Liverpool ta nace wa Murillo, darajar Osimhen ta lunka

Lokacin karatu: Minti 1

Rahotannin da ke cewa Jurgen Klopp zai bar muƙaminsa a Kungiyar Red Bull karya ne, a cewar shugaban ƙungiyar Oliver Mintzlaff. (Sky Sports Germany - in German)

Liverpool ta nace kan ɗanwasan Nottingham Forest da Brazil mai shekara 23 Murillo, kodayake Chelsea ce kan gaba. (Teamtalk)

Ɗanwasan gaba na Serbia Dusan Vlahovic ya fi son zuwa Barcelona idan yarjejeniyarsa ta kawo ƙarshe a Juventus, kodayake Tottenham Hotspur da Chelsea na ci gaba da farautarsa. (Teamtalk)

Arsenal da Manchester City na nazari kan ɗanwasan baya na Atalanta Honest Ahanor. Chelsea ma na son ɗanwasan na Najeriya. (Caught Offside)

Liverpool da Manchester United ba za su iya biyan kuɗin da Wolves ta nema ba fam miliyan 50 kan matashin ɗanwasan Ingila Mateus Mane. (Football Insider)

Al Ahli ta Saudiyya na neman ɗanwasan gaba na Brentford Ivan Toney, amma ɗanwasan na Ingila mai shekara 29 ya fi son ya koma gasar Premier. (Talksport)

Ɗanwasan gaba Nicolas Jackson na shirin komawa Chelsea. Ɗanwasan na Senegal na ke taka leda a Bayern Munich a matsayin aro, amma ƙungiyar ta Bundesliga na son sayensa. (CFBayernInsider)

Napoli ta saka wani adadin kuɗi a yarjejeniya ɗanwasan gaba na Najeriya Victor Osimhen lokacin da ya koma Galatasaray wanda ke nufin idan za a sayar da shi ga wata kungiyar Italiya sai an biya fam miliyan 60. (Gazzetta dello Sport - in Italian)