'Lakurawa sun yi barazanar halaka mu idan muka sayar da shanunmu'

'Yan bindiga

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 2

Mayakan kungiyar nan ta Lakurawa sun gargadi al'ummomin garuruwa fiye da goma na yankin karamar hukumar Augie ta jihar Kebbi, a kan su yi watsi da dabarar sayar da shanun huda suna sayen wasu na'urorin zamani na huda da ke amfani da man fetur.

Mayakan sun ce za su halaka duk wanda ya ki jin gargadin nasu.

Manoman dai kan sayar da shanun su sayi na'urorin huda saboda tsoron da suke yi, cewa 'yan bindigar suna sace musu dabbobi.

Kashedin da ake zargin 'yan kungiyar ta Lakurawa sun yi wa jama'ar garuruwan, ya jefa fargaba da zaman dar-dar ga mutanen yankin.

Wani mutumin Daya daga cikin yankunan da ba ya so a ambaci sunansa, ya shaida wa BBC cewa suna sayen motocin ne domin yin noman shinkafa, kuma suna yin hakan ne don kada a kama musu shanunsu shi y asa suke sayar da su.

Mutumin ya ce," Mayakan Lakurawan na zargin cewa ana sayar da shanun ne don kada su sace su sannan kuma manoman na boye kudadensu idan suka sayar da shanun."

"Yanzu ala tilas babu yadda zamu yi dole mu karbi wannan gargadi domin mahukunta kansu sun rasa yadda za su yi da su ballantana mu talakawa dole mu hakura da sayar da shanun mu sayi motocin noman." In ji shi.

Matsalar ta 'yan kungiyar Lakurawan dai ta yi kamari, kuma ta zama wani karfen kafa, kamar yadda mutumin ya shaida wa BBC.

Ya ce mayakan kan zo garuruwansu ne a kan mashin inda suke goyon uku a kan kowane mashin sannan ga bindiga a hannunsu.

Ya ce," Idan suka shiga gari haka suke tafiya da dabbobi ciki har da shanu kai hatta kaji ba sa bari kuma mutum na kallo za a kada dabbobinsa amma bai isa ya ce komai ba dan kana magana sai dai kaji harbi."

Mutumin na yakin Augie a jihar Kebbi dai ya bayyana fatan hukumomin da abin ya shafa su kara tashi tsaye, wajen samar da kwararan matakan tsaro da za su kai ga wanzar da zaman lafiya mai dorewa a yankin.