Wane ne Alireza Aarafi, mai riƙon muƙamin jagoran Iran?

    • Marubuci, Masoud Azar
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC
  • Lokacin karatu: Minti 4

Hukumomin Iran sun sanar da Alireza Aarafi, wanda wakili ne a Majalisar Magabatan ƙasar, domin ya jagoranci majalisar tafiyar da mulkin riƙon-ƙwarya na ƙasar.

Bayan tabbatar da rasuwar Ali Khamenei a ranar 29 ga watan Maris, za a kafa majalisar riƙon ƙwarya ta ƙasar, bisa dogaro da sashe na 111 na kundin tsarin mulkin ƙasar, wadda za ta ƙunshi shugaban ƙasa da babban alƙalin alƙalai da kuma wani wakili daga Majalisar Magabatan ƙasar.

Bayan sanar da Mista Aarafi a matsayin mamban wannan majalisa, ana sa ran mutanen uku ne za su karɓi ragamar tafiyar da lamurran ƙasar har sai majalisar masana ta ƙasar ta sanar da sabon jagoran addinin ƙasar.

Sashe na 111 na kundin tsarin mulki ya bayyana cewa, daga lokacin rasuwar jagoran addini zuwa lokacin da Majalisar Masana za ta sanar da sabon Jagora, Majalisar wasu mutane guda uku ne za su tafiyar da ayyukan ofishin Jagora.

Wakilan wannan majalisa su ne Shugaban ƙasa, da Babban alƙalin ƙasa da kuma wakilin Majalisar Magabata wanda Majalisar lura da buƙatun gaggawa ke zaɓa.

Sai dai, wannan Majalisa ta Mutane uku ba ta da cikakken iko, kuma tana buƙatar amincewar kashi uku cikin huɗu na Majalisar lura da buƙatun gaggawa kafin aiwatar da abubuwa kamar haka:

  • Yanke hukunci kan manufofin gwamnati
  • Sanar da batun yin ƙuri'ar jin ra'ayi
  • Ayyana yaƙi ko tsagaitawa
  • Tsige shugaban ƙasa
  • Cirewa ko naɗa babban kwamandan dakrun juyin juya hali ko shugabannin hukumomin tsaro ko na soji

Kasancewar an kashe babban kwamandan rundunar juyin juya halin ƙasar, da shugaban rundunar tsaro ta ƙasar da kuma da dama daga cikin manyan hafsoshin sojin ƙasar, ana sa ran majalisar shugabancin ta riƙon ƙwarya za ta riƙa zartar da manufofi ne ta hanyar samun amincewar kashi uku bisa huɗu na wakilan majalisar ƙasar.

Wasu kafafen yaɗa labarai na ciki da wajen ƙasar, ciki har da jaridar New York Times cewa an samar da "mataki huɗu na magadan jagororin" ƙasar, sai dai kafafen yaɗa labarai da ke kusa da gwamnatin ƙasar sun bayyana lamarin a matsayin "farfagandar yaƙi."

Wane ne Alireza Aarafi?

Bayanai daga kafafen yaɗa labaran Iran sun ce an haifi Alireza Aarafi ne a shekara ta 1955 a birnin Meybod da ke lardin Yazd.

Mahaifinsa Mohammad Ebrahim Aarafi shahararren malami ne a lokacin rayuwarsa, wanda ya yi adawa da jagorancin sarki Pahlavi, kuma yana da alaƙa ta ƙut da ƙut da malaman da ke kusa da Ruhollah Khomeini.

Mahaifiyarsa ƴa ce ga Sheikh Kazem Malek Afzal Ardakani.

Alireza Aarafi ya yi karatunsa na farko-farko ne, kamar ilimin Qur'ani da adabi da harkar shari'a a wurin mahaifinsa da kuma wasu malamai.

Ya koma birnin Qom a shekarar 1960, sannan bayan kammala karatun elemantare ya fara karatun koyon maluntan addini a shekarar 1977.

Bayan kammala matakin farko, sai ya fara tafi wurin manyan malaman shi'a daban-daban ya yi karatun shari'a, ciki har da Morteza Haeri, da Mohammad Fazel Lankarani, da Hossein Vahid Khorasani, da Javad Tabrizi, da Ali Meshkini, da kuma Hassan Hassanzadeh Amoli, sannan ya yi karatun falsafa a wurin Mohammad Taqi Misbah Yazdi.

Ya kuma yi karatun harkokin addini a tsangayoyi da jami'o'i kamar Allameh Tabataba'i da Tarbiat Modarres.

Alireza Aarafi ya kasance cikin harkokin siyasa tun yana matashi, kuma ya bi sahun mahaifinsa wajen adawa da gwamnatin Pahlavi.

An kama shi tare da ɗaure shi a gidan yari tun yana da shekara 16.

A shekarar 1979, an kafa wata ƙungiyar mai lura da ɗalibai waɗanda ba ƴan asalin ƙasar Iran ba a cibiyar karatun addini ta Qom.

Wadda daga baya ƙungiyar ta zama 'Cibiyar Kimiyyar Musulunci ta Duniya', inda ta koma ƙarƙashin kulawar jagoran addini na Iran.

A shekara ta 2002 ne aka naɗa Alireza Aarafi a matsayin shugaban cibiyar bisa amincewar Ayatollah Ali Khamenei.

Yana daga cikin iyayen jami'ar Kimiyyar Qur'ani da ilimi.

Aarafi ya kasance limamin Juma'a na Meybod tun daga shekara ta 1992, kuma an naɗa shi limamin juma'a na Qom a 1994.

Shi mamba ne a ƙungiyar malaman cibiyar horas da malaman addini ta Qom.

Mista Aarafi ya yi takarar shiga majalisar ƙwararru ta Iran a zaɓen shekara ta 2015 domin wakiltar mazaɓar Tehran, sai dai bai samu nasara ba.

Ya sake gwada yin takara a zaɓukan tsakiyar zango, inda ya samu nasara, domin wakiltar Tehran.

Ya samu shiga majalisar ne karon farko daga Tehran a zaɓen da aka yi a watan Maris na 2023, inda ya samu ƙuri'a 888,618.

A ranar 14 ga watan Yulin 2019 aka naɗa Mista Aarafi zuwa Majalisar Magabata bisa amincewar Ali Khamenei.

Daga Majalisar Masana zuwa jagoran riƙo

A shekarun baya-bayan nan ne mutane suka fara sanin Alireza Aarafi, a baya idan za a ambace shi a labarai, akan kira shi da laƙabin "Hujjat al-Islam", amma a yanzu za a riƙa masa laƙabi da "Ayatollah".

Alireza na cikin mutanen da Ali Khamenei ya amince da su kuma yana cikin na kusa da shi. Wannan karɓuwa da ya samu a wurin jagoran addinin ta sanya darajarsa ta riƙa ɗagawa, har ya kai ga inda ake ambaton sunansa a matsayin wanda zai iya gadon Ali Khamenei.