Ko haɗakar jam’iyyu na tasiri a siyasar Najeriya?

Asalin hoton, Google
- Marubuci, Ahmad Bawage
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Daya daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a siyasar Najeriya a yanzu shi ne shirye-shiryen tunkarar babban zaben kasar na 2027.
Jam’iyyun adawa da manyan ‘yan hamayya na ci gaba da lissafin yadda za su kalubalanci jam'iyyar APC mai mulkin ƙasar, kuma ɗaya daga cikin abin da suke nazari a kai shi ne haɗaka.
Haɗaka ko maja dai ba sabon abu ba ne a siyasar Najeriya.
A lokuta da dama wasu ƴan siyasa na sauya sheƙa zuwa wasu jam'iyyu ko kuma su kafa sabbi domin haɗa kai wajen ƙoƙarin kayar da jam'iyya mai mulki - wadda suke ganin ta gaza yi wa ƴan ƙasa aiki.
Ƴan‘adawa dai na gangamin kulla alaƙa a tsakaninsu, musamman idan lokacin zaɓe ya tuaro domin cimma burinsu.
A lokutan baya jam’iyyu a Najeriya sun sha yin hadaka, musamman idan suka lura cewa karfinsu su kaɗai bai isa ya kayar da jam’iyya mai muki ba.
Misali…
Haɗuwar jam'iyyu huɗu don kada NPN
Maja ko haɗaka dai ya kasu zuwa biyu; akwai wanda jam'iyyu suke haɗewa don adawa da guda ɗaya da kuma na haɗuwa a shiga jam'iyya ɗaya, a cewar Farfesa Kabir Sufi na makarantar share fagen shiga jami'a a Kano.
Ya ce a Jamhuriya ta ɗaya da ta biyu, wasu jam'iyyu huɗu sun haɗu don kada jam'iyyar Northern People's Congress, wato NPC.
"A lokacin jam'iyyun sun ga babu wata mafita ta kada NPN sai sun haɗe. Shi muke kira da alliance a turance," in ji shi.
Ya ce hakan yafi fitowa a fili a Jamhuriya ta biyu, inda ɗaya daga cikin gwamnoni a wancan lokaci da ya ga abin ba zai kai su ga mafita ba, ya kushe abin.
Majar jam'iyyar APP da AD
Har ila yau a Jamhuriya ta huɗu, wasu jam'iyyu sun zo wuri guda don yin haɗaka.
Alal misali, lokacin da zaɓen shugaban ƙasa na 1999 ya karato, jam'iyyar All People's Party da Alliance for Democracy, sun shiga haɗaka.
Bayan tattaunawa, sun amince su tsayar da ɗan takarar shugaban ƙasa daga jam'iyyar AD, mai suna Cheif Olu Falae yayin da ita APP ta karbi takarar kujerar mataimakin shugaban ƙasa - inda aka ɗauki Umaru Shinkafi.
Haka ma, jam'iyyar AD ta shiga haɗaka da jam'iyyar PDP don mara wa takarar Cif Olusegun Obasanjo baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2003, ta hanyar dakatar da fitar da ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen.
Ita kuma jam'iyyar PDP a nata ɓangare ta amince ta kare muradun AD da tabbatar da sake zaɓar gwamnonin jam'iyyar a jihohi shida na kudu maso yammacin Najeriya.
Haɗuwa don kafa jam'iyyar APC
Farfesa Sufi ya ce wata maja da aka taɓa yi a Najeriya ita ce lokacin da ƴan siyasa suka haɗau wajen kafa jam'iyyar All Progressive Congress (APC) a 2013.
Kafa jam'iyyar ta APC ya kasance wani babban ci gaba a ɓangaren siyasar Najeriya, inda ƴan adawa suka yi gangami da haɗa karfi da karfe wajen kalubalantar jam'iyyar PDP mai mulki a zaɓen 2015.
Mutane da dama sun fito daga jam'iyyun CPC da ACN da sauransu, inda suka hakura da rajistar jam'iyyunsu don zuwa su haɗe.
"Wannan ya shiga tarihi a siyasar Najeriya saboda nasarar da APC ɗin ta samu a babban zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar," in ji Kabir Sufi.
'Jam'iyyar da ake gangami a kanta ita ma ba zama take yi'
Farfesa Sufi ya ce ita ma jam'iyyar da ake yin gangami don ganin an kada ita, ba zama take yi ta yi kallo ba.
Ya ce za ka ga tana nata yunkuri yanda ake so a cimma ta, ita ma ta karya lagon waɗanda ke son kawo mata cikas.
"Alal misali, jam'iyyar NPC a Jamhuriya ta ɗaya ta yi ta fito da ƙananan jam'iyyu domin ta yi wa manyan jam'iyyu da ke ƙoƙarin yin haɗaka a kanta. Misali irin jam'iyyu kamar Ibadan peoples Party don ta zama kishiya ga Action Group da kuma yunkurin hanata sukuni.
"Akwai kuma kirkiro da jam'iyyar Borno Youth Movement domin kada a bai wa Nepu damar yin karfin da za ta dami NPC a arewa. A can kudu maso gabas ma an kirkiro da Dinamic Party don shagaltar da NCNC duka a Jamhuriya ta ɗaya," in ji Sufi.
Me yake janyo jam'iyyu yin haɗaka?
Yawanci abubuwan da ke janyo ake yin haɗaka shi ne rashin gamsuwa da salon mulkin jam'iyya mai mulki, a cewar Farfesa Kabiru Sufi.
"Na biyu kuma idan jam'iyyar mai mulki ta yi karfin gaske, karfin da ya wuci yanda ake za to - hakan na tsorata sauran ƴan jam'iyyu inda za su buƙaci haɗa-kai don daƙile jam'iyyar da kuma karɓe mulki," in ji shi.
Ya ƙara da cewa ana kuma yin haɗaka ne saboda yanayin dimokraɗiyya, inda ya ce idan aka bar mulki a wuri guda daɗewar na sanya wahala wajen karɓar mulki a hannun wanda yake kai.
"Idan ana samun jujjuyawa na mulki tsakanin al'ummu hakan na fitar da kyawun dimokraɗiyya," a cewar Kabiru Sufi.
'Haɗakar na da tasirin gaske a siyasar Najeriya'
Farfesa Kabir Sufi ya ce irin wannan haɗaka ko maja da ake yi yana da tasiri a siyasar Najeriya.
Duk da cewa na Jamhuriya ta ɗaya da ta biyu bai kai ga karɓe mulki ba, amma na bayansa ya nuna akwai tasiri.
Ya ce haɗakar Jamhuriya ta huɗu ya yi tasiri saboda irin nasarar da aka samu.
"Wanda ya fi tasiri da kuma kai ga nasara shi ne na idan aka tashi sabuwar jam'iyyar adawa, musamman idan ta zo da tagomashi," in ji shi.











