Cutuka 5 da shan magani ba bisa ƙa'ida ba ke haifarwa

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Aisha Babangida
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
A yau, shan magani ba tare da gani ko izinin likita ba ya zama ruwan dare a Najeriya da kuma wasu ƙasashen Afirka.
Mutane da dama na ɗaukar kowane irin ciwo ko alamomin rashin lafiya da suka ji a jiki su kai tsaye su nufi shagunan sayar da magunguna domin sayen magani, ba tare da takardar likita ba.
Wannan ɗabi'a ta yi yawa a birane da ƙauyuka, inda wasu ke ganin samun magani a kanti ya fi sauƙi, ya fi arha, kuma ya fi sauri fiye da ziyartar asibiti.
Wasu kuma na yin hakan ne saboda tsadar kuɗin asibiti ko kasala ko ƙarancin lokaci ko kuma ƙoƙarin guje wa dogayen layuka da cunkoson da ake samu a asibitoci.
A wasu lokuta kuma, neman sauƙi cikin gaggawa ne ke tura mutane yin amfani da magunguna ba tare da cikakken bincike ba.
Sai dai duk da cewa wannan hanya na iya ba da sauƙi na ɗan lokaci, ƙwararru sun yi gargaɗin cewa tana iya janyo mummunan haɗari ga lafiyar mutum kamar yadda
Dr. Amina Abdullahi ta bayyanawa BBC cewa "shan magani ba bisa ƙa'ida ba ko ba tare da takardar likita ba na iya jawo matsaloli masu tsanani da dama da suka haɗa da."
Gazawar hanta
Dr. Amina ta ce amfani da magunguna ba tare da izinin likita ba na iya raunata hanta ko hantar ta samu matsala.
"Hanta ita ce ke tace magunguna a jiki. Idan aka riƙa shan magani fiye da ƙima ko ba daidai ba, hanta na iya gajiya ta kasa aiki, wanda hakan na iya kai wa ga cutar hanta mai tsanani," in ji ta.
Matsalolin ƙoda
Likitar ta ƙara da cewa magunguna da dama, musamman masu rage jin zafi ko raɗaɗi da wasu na gargajiya, na iya lalata ƙoda.
"Idan ƙoda ta lalace, jiki ba zai iya tace guba da ruwa yadda ya kamata ba, kuma hakan na iya jawo kumburi da raguwar fitsari ko ma gazawar ƙoda," in ji likitar.
Olsa da ciwon ciki mai tsanani

Asalin hoton, Getty Images
Likitar ta ce magungunan da mutane ke zuwa saye daga kantunan sayar da magani musamman idan sun ji zazzaɓi na iya haifar da ulcer ko jini ya fara fita idan mutum ya yi bayan gida, musamman idan an sha su ba tare da cikakken shawarwarin likita ba.
Rashin daidaiton jini
Dr. Amina ta ce wasu magunguna na iya haddasa hawan jini ko saukar jini fiye da ƙima.
"Idan mutum ya sha magani ba tare da gwaji ba, hakan na iya jawo bugun zuciya ko jiri ko faɗuwa, musamman ga masu matsalar zuciya ko hawan jini."
"Kuma akwai mutane da dama da ke zuwa sayen magungunan irin waɗannan cutuka ba tare da ganin likita ba."
Tsananta cuta
Dr. Amina ta ce shan magani ba tare da cikakken bincike ba na iya sa cuta ta ƙara tsananta. "Idan ba a gano ainihin cutar ba, maganin da aka sha ba zai yi aiki ba, hakan kuma na iya jinkirta warkewa ko jawo matsaloli na dogon lokaci."
Dr. Amina ta ƙara da cewa alamomi kamar ciwon ƙirji da zazzaɓi mai yawa da fitar jini daga jiki, ko ciwon ciki mai tsanani ba za a iya magance su ba kai tsaye ta hanyar sayen magani daga shaguna ba tare da ganin likita ba.
Saboda haka ne ta shawarci jama'a da su ga likita domin tantance yanayi kafin amfani da magunguna.
'Shan magani ba tare da ganin likita ba ya kumbura min ƙoda'

Asalin hoton, Getty Images
BBC ta kuma tuntuɓi wasu mutane da ke yawan sayen magani daga kanti domin samun sauƙi amma daga bisani ya koma barazana ga rayuwarsu
Hauwa Ibrahim, mazauniyar Abuja ta ce shan magani ba tare da ganin likita ba abu ne da ta saba da shi.
"Duk lokacin da na ji ciwon kai ko zazzaɓi, zan je shago na saya magani ne kawai. Ban taɓa tunanin hakan zai janyo min matsala ba," in ji ta.
Sai dai ta ce a wani lokaci ciwon ya ƙi raguwa, kuma sai ta fara jin ciwon ciki a ɓarangen dama wanda hakan ya sa ta je asibiti.
"Da na je likita ya duba ni, aka min gwaje-gwaje, sai likitan ya ce min wai ƙoda ta ce ta samu matsala, amma ya ce min idan na daina shaye-shayen magunguna barkatai, sannan in dinga motsa jiki, ƙodar za ta koma daidai." in ji ta.
'Ana sayen magani a waje na aƙalla sau 35 a kowane mako'
Wani mai kantin magunguna a Abuja wanda ya nemi a sakaya sunansa ya shaidawa BBC cewa a kullum, mutane suna zuwa sayen magani ba tare da takardar shaidar likita ba, inda ya ce yakan samu tsakanin mutum 15 zuwa 20 a mako.
"Amma gaskiya ni sai na tabbatar da cewa magunguna masu sauƙi ne kamar na mura da zazzaɓi da ciwon kai ko cutar maleriya ne suka zo saya kafin nake sayar musu da magani."
"Kuma a haka sai na tambayi wanda ya zo sayan maganin abubuwan da ke damunsa kafin nan na ba da maganin, idan har alamomin da ya faɗa ko ya nuna ya wuce ƙima kuma suna buƙatar ganin likita da cikakken binciken, cewa nake yi su je su ga asibiti." in ji shi.
Ya bayyana cewa, duk da yana da sha'awar taimakawa mutane, yana fargabar illolin da zai iya haifar wa idan aka yi amfani da magunguna ba tare da sahalewar likita ba, musamman magungunan da ke da haɗarin ko ke buƙatar auna yanayin jini ko cututtukan ciki kafin a yi amfani da su.










