Yadda ƴan Somaliya ke amfani da manhajar koyon karatu

..

Asalin hoton, Sahamiye Foundation

    • Marubuci, Sara Monetta
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
k

Asalin hoton, Sahamiye Foundation

Hodan Artan tana ɗinke wasu tsummokara da take amfani da su a saman rufin gidanta.

Tana aiki ne a matsayin mai share-share a Hargesia, babban birnin yankin Somaliland.

Kasancewar kuɗin da take samu ƙalilan ne, muhallin da matar, mai shekara 23 za ta iya samu kawai shi ne wani ɗakin ƙasa da aka yi wa rufi da tsumma.

Ita da ɗiyarta ne ke rayuwa a wannan ɗaki.

A baya, ba ta taɓa tunanin cewa tana da wani buri a nan gaba ba.

"Lokacin da nake ƙarama, ban samu damar zuwa makaranta ba, su ma iyayena ba su yi karatu ba." In ji ta.

Hodan ba ta taɓa koyon karatu ko rubutu ba.

Amma a ƴan watannin da suka gabata ta samu labarin wata manhaja da ake kira Daariz, wadda bayanai suka nuna cewa mutane sama da 410,000 ne suka ilimantu ta hanyar mahajar a ƙusurwar Afirka.

Bayan samun ƙwarin gwiwa daga ƙawayenta, Hoda ta rinƙa koyon abubuwa daga manhajar a lokacin da ba ta da ayyuka da yawa - sai ga shi a cikin wata biyu kacal ta koyi abubuwa da dama: yanzu tana iya karantawa da kuma fahimtar labarun da aka rubuta da harshen Somali.

..

Asalin hoton, Sahamiye Foundation

Bayanan hoto, Hodan (ta biyu daga hagu) tare da ƙawayenta a wani shagon sayar da litattafai a garin Hargesia domin yin karatu

Akwai irin waɗannan labarai da dama a Somaliland, wani yanki da ya daɗe yana fama da matsalar rashin ilimi.

A shekarar 1991 ne yankin ya ayyana ƴancin kai a lokacin da yake fama da yaƙin basasa.

Ƙasashen duniya dai ba su amince da yankin a matsayin ƙasa ba, sai dai yana da zaɓaɓɓiyar gwamnatinsa kuma yankin ya samu kwanciyar hankali fiye da sauran kasar Somalia.

Matsalolin da yaƙi ya haifar, kamar rashin kayan more rayuwa da fari sun sa yankin ya zama ɗaya daga cikin yankunan da ilimi ya yi ƙaranci sosai a duniya.

g

Asalin hoton, Sahamiye Foundation