Abubuwan da suka kamata ku sani game da bikin rantsar da Donald Trump

Zanen ginin majalisar Amurka ta Capitol, kewaye da taurari da launuka daban-daban
    • Marubuci, Ana Faguy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Washington
  • Lokacin karatu: Minti 4

Zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump zai sake shiga Fadar White House a ranar Litinin lokacin da za a rantsar da shi a matsayin shugaban Amurka na 47.

A ranar ne zai karɓi rantsuwar kama aiki inda da yammacin ranar kuma za a yi waƙe-waƙe da kaɗe-kaɗe duka dai domin murnar fara sabuwar gwamnati.

Shi ma JD Vance zai sha rantsuwar kama aiki a ranar Litinin inda zai kasance tare da Trump a kan mumbari inda za su fara sabuwar gwamnatinsu a hukumance.

Ga abubuwan da ya kamata ku sani game da wannan babbar ranar ga Trump.

Mene ne bikin rantsarwa?

Rantsarwa ita ce bikin da ake yi a hukumance da ke nuna cikar wa'adin mulkin wani shugaban ƙasa da kuma farawar sabuwar gwamnati.

Gagarumin biki ne na miƙa mulki tsakanin jagororin gwamnati a Washington DC.

Wani muhimmin ɓangare na bikin ya ƙunshi zaɓaɓɓen shugaban ƙasar ya sha rantsuwar kama aiki: "Na yi alƙawarin tafiyar da ayyukan ofishin shugaban Amurka bisa gaskiya da amana, kuma iya ƙarfina zan kare kundin tsarin mulkin Amurka."

Duk da cewa ya ci zaɓe ne a watan Nuwamba, amma a hukumance, Trump zai zama shugaban ƙasar Amurka na 47 da zarar ya furta waɗannan kalaman.

Vance zai karɓi rantsuwar kama aiki kafin ya zama mataimakin shugaban ƙasa a hukumance.

A bikin, za a yi kaɗe-kaɗe da waƙe-waƙe, da jawabai - inda a nan ne Trump zai yi wa jama'ar ƙasar jawabi tare da zayyana masu ayyukan da yake son yi masu a shekaru huɗun da zai kasance a kan mulki.

Yaushe ne ranar rantsarwar?

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Za a soma bikin rantsar da Trump karo na biyu da addu'oi a majami'ar St Johns da ke dandalin Lafayette, wani coci a Washington DC mai daɗaɗɗen tarihim daga nan kuma zai a yi zaman shan shayi a Fadar White House.

Za a yi kaɗe-kaɗe da jawabin buɗe taro a gaban majalisar dokokin Amuka da ƙarfe 2:30 na rana agogon GMT.

Daga nan kuma ne za a rantsar da Trump da Vance da kuma jawabi bayan rantsarwar.

Daga nan kuma sai Trump ya shiga ɗakin shugaban ƙasa - kusa da zauren majalisar dattawa - inda zai sa hannu kan wasu muhimman takardu don soma sabuwar gwamnatinsa.

Kwamitin haɗin gwiwa ma majalisar dokoki kan bikin ƙaddamar da sabuwar gwamnati zai shirya wata liyafa da Trump zai halarta daga baya.

Daga nan ne kuma za a soma fareti daga Capitol zuwa titin Pennsylvania zuwa Fadar White House.

Da yammacin ranar kuma, Trump zai halarci wasu manyan taruka guda uku da za a gudanar don ƙaddamar da sabuwar gwamnati.

Ana sa ran zai yi jawabi a duka tarukan uku.

Yadda za ku kalli bikin rantsarwar

Mutane da dama na da burin zuwa kallon yadda za a rantsar da sabon shugaban Amurka sannan kuma ana ta neman tikitin zuwa bikin.

Ƴan majalisar dokoki na da wani adadi na tikitin da za su rarrabawa mutanen da suke wakilta domin su halarci bikin.

Tikitin kyauta ne amma yana da wuyar samu. Amurkawa na iya tuntuɓar ƴanmajalisarsu domin su samu tikitin.

Idan ba ka samu zuwa halartar bikin ba, akwai hanyoyi da dama da za ka iya kalla ta intanet.

Fadar White House za ta watsa bikin kai tsaye ta intanet.

BBC ma za ta kawo maku wainar da ake toyawa kai tsaye a bikin rantsar da Trump.

Za kuma ku iya kalla a shafinmu na intanet sannan kuna iya bibiyarmu a shafin kai-tsaye, inda za a riƙa wallafa bayanai game da muhimman abubuwan da ke faruwa a bikin kai tsaye.

Su wane ne za su halarci rantsarwar?

Ana sa ran mutum kusan 200,000 ne za su halarci bikin a Washingto DC da za su haɗa da magoya baya da suka zaƙu su ga ranar da kuma masu zanga-zanga.

Sanatocin Amurka da dama da ƴan majalisar wakilai suma za su halarta, da kuma baƙin shugaban ƙasa mai jiran gado da mataimakinsa.

Bayan Trump da Vance da iyalansu, sauran muhimman mutanen da za su halarci bikin su ne shugaban ƙasa mai barin gado da mataimakiyarsa. Hakan na nufin za mu ga Shugaba Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris - da suka sha kaye a zaɓen watan Nuwamba a hannun Trump - tare da iyalansu - Jill Biden da Doug Emhoff.

Tsaffin shugabannin ƙasar da matansu suma za su halarci bikin rantsar da Trump.

A bana, bikin zai haɗa har da George da Laura Bush da Barack Obama, duk da cewa rahotanni na cewa Michelle Obama ba za ta halarci bikin ba.

Waɗanne mawaƙa a ka gayyata?

Mawaƙiya kuma tsohuwar gwarzuwar shirin mawaƙa na American Idol, Carrie Underwood za ta rera waƙar 'America the Beautiful' a bikin ƙaddamarwar.

"Ina ƙaunar ƙasarmu kuma ina farin ciki da aka nemi na rera waƙa a bikin rantsarwar da kuma kasancewa cikin waɗanda za su halarci bikin na tarihi," kamar yadda Underwood ya faɗa a cikin wata sanarwa ranar Litinin.

Ita ma tawagar mawaƙa ta 'The Vllage People', za ta rera waƙa a ɗaya daga cikin manyan tarukan da za a yi a bikin rantsar da Trump ɗin, kamar yadda ƙungiyar ta sanar.

A yayin yaƙin neman zaɓe, Trump ya sha sanya waƙoƙin ƙungiyar -YMCA da Macho Man.

"Mun san wannan ba zai faranta wa wasun ku ba sai dai muna da yaƙinin cewa ya kamata a rera waƙa ba tare da la'akari da siyasa ba," in ji ƙungiyar a wani saƙo da ta wallafa a shafin Facebook.

"Wakarmuta Y.M.C.A. ta zama wani take a duniya da muke fatan za ta haɗa kan ƙasar bayan yaƙin neman zaɓe mai cike da ruɗani da rarrabuwar kai inda ƴartakarar da muka so ta yi rashin nasara."

Mawaƙi Lee Greenwood - daɗaɗɗen aboki ga Trump - da Christopher Macchio duka za su rera waƙa a wajen bikin.