Yadda maganar sauya sheƙar tsohon Ministan Tsaro, Badaru ta samo asali

Tsohon Ministan Tsaro na Najeriya, Mohammed Badaru Abubakar ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin sauya sheka daga jam'iyyarsa ta APC mai mulkin kasar zuwa jam'iyyar hamayya ta ADC.
A wata sanarwa da tsohon ministan ya sanya wa hannu da kansa, ya ce wannan zancen, labarin kanzon kurege ne, kuma wani yunkuri ne kawai na bata masa suna, da kuma kassara harkar siyasarsa.
A tattaunawarsa da BBC wani hadimin tsohon ministan, Kwamared Abba Malami, ya ce su wannan labari ya zo musu ne ma da mamaki:
''Na farko dai babu kanshin gaskiya a cikin wannan magana kuma ta zo mana da mamaki kwarai da gaske.
''Ta yaya mutum zai gina gida tun daga harsashi ya gina gidan bene katoto a masa fenti mutane ma su dinga zuwa, da 'yan haya da ma 'yan gidan, kuma shi a ce zai fita daga cikin gidan, to ya je ina?''
ganin cewa ko bambancin siyasa ne aka samu shi ya sa ake wannan jita-jita sai makusancin na Badaru ya ce :
''Bambancin siyasa da wa? Ba yanda za a yi mutum ya gina gidansa da karfinsa kuma ya fita daga cikinsa ko da kuwa akwai bambanci a cikin gidan. Ai duk bambanci in aka ce wannan gidanka ne. Ga me gidan ai bambanci ya kare.''
Ya kara da cewa, ''su ne masu wuka da nama na in ma an samu bambanci a daidaita bambancin tsakanin 'yan cikin gidan. Ai iyayen gida ne su suke da wannan ikon.''
Dangane da inda maganar ta samo asali, Kwamared Abba ya ce, yadda kowa ya ji maganar a kwararo da kafofin labarai na zamani su ma haka suka tsince ta.
''Kuma mu gaskiya ba ta zo mana da mamaki ba saboda wani lokacin idan daukaka ta kai daukaka aka ga lalle an yi tashin gwauron-zabi, sai ka ga mutane suna ta soki-burutsu, musamman irin mutanen da watakila ko ka taimake su sun zama wani abu, suke ganin wuyansu ya yi kauri, ko ma dai wasu makamantan haka. Za ka iya samun wannan matsalar daga wurinsu.''
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ganin cewa yanzu lokaci ne na yayin sauya sheka, ko hakan ne ya sa ake ganin tsohon ministan tsaron shi ma yana son sauya shekar ne har aka fara jita-jita, makusancin Badarun ya ce ko alama wannan ba akidar mai gidan nasa ba ce.
''To ai in ka kalli tarihin mai girma tsohon ministan tsaro ai ba dan siyasar yayin sauya sheka ba ne. Dan siyasa ne mai dandakakkiyar akida. Ai yana da tarihi. Lokacin da ya dauko ACN bai taba cewa ya fita ba sai da aka zo aka ce a zo a yi hadaka.
''Ka ga shi za ka ce mutum ne wanda daman da shi aka kirkiri wannan jam'iyya ta APC, tunda ai da satifiket dinsu na ACN aka hada. Ka ga ba mutum ba ne mai zara. Kamar yanda Hausawa ke cewa, ''daga an ga nan a yi nan'. Saboda haka shi ba dan siyasar yayi ba ne dan siyasar akida ne.
Kwamared ya ce tun asali ma Badaru ya sauka daga mukamin ministan ne bisa radin kansa, saboda yana son ya je ya huta, kasancewar shekararsa goma da rabi bai huta ba, yana yi wa kasa da jihar Jigawa hidima.
Hadimin ya kawar da duk wani zargi na tsamin dangantaka tsakanin Badarun da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya ce: ''Ai shugaban kasa ma ba shi da wasu hadimai a arewacin Najeriya kamar irin su mai girma tsohon minista. Mutumin da yake da alaka da shi tun tsohuwar alakar ACN, ta gangaro ta APC ta gangaro har ya zama shugaban kasa.
''Mutumin da ya janye masa takarar shugaban kasa a zaben fitar da gwani, ina zancen tsamin alaka? Ai sai dai alaka da ta dada danko. Ai da jam'iyyar APC da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ai suna nan rim da taya tare da tsohon minista.
''Tsohuwar amintaka ce wannan saboda haka jama'a duk su yi watsi da wata jita-jita da wani zai ce wai mai girma tsohon minista ko zai canza jam'iyya,'' in ji hadimin tsohon ministan.











