Chelsea za ta sayar da Sterling da Disasi, Man U na zawarcin Garner

Asalin hoton, Getty Images
Manchester United na sha'awar tsohon dan wasan tawagar Ingila masu shekaru kasa da 21,James Garner, wanda kwantariginsa a Everton zai kare a bazara mai zuwa . (Mail, external)
Chelsea na bibiyar dan wasan Rennes' da Faransa Jeremy Jacquet, mai shekara 20 da dan wasan Saint-Etienne' Djylian N'Guessan, mai shekara 17 sai dai sun fi ba batun sayarda 'yan wasan kungiyar da suka hada da Axel Disasi, mai shekara 2, da dan wasan Ingila Raheem Sterling, mai shekara 31 da Tyrique George,mai shekara 19.(Athletic - subscription required, external)
Juventus na zawarcin dan wasan tsakiya na Newcastle United da Italiya Sandro Tonali mai shekara 25 kuma ana ganin dan wasan na son ya koma Seria A,ya yin da suke sha'awar dan wasan Tottenham da Romania Radu Dragusin, wanda Roma ke son ta saya. (La Gazzetta dello Sport - in Italian, external)
Fulham da Crystal Palace na bibiyar dan wasan Manchester City Oscar Bobb, mai shekara 22, idan kungiyar ta amince ya tafi a watan Janairu - sai dai kungiyoyin da ke wajan Ingila ciki har da Sevilla, na zawarcin dan wasan tsakiya na Norway. (Talksport, external)
Sporting ta sha gaban abokiyar hammayata Portugal watau Porto a rige -rigen daukar dan wasan West Ham ,Luis Guilherme,kuma sun kusan kulla yarjejeniyar maida dan kasar Brazil mai shekara 19 dan wasa na dindin. (ESPN Brazil - in Portuguese, external)
Tottenham na son ta tsawaita kwantaragin dan wasan Netherlands Micky van de Ven. (Athletic - subscription required, external)
Watakila Liverpool ta nemi a bata aron dan wasa mai kai hari na Paris St-Germain da Portugal Goncalo Ramos, 24 na tsawon wata 6 , domin maye gurbin dan wasan Sweden da ya ji rauni Alexander Isak, mai shekara 26. (Caught Offside, external)
Wolves na son ta kulla yarjejeniya da tsohon dan wasan Bournemouth da Nottingham Forest Sam Surridge,mai shekara 27 wanda ya zira wa Nashville kwallo 24 a kakar wasa ta bana ta Major League Soccer (MLS) . (Talksport, external)
Kawo yanzu Liverpool bata yanke shawara akan ko za ta bar dan wasan tawagar Ingila na masu shekaru kasa da 20 Trey Nyoni mai shekara 18 ya fice daga kungiya a kasuwar Janairu, sai dai suna tattaunawa da kungiyoyin Firimiya da kuma na zakarun (Teamtalk, external)
Sevilla da Real Oviedo da Getafe suna zawarcin dan wasan Bournemouth da Turkiyya Enes Unal mai shekara 28. (Fichajes - in Spanish, external)














