Sarki Charles III na Birtaniya na fama da cutar kansa

Sarki Charles III

Asalin hoton, Huw Evans Picture Agency

Bayanan hoto, Sarki Charles III

Fadar masarautar Birtaniya ta Buckingham ta bayyana cewa an gano Sarki Charles na fama da cutar kansa.

Sai dai ba a bayyana takamaiman nau'in cutar kansar da aka gano Sarkin na fama da ita ba.

Amma sanarwar da fadar ta fitar ta bayyana cewa Sarkin zai fara karɓar magani daga ranar Litinin.

Sanarwar ta ƙara da cewa sarkin "na cike da kyakkyawar fata game da maganin da zai riƙa karɓa kuma yana sa ran komawa aiki kamar yadda ya saba da zarar damar hakan ta samu."

A yanzu Sarkin zai jingine ayyukansa kuma ana sa ran sauran manyan ƴan gidan sarautar za su gudanar da wasu daga cikin ayyukan yayin da yake karɓar magani.

Babu dai wani cikakken bayani game da matsayin cutar ta kansa da yake fama da ita.

Duk da zai jingine ayyukan nasa amma Sarkin zai ci gaba da riƙe muƙamin da kundin tsarin mulki ya ba shi na shugaban gwamnati, ciki har da sanya hannu kan takardu da kuma tattaunawa ta sirri.

Kimanin mako ɗaya da ya gabata ne aka yi wa Sarkin aiki kan lalurar mafitsara a wani asibiti da ke birnin Landan.

Lokutan da sarki Charles III na Birtaniya ya yi jinya

.

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sarki Charles da sarauniya Camilla lokacin da suke barin asibitin birnin London
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An sanar da cewa sarki Charles ya kamu da cutar kansa ne bayan an shafe fiye da makwanni biyu ana fitar da rahoto game da lafiyar sa.

17 Janairu: Fadar Buckingham ta sanar da cewa sarki Charles je asibiti domin yi mashi maganin lalurar mafitsara.

26 Janairu: An yi wa sarkin maganin lalurar mafitsara bayan ya kwanta a wani asibitin birnin London kuma da safe sarauniya Camila ta ce yana nan lafiya.

29 Janairu: An sallami Sarki Charles daga asibiti bayan jinyar kwana uku. Fadar sa ta sanar cewa za a soke duk wasu ayyukan da aka tsara zai yi a bainar jama'a, domin ya samu damar murmurewa.

31 Janairu: Sarauniya Camila ta ce mijinta ya na ci gaba da murmurewa bayan shan magani.

4 Fabrairu: Sarkin da uwargidansa sun halarci bauta a wata cocin a Sandringham, inda a karon farko tun bayan jinyar, sarki Charles ya bayyana a gaban jama'a har yana ɗaga hannu.

5 Fabrairu: Fadar sa ta sanar cewa sarki Charles ya kamu da cutar kansa kuma har an fara bashi magani.