Yadda satar mutane don neman kudin fansa ke karuwa a Kano

Asalin hoton, Getty Images
Ana ci gaba da nuna damuwa a game da yadda ake samun karuwar matsalar garkuwa da mutane sakamakon yadda 'yan bindiga ke kutsawa wasu yankuna na jihar Kano daga jihar Katsina mai makwabtaka.
A baya bayannan dai satar mutane don yin garkuwa da su a jihar ta fara zama ruwan dare gama duniya inda ko karshen makon daya gabata sai da aka yi garkuwa da mutane da dama.
Rahotanni na cewa wasu daga cikin mutanen da 'yan bindigar suka yi garkuwa da su sun kubuta daga hannun 'yan bindigar.
Tun da farko dai mutum hudu ne 'yan bindigar suka sace ciki har da mata biyu..
Hari na baya-bayan na shi ne wanda 'Yan bindigar suk kai yankin Lakwaya da ke ƙaramar hukumar Gwarzo a Jihar ta Kano, inda suka sace mutum huɗu tare da jikkata wasu uku.
Idris Adamu shi ne dagacin Lakwaya ya shaida wa BBC cewa 'yan bindigar kusan 30 ne suka kutsa ƙauyen Zurun mahauta mai makwafta da jihar Katsina.
Ya ce,"Duk da akwai jami'na tsaro da gwamnati ta tura, 'yan bindigar da suka shiga garinmu sun fi karfinsu, saboda babur sama da talatin ne suka shiga garin kuma anan ne suka dauki mutum biyu maza biyu mata biyu amma daga bisani matan sun kubuto, kana sun kora shanu sama da 100."
"Saboda wannan hari da aka kai garin namu yanzu mutanen garin muna cikin yanayi na fargaba da tashin hankali domin a kodayaushe wadannan 'yan bindiga za su iya dawowa, ba don komai ba saboda arzikin da Allah ya yi mana a yankinmu." In ji shi.
Idris Adamu, ya ce" A bisa wannan fargaba da muke ciki muna kira ga gwamnatinmu da ta kara samar mana da tsaro a garinmu dama sauran yankunan da wadannan 'yan bindiga suke kai hari."
Wannan hari da aka kai garin na Lakwaya, na cikin jerin hare-haren da 'yan bindigar suka kai a jihar, waɗanda suka yi sanadiyar asarar rayuka da garkuwa da mutane da dama.
Rahotanni na nuna cewa, kananan hukumomi akalla uku a arewacin jihar da suka hada da Tsanyawa da Shanono da kuma Gwarzo da ke maƙwabta da Jihar Katsina sune suka fi fuskantar hare-hare 'yan bindigar.
Gwamnatin Kanon dai ta kafa wata rundunar kar-ta-kwana don ƙarfafa tsaro a tashoshin mota wadda za ta riƙa sanya ido da tattara bayanan sirri tare da aiwatar da ayyukan tsaro na haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro, sannan kuma aikin rundunar zai shafi gidajen mai da sauran wuraren taruwar jama'a da ake ganin akwai yiwuwar fuskantar barazanar tsaro.










