyana. Masana kimiyyar sun yi aiki cikin matsi, inda suka yi ta kwan-gaba kwan-baya domin gano wasu kasusuwa da kuma gane wurin da suke.

Bayan komawa ɗakin gwaje-gwaje, sun cika da mamaki: sun gano cewa ƙasusuwan dabbar dinosaur ne wadda ta yi rayuwa sama da shekara miliyan 100 da suka shuɗe.

Gano sabon na'uin halittu

Lokacin da harkoki a duniya suka tsaya cik a 2019 sakamakon annobar korona, hakan ya shafi binciken da Dr. Paul da tawagarsa ke yi inda suka dakata har na tsawon shekara biyu.

"Daga karshe lokaci ya zo da muka sake haɗa kayanmu don komawa bincike," in ji Paul. Ya ce a lokacin burinsu shi ne su koma don tattara waɗannan ƙasusuwa son ransu.

Ba su daɗe da komawa ba suka fara gano ƙasusuwan. "Cikin ƙasa da sa'a ɗaya da isar mu, wani ya zo yana gudu a gare ni yana cewa: 'Ya kamata ku ga wannan abu!...kamar yadda Paul ya tuna.

Daga nan farin ciki ya fara rufe su. Sa'o'i biyu bayan haka, wani mai bincike ya gano wani ƙashi a cikin ƙasa. "Ya tambaye ni mene ne. Ƙashin dabbar ta dinosaur ne. Mun yi matukar kaɗuwa a lokacin,"in ji shugaban masu binciken.

"Babu wanda ya taɓa ganin irin ƙashin," in ji shi.

Masu binciken sun ɗauki hotunan ƙasusuwan ta kowane ɓangare domin kafa hujja kan bincikensu.

Tafiya zuwa cikin Sahara

Wannan sabon na'ui na dabbar dinosaur da aka gano a saharar Nijar za ta taimaka wajen ƙara ilimi irin na'uin dabbobin da ake da su.

A cewar Paul, dabbar ta fi kama da wasu dabbobi maimakon waɗanda ke rayuwa a cikin ruwa. Tsawonsa ya kai mita 12u, kuma yana da damar afka wa cikin ruwa da kuma a fili," in ji shi.

Dabbar ba ta iya iwo sosai ba a cikin ruwa, ba kamar yadda wasu bincike suka nuna ba. "Ba ta iya yawo sosai a cikin ruwa ba kamar sauran dabbobi, tana bin koguna inda take cin kifaye a matsayin abincinta.

Binciken da aka gano a Nijar ɗin ya sha bamban da wanda aka yi a tarihi a arewacin Amurka.

Ga masu binciken, wannan farawa ne kaɗai. "Wannan shi ne na farko a cikin dogon bincike kan ɓacewar dabbar a duniya," in ji shi.

Me ya sa binciken ke da muhimmanci?

Ga Dakta Paul Sereno, binciken ya wuce na ɓurbushin halittu kaɗai. Yana ba da labarin wata tafiyar binciken kimiyya mai muhimmanci - kuma ya buɗe sabon babi a tarihin dabbar dinosaur.

Mai binciken ya bar Ingila tare da tawagarsa a cikin wata tsohuwar mota ƙirar Land Rovers, inda suka nufi wani yanki mai haɗari a duniya. Sai dai balaguron da zai gano wani abu mai muhimmanci.

"Kamar yadda za ku iya gani a cikin hotunan da muka ɗauka, ina son motar sosai kuma na kasance ina lallaɓa ta tsawon shekara 30. Ita ma kamar dinosaur suke," ya faɗa cikin barkwanci. Motar ta kai mu zuwa cikin Sahara da kuma dawo da mu ba tare da an samu matsala ba

Sun fara tashi ne daga birnin Southampton da ke Ingila, inda suka isa saharar Nijar - wani wuri da yake ganin ba a yin bincike a cikinsa yadda ya kamata.

"A farkon rayuwata na gano wani abu ɗaya: yankin Sahara shi ne wuri ɗaya da ya rage da a ba yi bincike kan dabbobin dinosaur da ke cikinsa ba," in ji shi.

Yayin binciken, jami'an sun cire ƙasusuwa kusan tan 55 daga tsakiyar Sahara. Wanda kuma shi ne irinsa na farko a yankin da ba shi da ababen more rayuwa.

Amma ga Sereno, abu mafi mahimmanci shi ne. "Har yanzu akwai abubuwa da yawa da ya kamata a yi bincike a kai. Muna matakin farko na gano yadda dabbobin dinosaur na Afirka suke," ya faɗa cikin farin ciki.