Liverpool ta jinkirta ɗaukar Guehi, watakil Johnson ko Fatawu su maye gurbin Semenyo a Bournemouth

Marc Guehi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Marc Guehi
Lokacin karatu: Minti 2

Bournemouth na son ta sayi dan wasan Tottenham, Brennan Johnson mai shekara 24 a matsayin wanda zai maye gurbin Antoine Semenyo, mai shekara 25, idan dan wasan Ghana ya bar kungiyar a watan Janairu. (Sky Sports)

Haka kuma Bournemouth din na zawarcin dan wasan Leicester City da Ghana Abdul Fatawu mai shekara 21 ,wanda a baya Crystal Palace da Everton da kuma Sunderland ke zawarcinsa.(Mail)

Barcelona na son ta sayi dan wasan bayan Bournemouth da Argentina Marcos Senesi, mai shekara 28, a kakar wasa mai zuwa.(Sport )

Liverpool ta gwammace ta jira har zuwa bazara don siyan dan wasan bayan Crystal Palace da Ingila Marc Guehi mai shekaru 25,a maimakon watan Janairu.(Mail)

Everton na tunanin karbar aron dan wasan Manchester United da Ingila Kobbie Mainoo mai shekara 20 da abokin wasansa kuma dan kasar Netherlands, Joshua Zirkzee, mai shekara 24.(i Paper)

Manchester United na son ta dawo da dan wasan tsakiya na Scotland, Scott McTominay, mai shekara 29, filin wasa na Old Trafford daga Napoli. (Caught Offside)

Wolves na son dan wasan Hajduk Split da Kanada Niko Sigur mai shekara 22. (Fabrizio Romano)

Chicago Fire na son ta kulla yarjejeniya da dan wasan Barcelona da Poland Robert Lewandowski, mai shekara 37, amma kungiyar ta MLS na fuskantar gogayya daga Fenerbahce da kungiyoyin Saudi Arabiya. (Bild - in German)

Conor Gallagher na shirin barin Atletico Madrid a watan Janairu, inda Manchester United da Tottenham da Newcastle duk suke sha'awar dan wasan tsakiyar na Ingila mai shekara 25. (Teamtalk)

Everton ta fasa siyan dan wasan mai kai hari na Wolves da Norway, Jorgen Strand Larsen, mai shekara 25 wanda West Ham ke zawarcinsa. (Football Insider)

Leeds ta bi sahun Flamengo wajen zawarcin dan wasan Lazio, Taty Castellanos mai shekara 27 (Calcio Mercato)

Manchester United da Arsenal da Newcastle da Brentford duk suna zawarcin dan wasan Hoffenheim da Ivory Coast Bazoumana Toure mai shekara 19. (Caught Offside)