An taƙaita yawan masu yin jana'iza a Rwanda saboda cutar Marburg

Particles of the Marburg virus

Asalin hoton, Getty Images

    • Marubuci, Makuochi Okafor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa health correspondent
  • Lokacin karatu: Minti 2

Hukumomi a Rwanda sun taƙaice yawan mutanen da ya kamata su halarci jana'izar mutanen da cutar Marburg ta ƙashe, a wani mataki na daƙile kaifin yaɗuwar cutar mai saurin bazuwa.

Mutum takwas ne aka tabbatar da rasuwarsu sakamakon cutar da ta ɓarke a ƙasar, kamar yadda ma'aikatar lafiyar ƙasar ta sanar a ranar Juma'a.

Ita dai ƙwayar cutar Marburg wadda ke saurin kisa an samo ta ne daga ƙwayar cutar Ebola. Mutane kan ɗauki ƙwayar cutar daga birbiri inda kuma ake iya yaɗa ta ta hanyar gumin jiki ko yawu.

A wani sabon matakin daƙile yaɗuwar cutar, ma'aikatar lafiyar ƙasar ta ce bai kamata masu jana'izar wanda ya rasu sakamakon cutar ba su wuce 50.

Mutum ɗaya kawai za a bai wa marasa lafiyar domin kula da su kamar yadda sabbin dokokin suka ce.

A ranar Asabar, lokacin da alƙaluman waɗanda cutar ta kashe suna shida, ma'aikatar lafiyar Rwandar ta ce mafi yawancin waɗanda cutar ta kama ma'aikatan lafiya ne fannin kula da masu matsanancin rashin lafiya. Mafi yawancin waɗanda suka kamu suna babban birnin ƙasar, Kigali.

Hukumomi a Rwanda dai sun ce sun tsaurara bin sawun mutum mutum 300 bayan annobar cutar ta Marburg ta kashe mutum takwas cikin 26 da aka tabbatar sun kamu da ita, a cewar gidan talabijin na ƙasar Rwanda TV.

Ministan Lafiya Sabin Nsanzimana ya ce mutum 18 ne ke jinya yayin da gwmanati ta mayar da hankali kan gwaji da kuma wayar da kan al'umma game da cutar da aka tabbatar da ɓullarta ranar 27 ga watan Satumba.

Nsanzimana ya nemi 'yan ƙasar da ke jin alamomi kamar zazzaɓi, da ciwon gaɓoɓi, da gudawa ko amai da su kai rahoto zuwa asibiti mafi kusa da su.

"Abu ne mai muhimmanci idan kuka ji waɗannan alamomi ku sanar da hukumomi ta lambar waya 114 da kuma tuntuɓar hukumomin lafiya," a cewar ministan.

Wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) a Rwanda, Brian Chirombo, ya ce an tura ƙwararru bakwai domin talafa wa gwamnatin ƙasar shawo kan annobar.

Wannan dai karon farko da aka samu ɓullar cutar ra Marburg a Rwanda.

Maƙwabciyar ƙasar wato tanzania ta taɓa samun ɓullar cutar a 2023, sannan an samu mutuwar mutum uku a 2027 a Uganda.