Man City na harin Guehi, Manchester United za ta ɗauko Gallagher

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City na fatan taya ɗan ƙwallon Crystal Palace, Marc Guehi a shirin da take na kara karfin gurbin masu tsare mata baya a kaka mai zuwa. (Times - subscription required),
Manchester City da Manchester United da Chelsea na bibiyar ɗan ƙwallon Colombia, Daniel Munoz sai dai Crystal Palace ba za ta sayar da ɗan wasan mai shekara 29 ba.(Caught Offside).
Manchester United za ta yi kokarin sayen ɗan wasan Atletico Madrid, Conor Gallagher, mai shekara 25 da zarar an buɗe kasuwar cinikayyar ƴan ƙwallo a watan Janairu. (Teamtalk).
Manchester United ta ambaci sunan ɗan wasan Bournemouth ɗan kasar Amurka, Tyler Adams, mai shekara 26, cikin waɗanda za ta yi zawarci a watan Janairu.(Mail).
Napoli da ƙungiyoyin Premier League 10 na sha'awar ɗaukar matashi mai shekara 20, Kobbie Mainoo, amma manyan mahukuntan United ba sa son ya bar Old Trafford. (Telegraph - subscription required).
Mahaifin matashin ɗan ƙwallon nan mai shekara 16 da ke taka leda a Bayern Munich mai tsaron baya ɗan kasar Jamus, Cassiano Kiala ya je Landan a makon jiya domin tattaunawa da Chelsea da Manchester City. (Mirror).
Arsenal na sha'awar sayen ɗan wasan AC Milan, mai shekara 20 mai tsare raga ɗan kasar Italiya, Lorenzo Torriani. (Gazzetta - in Italian).
Watakila Newcastle ta yi wa mai tsaron bayanta, Matt Targett kiranye daga Middlesbrough da yake yi wa wasannin aro, domin ya maye gurbin Dan Burn, wanda ya ji rauni. (The I).
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
AC Milan ta cimma yarjejeniyar sayen Niclas Fulkrug, mai shekara 32, wadda ke fatan cimma yarjejeniya da West Ham, domin ɗaukar ɗan kasar Jamus cikin gaggawa. (Calcio Mercato - in Italian).
Milan za ta yi tayin karɓar aron Fullkrug, amma da ƙyar ne idan West Ham za ta amince da tayin da ƙungiyar Serie A za ta gabatar mata.(Mail).
Mauricio Pochettino da Oliver Glasner da kuma Marco Silva ake ganin ɗaya daga ciki ka iya maye gurbin kociyan Tottenham, Thomas Frank idan har ƙungiyar ta yanke sha'awar ta rabu da shi ɗan kasar Denmark. (Caught Offside).
Manchester City ba ta da shirin sayar da James Trafford a watan Janairu, bayan da Wolverhampton ke fatan sayen mai tsare ragar. (Football Insider).
Liverpool ta ci gaba da tattaunawa da Ibrahima Konate kan batun tsawaita ƙwantiraginsa, kenan ba za ta sayar da shi ba a watan Janairu, koda yake yana da damar tattaunawa da wasu ƙungiyoyin a watan gobe.(Teamtalk).
Ƴan wasan Arsenal sun nuna matukar fushinsu a ɗakin hutu, saboda kasa taka rawar gani ranar Asabar da suka yi nasara da kyar da gumin goshi a kan Wolverhampton a Emirates.(Telegraph - subscription required)











