Dalilan da suka sa Ministan tsaron Najeriya ya ajiye aiki

Asalin hoton, X/Mohammed Badaru CON mni
Ministan tsaron Najeriya Mohammad Badaru Abubakar ya sauka daga muƙaminsa, yayin da kasar ke ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro.
A wata sanarwa da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai, Bayo Onanguga ya fitar ranar Litinin da daddare, ya ce Badaru ya sanar da ajiye aikin nasa ne a takardar ya aika wa shugaba Bola Tinubu.
Sanarwar ta kuma ce shugaban na Najeriya ya amince da ajiye aikin ministan tare da gode masa kan gudumawar da ya bayar.
Hakan na zuwa ne a wani lokaci da kasar ke fama da sake dawowar garkuwa da mutane a yankin arewacin kasar.
Satar dalibai 25 a jihar Kebbi da wasu kimanin 300 a jihar Neja na daga cikin abubuwan da suka kara dugunzuma matsalar rashin taaro a kasar.
Bayan haka, harin da aka kai kan masu ibada a wani coci da ke jihar Kwara da satar mutane a jihar Kogi na ci gaba da nuna raunin yaki da matsalar tsaro da gwamnatin kasar ta ce tana yi.
Sanarwar da fadar shugaban ƙasar ta fitar ta ce ministan ya ajiye muƙamin ne bisa dalilai na lafiya.
Sai dai a tsawon lokacin da Badaru ya kwashe yana jagorancin ma'aikatar tsaron, an ci gaba da samun hare-hare na mayaƙan Boko Haram a arewa maso gabashin kasar da kuma na ƴan fashin daji a arewa maso yamma.
A wata tattaunawa da BBC cikin makon da ya gabata, Badaru ya ce gwamnatin Najeriya na bakin kokarinta wajen yaki da matsalar.
Ya ce suna bincike don gano abin da ya janyo dawowar satar ɗalibai a makarantu da ƴanbindiga ke yi a ƙasar.
''Na tabbatar sojojinmu suna aiki ba dare ba rana su ga yanda za su yi maganin wannan abin.''
Matsalar tsaro a Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da ci gaba da ake yi da yunƙurin nemo ɗalibai da malaman da aka sace a jihar Neja, da kuma ayyana dokar ta-ɓaci a kan matsalar tsaro da shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya yi, masu ɗauke da makamai na ci gaba da sace-sacen al'umma a yankuna da dama na arewacin Najeriya.
Wani hari da aka kai a jihar Sokoto ya yi sanadiyyar sace mutane aƙalla 10, ciki har da amarya da ƙawayenta, yayin da aka kai wani harin a jihar Kogi, inda aka sace wani fasto da matarsa.
Haka nan hukumar shige da fice ta Najeriya ta sanar da cewa wasu mahara sun kashe jami'anta uku a wani hari da suka kai a wajen bincike na Bakin Ruwa da ke jihar Katsina.
Mai magana da yawun hukumar, A.S Akinlabi ta ce lamarin ya faru ne a ranar 27 ga watan Nuwamba da daddare.
Duk waɗannan hare-hare da kashe-kashe da kuma garkuwa da mutane na zuwa ne yayin da ƙasar ke fuskantar matsi bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya yi zargin ana yi wa mabiya addinin Kirista kisan gilla a ƙasar.
Donald Trump ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta ɗauki mataki a kan Najeriya matuƙar ba ta ɗauki matakan hana kashe kirista ba, ciki har da 'matakin soji'.
Sai dai gwamnatin Najeriya ta tura tawaga mai ƙarfi zuwa ƙasar ta Amurka, ƙarƙashin jagorancin mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaro Nuhu Ribadu, inda tawagar ta gana da masu ruwa da tsaki domin warware matsalar.
Gwamnatin Najeriya ta musanta zargin cewa ana yi wa kiristoci kisan gilla, tare da cewa "matsalar tsaro ta shafi ɗaukacin al'ummar ƙasar ba tare da la'akari da bambancin addini ba."
Wane ne Badaru Abubakar?
Mohammad Badaru Abubakar, wanda tsohon gwamnan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ne, ya zama Ministan tsaro na kasar bayan nadin da shugaba Tinubu ya masa a watan Agustan 2023.
Ya mulki jihar Jigawa na tsawon shekara takwas, daga 2015 zuwa 2023.
Badaru ya karanta ilimin akanta a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya kuma ya halarci cibiyar horaswa kan manufofi da tsare-tsare da ke Jos a jihar Filato.
Ya kasance babban ɗan kasuwa, inda ya riƙe shugabancin manyan ƙungiyoyin kasuwanci a Najeriya.











