Me ya sa ƴan Somaliland ke matuƙar ƙaunar Donald Trump?

'Yan mata uku sanye da tufafi masu launuka daban-daban dauke da tutar yankin Somaliland - a Hargeisa, 2018

Asalin hoton, AFP

    • Marubuci, Mary Harper
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Horn of Africa analyst
  • Lokacin karatu: Minti 5

Mutane da dama a yankin Somaliland sun yi amannar cewa Amurka a ƙarƙashin mulkin Shugaban Ƙasa Donald Trump za ta zama ta farko da za ta bayyana ta a matsayin ƙasa mai ƴanci.

Yankin ya ɓalle ne tare da ayyana ƴanci a shekarar 33 bayan ƙasar Somalia ta faɗa cikin yaƙi - inda tun daga lokacin take ta ƙoƙarin tsayuwa da ƙafarsa.

"Donald ne zai ƙwatar mana ƴancinmu. Mutum ne mai basira. Allah ya taimaki Amurka," in ji wata ɗalibar jami'a, Aisha Ismail, wadda ta min magana muryarta na rawa saboda murna.

Mun yi magana ne da ita daga Hargeisa, babban birnin Somaliland - birni mai nisan kilomita 850 daga birnin Mogadishu, babban birnin ƙasar Somalia.

Amma ita gwamnatin Somalia tana ganin Somaliland wani yanki ne ƙasarta.

"Ba na tunanin Donald Trump ya san inda Somalilan take, kuma ba na tunanin zai damu da inda take," in ji Abdi Mohamud, wani masanin ƙididdiga a Mogadishu.

Wasu manyan mutane a jam'iyyar Republican na Amurka suna goyon bayan fafutikar, ciki har da ɗanmajalisar Amurka Scott Perry, wanda a watan jiya ya gabatar da ƙudurin buƙatar Amurka ta amince da Somaliland a hukumance.

A daftarin tsare-tsaren mulkin Trump na biyu mai suna Project 2025, yankunan Afirka biyu - Somalilan da Djobouti sun samu shiga.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Amma yadda aka ƙarƙare batun yankin na Afirka a shafuka biyu kacal a kundin mai sama da shafuka 900 ya nuna cewa nahiyar ba ta cikin lissafinsa sosai.

Haka kuma babu tabbacin gwamnatin mai shigoza ta yi amfani da tsare-tsaren kundin ɗari bisa ɗari. Amma dai a zahiri yake Amurka ta fara sauya tunaninta game da Somaliland.

Somalia na cikin ƙasashen Amurka ta yi asara mafi muni, wanda yake cikin munanan asara da ƙasar ta yi tun daga shekarun 1990s, inda da aka ja gawarwakin sojojin Amurka 18 a titin Mogadishu bayan wasu mayaƙa na ƙasar sun harbo helikwaftar Amurka.

Yaƙin mai suna "Black Hawk Down" na cikin yaƙe-yaƙen da Amurka ta yi asarar sojoji mafiya yawa tun bayan yaƙin Vietnam.

"Duk wani yunƙurin tabbatar da ƴancin Somaliland, ba cin fuska ba ne kaɗai ga ƴancin Somalia, har ma da yunƙurin jefa yankin cikin ruɗani," in ji ƙaramin ministan harkokin wajen Somalia, Ali Mohamed Omar.

Omar ya kuma bayyana fargabar da suke da ita cewa za a iya maimaita yunƙurin gwamnatin Trump na farko na janye sojojin Amurka da suke yaƙi da mayaƙan al-Shabbab, wadda al-Qaeda ta bayyana da ɓangarenta mafi girma.

A ƙarƙashin mulkin Joe Biden, an tura kusan sojojin Amurka 500 zuwa Somalia, inda suke aiki na musamman, tare da horar da dakarun ƙasar na musamman, Danab, kuma sun taimaka wajen wanzar da zaman lafiya fiye da asalin sojojin ƙasar ta hanyar fatattakar al-Shabab.

Sojojin Amurka na da wani sansani a Baledogle da ke arewa maso yammcin Mogadishu, kuma daga wajen suke luguden wuta kan mayaƙan masu ikirarin jihadi.

"Janye su zai jawo tsaiko a yaƙi da matsalar tsaro, wanda ba Somalia kaɗai zai shafa ba, har ma wasu sassan Afirka," in ji Omar.

Sojoji a bakin aiki, ciki har da mace guda, da ke karkashin rundunar Danab a yankin Somaliland,

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Amurka ce take horar da dakarun Danab na Somalia masu yaƙi da mayaƙan al-Shabbab

Wasu ƴan Somalia suna bayyana min cewa suna cikin fargabar, wadda har take hana su barci.

Turkiyya ta yi ƙoƙarin samar da maslaha, amma yadda Somalia ta shiga yarjejeniyar $600,000 (£492,000) a shekara da wata cibiyar kamun-ƙafa da ke Washington na BGR Group ya nuna cewa ƙasar ba ta da kwanciyar hankali kan gwamnatin Trump mai kamawa.

Wani na gaba-gaba a cikn ƴan Republican da ke bibiyar harkokin da suka shafi Afirka, musamman batun Somalia, Joshua Meservey, ya ce, "batun Somaliland a Amurka yana jan hankali. Ina tunanin lallai za a tattauna batun ƴancin ƙasar," in ji shi.

Haka kuma fitattun ƴan Afirka da suke cikin gwamnatin Trump, kamar tsohon mashawarcin shugaban ƙasar kan harkokin Afirka, Tibor Nagy da wakilinsa na musamman a Afirka, Peter Pham, duk suna cikin masu goyon bayan tabbatar da ƴancin Somaliland.

Waɗanda suke goyon bayan ƴancin Somaliland suna cewa Somaliland tana yanki da ke da muhimmanci ga tattalin arziki da tsaron Amurka.

Mr Meservey ya ce ya kamata a ba ƴankin ƴanci saboda amincewa da tsarin dimokuraɗiyya.

Haka kuma tana kusa da ɗaya daga cikin manyan gaɓar tekun da aka fi hada-hada.

Wataƙila mayaƙan ƙungiyar Houthi ta Yemen masu samun goyon bayan Iran sun maye ƴanbindigar Somalia wajen janyo tsaiko a hada-hadar da ke gudana a tekun, amma hare-haren na cikin manyan ƙalubalen da harkokin kasuwanci na duniya ke fuskanta.

Haka kuma yadda ƙasashen suke rububin kafa sansani a yankin tekun abun damuwa ne ga Amurka, wadda ta kafa babbar sansanin sojinta a nahiyar a Djibouti a 2002.

Rasha na yunƙurin ƙara ƙarfi a yankin Port Sudan, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa tana amfani da mayaƙan Eritrea na Assab domin yaƙi da Houthi.

Ita ma Turkiya, babban sansaninta yana ƙasar Somalia.

Sannan yaƙi da faɗaɗa iko da China ke yi a Afirka na cikin abubuwan da ke muhimmanci ga Trump.

Amurka ta zargi China da sa baki a harkokinta a Djibouti, wanda hakan ya sa za ta so ta koma wani yankin.

Kuma yankin gaɓar teku na Berbera, wanda ko dai kana masa kallon yankin Somaliland da Somalia ne, zai iya zama inda Amurka ke hanƙoron komawa.

A gwamnatin Biden, manyan jami'an gwamnatin Amurka, ciki har da shugaban hukumar Africom ya kai ziyara a gaɓar Berbara mai faɗin kilomita 4, wanda tarayyar Soviet ce ta gina a zamanin yaƙin Cold War.

A shekarar 2022, an yi gyara a dokar ɓangaren tsaron Amurka, inda Somaliland ta samu shiga.

Donald Trump dauke da murmushi a fuskar shi, ya nuna babban dan yatsansa da ke alamanta amincewa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Donald Trump zai iya amincewa da ƴancin Somaliland idan ya ga akwai wata damar kasuwanci a cikinta

Ƴan Republican da suke goyon bayan amincewa da ƴancin Somaliland sun bayyana cewa ƙasa ce da za a ƙaru da ita, inda suke amfani da hakan domin jan hankalin Trump.

Wani masani diflomasiyya ɗan asalin Somaliland mazaunin Amurka ya ce, "nasarar ta danganta ne da yadda suka tallata ƙasar a wajen Trump."

Haka kuma amincewa da Somaliland zai ƙara ɓata tsakaninsa da Somali, wadda take cikin ƙasashen da ya bayyana da marasa daraja a shekarar 2018.

Wani malamain makaranta a Amurka, wanda yake bibiyar harkokin Somalia na gomman shekaru, Ken Menkhaus, ya ce, "lallai akwai yiwuwar za a ga sauyi game da tsare-tsaren Amurka kan Somalilan da Somalia."