Saura ƙiris mu gama da 'yanbindiga - Badaru Abubakar

Hoton Ministan tsaron Najeriya Mohammed Badaru Abubakar

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Ministan tsaron Najeriya Mohammed Badaru Abubakar, ya ce suna bincike don gano abin da ya janyo dawowar satar ɗalibai a makarantu da ƴanbindiga ke yi a ƙasar.

Ministan ya kuma yarda da cewa dama matsalolin tsaron Najeriya ba su ƙare ba, domin a cewarsa yaƙin sunƙuru 'yanbindiga ke yi, amma ya ce suna da ƙwarin-gwiwar saura ƙiris su daƙile su.

''Daman irin wannan yaƙin haka yake, lokaci zuwa lokaci za a samu sauƙi wani lokacin sai su banko wani abin da zai girgiza kowa a ƙasa, duk da na ji wasu suna cewa an san inda suke an san waye su.

''Gaskiya ne an san wajensu amman inda suke mutane ne ba za ka kai musu hari ba, ko kuma suna cikin dazukan da bam ɗinmu ba zai taɓa su ba,'' in ji shi.

Ya ƙara da cewa: ''Na tabbatar sojojinmu suna aiki ba dare ba rana su ga yanda za su yi maganin wannan abin.''

Ministan ya ce, daman ɗaiɗaikun hare-hare ba su ƙare ba: ''Ba mu taɓa cewa an gama gabaɗaya ba, amma abin da ya dame mu, wannan ɗaukan yara da dawowa shiga makarantun nan, shi ne muke nazari yanzu mu gano mene ne ya faru, ya kuma za mu yi maganinsa.''

Dangane da raunin tsaro da ake gani a makarantu da har hakan ke sa 'yanbindiga satar ɗaliban, ministan ya ce akwai tsari da suke da shi na tsare makarantu.

''Akwai tsari na ba makarantu tsaro, kuma ana bi kuma ana yi, kuma shi ya sa aka samu saukin abin shekara biyu ba a samu ba.

''Amman duk wanda ya san yaƙin sunƙuru ya san cewa lokaci-lokaci akan faki numfashin jami'an tsaro ko masu kula da tsaro a yi farmaki domin mutanen nan su nuna cewa har yanzu suna nan. Da yardar Ubangiji ba za a sake mamayarmu ba,'' a cewar ministan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Badaru ya kuma ce suna gudanar da bincike kan yadda aka ce an janye sojojin da ke bayar da tsaro 'yan mintina kafin a kai harin da ka sace ɗaliban nan mata na garin Maga na jihar Kebbi.

''Kuma na tabbata za mu gane, mene ne ya faru a lokacin, in an samu da kuskure da kuma laifi dole za a hukunta su, kuma za mu gano diddigin mene ne ya faru.'' Ya bayar da tabbaci.

Ministan tsaron na Najeriya ya kuma sheda wa BBC cewa suna sane da yadda wasu ƙungiyoyin 'yanbindiga da 'yan ta'adda ke sanya wa al'ummomi haraji, inda ya ce 'yanbingigan suna satar hanya ne su yi haka. Kuma ba sa kai musu hari ne a irin waɗannan wurare don gudun kada harin ya shafi mutanen da ba su ji ba ba su kuma gani ba.

''To ai ba fitowa fili suke yi ba suna yin wannan za su fito ne su haɗu da mutane sannan su gudu maɓoya,'' in ji shi.

Alhaji Badaru ya kuma yi martani ga barazanar shugaban Amurka Donald Trump ta ɗaukar matakin soji kan Najeriya bisa zargin kisan ƙare-dangi ga Kiristoci.

''Shuwagabanninmu sun je kuma sun tattauna a can kuma ana kan tattaunawa kuma da yardar Ubangiji za a samu fahimta, kuma maganar ko za su daina sayar mana makamai, daman muna saye a wurare da yawa ne,'' a cewar ministan tsaron.