Me ya sa Majalisar Wakilan Najeriya ke ƙilawaƙala kan cire wa gwamnoni rigar kariya?

Asalin hoton, House of Reps
Yunƙurin da Majalisar Wakilan Najeriya ke yi na gyara kundin mulkin ƙasar domin janye rigar kariya ga gwamnoni da mataimakin shugaban ƙasa ya bar baya da ƙura, yayin da ta yi amai kuma ta lashe.
A ranar Laraba ne majalisar ta yi wa ƙudirori sama da 40 karatu na biyu, waɗanda ke neman a yi wa kundin tsarin mulki gyaran fuska, cikinsu har da wanda ya nemi a tuɓe wa mataimakin shugaban ƙasa da gwamnonin jiha rigar kariya.
Sai dai kuma, kwana ɗaya da ɗaukar matakin ne majalisar ta ce ta janye karatu na biyun da ta yi wa ƙudirin rigar kariyar.
Yayin zamanta na ranar Alhamis, ɗanmajalisa kuma Shugaban Masu Rinjaye Julius Ihonvbere ne ya gabatar da ƙudirin neman janye matakin da kuma neman sake saka shi cikin waɗanda za a yi muhawara a kai.
Mataimakin Kakakin Majalisar Benjamin Kalu, wanda ya jagoranci zaman, ya ce sun yanke shawarar yin hakan ne "saboda a sake yin cikakkiyar muhawara a kan sa ganin irin muhimmancinsa".
Haka nan, majalisar ta janye karatu na biyu da ta yi wa ƙudirin da ke neman a yi wa tanadin hukuncin kisa gyara.
Kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya bai wa shugaban ƙasa da mataimakinsa, da gwamnoni da mataimakansu rigar kariya daga tuhuma a kotu har sai sun sauka daga kan mulki.
Matakin nasu ya jawo cecekuce daga ɗaiɗaikun 'yan Najeriya da kuma masana harkokin mulki da siyasa.
Ɗanmajalisa daga jihar Rivers, Solomon Bob (PDP), shi ne ya gabatar da ƙudirin domin gyara sashe na 308 da ya tanadi kare martabar ofishi da kuma tabbatar da shugabanci na gari.
Taken ƙudirin shi ne: "Ƙudirin neman gyara kundin mulkin Najeriya na 1999 domin tabbatar da rigar da kariyar shugaban ƙasa, da janye wa mataimakin shugaban ƙasa, da gwamnoni da mataimakansu kariya, da zimmar daƙile cin hanci, da magance zalinci, da inganta shugabanci na gari a ofisoshi da makamantansu."
'Matsin lamba'
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Tun bayan komawar Najeriya kan turbar dimokuraɗiyya a 1999, kusan kowace majalisa kan yi yunƙurin yi wa kundin mulkin ƙasar kwaskwarima a fannoni daban-daban.
Sai dai akasarinsu ba su iya yin nasara saboda wahalhalun da ke tattare da yin hakan kamar yadda doka ta tanada.
Majalisa ta 10 ma na tsaka da wannan yunƙurin, inda ƙudirorin da majalisar ta amince da su game da gyaran kundin mulkin suka kai kusan 80 a ranakun Talata da Laraba.
Babban dalilin da majalisar ta bayar na dakatar da amincewa da ƙudirin shi ne cewa "hakan zai ba su damar yin cikakkiyar muhawara saboda muhimmancin lamarin".
Sai dai Malam Kabiru Sufi, masanin kimiyyar siyasa a jihar Kano, ya faɗa wa BBC cewa akwai yiwuwar 'yanmajalisar sun ji matsi ne daga wasu ɓangarori.
"Babu mamaki sun dubi cecekucen da suka jawo a ƙasa baki ɗaya," a cewarsa.
"Sannan ƙila su ma gwamnonin ba haka kawai suka zauna ba, akwai yiwuwar sun fara tuntuɓa ta ƙarƙashin ƙasa ta yadda zai tilasta wa masu neman a yi dokar su koma su sake nazari."
Ɗaya daga cikin fargabar da masu fafutikar kare dimokuraɗiyya ke nunawa game da bai wa gwamnoni rigar kariya ita ce cewa za su samu damar aikata abin da bai dace ba.
"Yana daga cikin abubuwan da marigayi lauya Gani Fawehemi ya dinga fafutika a kai kenan lokacin Shugaban Ƙasa Tinubu yana gwamnan Legas, inda ya dinga ƙoƙarin kotu ta saurari tuhumar da yake yi wa gwamnan," in ji Sufi.
A gefe guda kuma, masanin ya ce lamarin ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya. Amma kuma ya ɗiga ayar tambaya.
"Tun a 1999 ɗin ake yin wannan kiraye-kirayen, amma mene ne dalilin da ya sa sai yanzu za a bijiro da lamarin? Kuma me ya sa aka haɗa da mataimakin shugaban ƙasa?"
Ya ƙarƙare da cewa: "Wannan ta sa ake ganin kamar buƙata ce kawai ta wasu tsiraru, kuma ya jawo ana cigaba da zargin majalisar tarayya a matsayin 'yan amshin shata."
'Ya kamata a cire wa shugaban ƙasa ma'
Batun rigar kariya ga masu mulki fafutika ce da ta daɗe tana raba kan masana harkokin mulki da kuma masu fafutikar shugabanci na gari.
Dr Murtala Adogi - masanin harkokin mulki a Najeriya kuma shugaban kamfanin System Strategy and Policy Lab - na ganin tun tuni ya kamata a ce an cire wa shugabanni rigar kariya, har da shugaban ƙasa.
"Duk abin da ya shafi mataimakin shugaban ƙasa ai ya shafi shugaban ƙasa. Ina ganin tsari ne mai kyau saboda zai sa su yi taka-tsantsan da abin da aikatawa," a cewar mai sharhin.
Duk da cewa ya aminta game da fargabar da wasu ke nuna cewa yawan ƙararrakin da za a iya shigar da su a kotu ka iya janye hankalinsu daga gudanar da harkokin mulki, Dr Adogi ya ce aunawa ya kamata a yi.
"Sai a duba a gani mene ne amfani ko rashin amfanin cire kariyar. Duk rigimar da ake yi da gwamnoni fa a EFCC da ICPC maganar kwangila ce. Duk rigimar ta rashin bin ƙa'ida ce.
"Ɗaya daga cikin amfanin cire wannan kariyar zai jawo kowa ya dinga samun abin da ya cancanta ta hanyar rage cuwa-cuwa ko alfarma wajen ɗaukar ayyuka da kuma bayar da kwangila.
"Sannan waɗanda ke fargabar ko jam'iyya mai mulki a matakin ƙasa za ta tilasta wa gwamnonin adawa, ya kamata su sani cewa ko da kariya ko babu kariya za su takura musu."











