Ƴan ciranin Amurka na fatan masu laifi kaɗai Trump zai kora daga ƙasar

Tawagar Donald Trump ta ce tun farko za a mayar da hankali ne kan kare lafiyar jama'a da kuma masu barazana ga tsaron ƙasa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tawagar Donald Trump ta ce tun farko za a mayar da hankali ne kan kare lafiyar jama'a da kuma masu barazana ga tsaron ƙasa
    • Marubuci, Bernd Debusmann Jr da Angélica María Casas
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 7

Gabriela ta shiga Amurka fiye da shekaru 20 da suka gabata, tana haki a ƙarƙashin tarin masarar da ke cikin motar ƴan fasa-ƙwauri.

Yanzu ma'aikaciyar gida ce a Maryland, ƴar kasar Boliviar tana ɗaya daga cikin aƙalla bakin haure miliyan 13 da ba su da takardun izini da ke zaune a Amurka - wannana adadin ya haɗa da waɗanda suka shiga Amurka ba bisa ka'ida ba, ko kuma waɗanda suka wuce wa'adin biza ko kuma suna da matsayin kariya don gujewa kora.

A duk faɗin Amurka, baƙin haure kamar Gabriela suna kokawa da abin da alƙawarin gwamnatin Trump mai zuwa na gudanar da korar jama'a ke iya nufi ga makomarsu.

A cikin hirarraki sama da goma sha biyu, bakin haure da ba su da takardun izini sun ce batu ne da ake tattaunawa mai zafi a cikin al'ummominsu da ƙungiyoyin WhatsApp da kuma shafukan sada zumunta.

Wasu, kamar Gabriela, sun yi imanin cewa ba zai shafe su ba ko kaɗan.

"Ba na da wata fargaba," in ji ta. " Masu laifi ne za su damu da hakan. Ina biyan haraji, kuma ina aiki."

Ta kara da cewa "A kowane hali, ba ni da wasu takardu." "[To] ta yaya za su san da ni?"

A lokacin yaƙin neman zaɓen da batun bakin haure ya yi tasiri a matsayin babban abin da ke damun masu kaɗa ƙuri'a a Amurka, Trump ya sha yin alƙawarin korar baƙin haure baki ɗaya daga ƙasar Amurka tun daga ranar farko da ya hau kan karagar mulki idan zai koma kan kujerar shugabancin ƙasar.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai kusan makonni biyu bayan nasarar da ya yi a zaɓen, har yanzu ba a san haƙiƙanin yadda waɗannan ayyukan yaki da bakin hauren za su kasance ba.

Zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya dage cewa kashe kuɗi ba zai zama matsala ba, amma masana sun yi gargaɗin cewa alƙawuran nasa na iya fuskantar ƙalubalen kuɗi da kuma dabarun aiwatar da su.

Sabon zababben jagoran tsaron kan iyaka Tom Homan, ya ce ƴan ciranin da ba su da takardun izini da ake ganin su ne masu barazana ga tsaron ƙasa ko kuma ga lafiyar jama'a za a fi bai wa fifiko. Kuma ya ba da shawarar kai hare-hare a wuraren aiki - tsarin da gwamnatin Biden ta dakatar - na iya dawowa.

Da yake magana da Fox News a ranar Asabar, tsohon muƙaddashin daraktan kula da shige da fice da kwastam a wa'adin mulkin Trump na farko ya ƙalubalanci ra'ayin cewa "waɗanda ke tabbatar da bin doka su ne miyagu kuma waɗanda suka karya doka su ne waɗanda aka muzgunawa".

"Wane ɗan majalisa ne, wane gwamna ko wane magajin gari ne ke adawa da kawar da barazanar tsaron jama'a daga cikin al'ummarsu?" Ya tambaya, ya ƙara da cewa sabuwar gwamnatin za ta “bi umarnin da jama’ar Amurka suka ba shugaba Trump”.

Korar ƴan cirani da hukumomin Amurka ke yi ba wani sabon abu ba ne. Fiye da mutane miliyan 1.5 ne aka kora a ƙarƙashin Shugaba Joe Biden, ban da miliyoyin da aka juya daga kan iyaka cikin hanzari yayin barƙewar cutar Korona.

A cikin shekaru takwas na gwamnatin Barack Obama - wanda wasu suka kira "babban mai korar jama'a" - an kori kimanin mutane miliyan uku, tare da mayar da hankali kan maza marasa aure daga Mexico da ake iya kora cikin sauƙi daga yankunan kan iyaka.

Shirye-shiryen da Trump ya yi alkawarin aiwatarwa, suna da yawa kuma suna da tsauri, gami da ayyukan tsanantawa a yakunan Amurka da ke nesa da kan iyaka. Har ila yau, jami'ai na nazarin yin amfani da jami'an tsaron ƙasa da kuma jiragen soji wajen tsare mutane kafin daga baya a kore su.

JD Vance, abokin takarar Trump kuma mataimakin shugaban ƙasa mai jiran gado, ya ce ana iya "farawa" da korar mutane miliyan ɗaya.

Duk da haka, wasu bakin haure da ba su da takardun izini suna ganin za su ci gajiyar shugabancin Trump maimakon a kore su.

"Yawancin ƴan asalin yankin Latin Amurka, waɗanda ke da damar kaɗa ƙuri'a, sun yi haka ne saboda suna ganin shi [Trump] zai iya inganta tattalin arziki. Hakan kuma zai yi mana kyau sosai," in ji Carlos, wani ɗan ƙasar Mexico da ba shi da takardun izini da ke zaune a birnin New York. Ɗansa ɗan ƙasar Amurka ne.

A cewar ƙungiyar Kula da Shige da Fice ta Amurka - wata ƙungiya ce mai zaman kanta wadda ke gudanar da bincike da kuma bayar da shawarar yin garambawul ga tsarin shige da fice na Amurka - akwai Amurkawa sama da miliyan biyar da aka haifa ga iyayen da ba su da takardun izini kuma suna da tsaron shaidar zama ƴan ƙasar Amurka.

Carlos ya ce yana da damuwa kaɗan game da fadawa hare-haren jami'an shige da fice. Sai dai wannan fargabar na ɗan yin sauƙi idan ya yi tunanin yiwuwar samun ingantacciyar tattalin arziki ƙarƙashin Trump.

"Ana iya kasancewa cikin zaman ɗar-ɗar a cikin al'ummominmu a yanzu, amma damuwa ba ita ce mafita ba," in ji shi. "Abin da ya fi dacewa a yi shi ne guje wa shiga cikin matsaloli da kuma aikata laifuka."

Alƙawuran korar baƙi sun kasance wani muhimmin ɓangare na yaƙin neman zaɓen Donald Trump na 2024 - kuma hakan ya bayyana a babban taron jam'iyyar Republican a watan Yuli

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alƙawuran korar baƙi sun kasance wani muhimmin ɓangare na yaƙin neman zaɓen Donald Trump na 2024 - kuma hakan ya bayyana a babban taron jam'iyyar Republican a watan Yuli

Akwai wasu da yawa da ba sa tarayya cikin wannan kyakkyawar fata, kuma suna rayuwa cikin fargaba.

Daga cikinsu akwai wani mazaunin California Eric Bautista, wanda ke cin gajiyar shirin da ya daɗe yana ba da kariya daga korar waɗanda aka shigo da su Amurka ba bisa ƙa'ida ba tun suna yara.

Yana da shekaru 29, Mista Bautista ba ya iya tuna wasu abubuwa kan rayuwarsa a Mexico, ƙasar da aka haife shi kuma ya bar ta yana da shekaru bakwai.

A cikin shekaru huɗu da suka gabata, ya koyar da tarihin Amurka ga daliban makarantar sakandare - ciki har da cikakkun bayanai kan yadda ƴan cirani suka riƙa kwararowa daga Italiya da Ireland da China da Japan da Mexico kuma suka zauna a ƙasar, inda galibi suka fuskanci kyamar baƙi.

"Bana tunanin na taɓa jin yadda na ke ji yanzu, ko da bayan na shafe shekaru sama da 20 a nan," Mista Bautista ya shaida wa BBC. “Ina jin kamar mun kai wani matsayi, na sabon salon kishin ƙasa kamar wadanda nake koyarwa.

"Muna fuskantar makoma mai cike da fargaba da kuma rashin tabbas."

Masu fafutuka da masana harkokin shari'a sun ce babu tabbacin cewa ƴan ciranin da ba su da takardu da ba a taɓa samunsu da laifi ba ba za su shiga cikin tarkon yunƙurin korar.

Aaron Reichlin-Melnick, darektan tsare-tsare a ƙungiyar Shige da Fice ta Amurka, ya ce ya hango samun ƙari a adadin abin da ake kira “collateral arrests” - kalmar da aka yi amfani da ita a gwamnatin Trump ta farko don bayyana ƴan ciranin da aka yi wa kamun kazan kuku yayin aiwatar da doka duk da cewa watakila ba su ne ake hari ba tun asali.

"Bari mu ce suna bin wani da ya taɓa aikata laifi, kuma mutumin yana zaune ne a wani gida tare da wasu mutane huɗu (marasa takardun shaida)," in ji shi. "Mun ga gwamnatin Trump ta farko, za su kuma kama har da waɗancan mutanen."

A cikin wata hira da aka yi a CBS cikin kwanakin nan, an tambayi Homan game da wani yanayi da zai iya yiwuwa wani aikin da ke harin waɗanda suka aikata laifuka ya rutsa da wata kaka.

Da aka tambaye ta ko za a kore ta, Homan ya amsa "ya danganta".

''Alƙali ne zai yanke hukunci," in ji shi. "Za mu cire mutanen da umarnin alkali ya kora."

Kamawa da yuwuwar korar irin wadannan mutanen na iya zama alamar ficewa daga tsarin gwamnatin Biden, wadda ta mai da hankali kan barazanar tsaron jama'a da korar mutane jim kadan bayan kama su a kan iyaka.

Yayin da Homan kwanan nan ya yi watsi da shawarwarin da ke cewa za a iya "afkawa unguwanni" ko kuma kafa manyan sansanonin tsare mutane, farashin hannayen jari na kamfanonin da ke da hannu wajen gina wuraren tsare mutane ya yi sama da kashi 90% tun bayan zaɓen. Sun haɗa da kamfanonin gidan yari na GEO Group da CoreCivic.

Baƙi ba su da takardun aiki suna aiki a ɓangarorin tattalin arzikin Amurka da dama- daga filayen noma zuwa ɗakunan ajiya da wuraren gine-gine.

Mista Reichlin-Melnick ya ce kai farmaki irin waɗannan wuraren aikin na iya haifar da kamen kan mai uwa da wabi.

"Ba na jin cewa kasancewa mutumin da ba shi da wani laifi [wanda] ke biyan haraji yana kare kowa," in ji shi. "Daya daga cikin abubuwan farko da Trump zai yi shi ne kawar da abubuwan da gwamnatin Biden ta sanya a gaba. Kuma mun ga cewa idan ba a ba da fifiko ba, za su hari duk wanda ya fi saukin kamawa."

Yiwuwar zama "mafi sauƙin kamawa" ya damu yawancin ƴan ci-rani - musamman waɗanda suka fito daga iyalai waɗanda doka ta bambamta a kansu. Babban abin fargaba a gare su shine lamarin da zai sa a raba su da juna.

Brenda, ƴar shekaru 37, haifaffiyar Mexico a Texas, a halin yanzu tana samun kariya daga kora amma mijinta da mahaifiyarta ba sa da wannan kariyar.

An haifi ƴaƴanta biyu a Amurka kuma ƴan Amurka ne.

Yayin da Brenda ta shaida wa BBC cewa ba ta yarda cewa "mutanen kirki" za su kasance cikin wadanda za a kai wa harin da za a kai ga kora ba, ba za ta iya tserewa tunanin cewa za a iya mayar da mijinta Mexico ba.

"Yana da mahimmanci a gare mu mu ga ƴaƴanmu maza sun girma," in ji ta. "Tabbas tunanin cewa za a iya raba mu ya bar mutum a tsorace."