Sarki Charles ya yi godiya ga masu yi masa fatan waraka daga cutar kansa

KING CHARLES

Asalin hoton, PA MEDIA

Sarki Charles ya aike da saƙon godiya ga al'ummar duniya da suka nuna alhinin kamuwa da cutar kansa da ya yi, a saƙon sa na farko tun bayan kamuwa da cutar.

Sarkin mai shekara 75 ya ce: "Kamar dai yadda sauran mutanen da suka kamu da cutar kansa suka sani, irin wannan alhini, da fatan aleri daga jama'ar gari su ne kan gaba wajen samar da natsuwa a zuciyar wanda ya kamu da cutar."

A ranar Litinin Fadar Buckingham ta sanar da cewa sarkin ya kamu da kansa.

Ana yi wa Sarkin maganin cutar kansar da ba a fayyace irin ta ba a Sandringham.

An gano ya na ɗauke da cutar kansar ne a lokacin da ake masa maganin lalurar mafitsara a cikin watan Janairu. Ba a dai bayyana irin kansar da yake fama da ita ba, amma fadarsa ta tabbatar cewa ba kansar mafitsara ba ce.

A cikin saƙon godiya da ya fitar, sarkin ya ce: "Na yi farin ciki matuƙa da sanin cewa bayyana wa duniya halin da nake ciki ya taimaka wajen ƙara wayar da kan jama'a, da kuma tallafawa ayyukan da ƙungiyoyi ke yi wajen taikamawa masu kansa da ma iyalansu a Birtaniya da duniya baki daya.

"Halin da na tsinci kaina ya sa na ƙara fahimtar aikin sadaukarwar da suke yi."

A yanzu Sarkin zai jingine ayyukansa kuma ana sa ran sauran manyan ƴan gidan sarautar za su gudanar da wasu daga cikin ayyukan yayin da yake karɓar magani.

Ya isa gidansa da ke Norflolk a ranar Laraba bayan ya bar birnin London tare da matarsa.