Me ya sa aka samar da Tudun-mun-tsira ga ƴan fashin daji a Zamfara?

'Yan bindiga

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 3

Yayin da shalkwatar tsaron Najeriya ta ƙaddamar da Tudun Mun Tsira a jihar Zamfara don 'yan fashin dajin da ke son ajiye makamansu a yankin Arewa maso Yamma, mutane da dama a kasar na tunanin ko matakin hakan zai yi tasiri wajen magance matsalar tsaron da ake fama da ita a kasar.

Rahotanni sun ce Tudun Mun Tsiran wani shiri ne na musamman na sojoji da zai bai wa 'yan ta-da-ƙayar-baya da 'yan fashin dajin da suka tuba dama domin su koma cikin al'umma.

Kazalika an tsara shirin ne a kan sigogi guda biyar kamar ajiye makami da kwance ɗamara da sauke wa mutum kangara da gyara zama da kuma mayar da su cikin al'umma.

Sulaiman Bala Idris, shi ne mai magana da yawun Gwamnan Zamfara ya shaida wa BBC cewa an kaddamar shirin ne domin bayar da dama ga 'yan fashin dajin da suka gaji suke neman mafita su ajiye makamansu.

Ya ce,"A duk lokacin da ake yaki a waje to idan aka fara cin karfin masu tayar baya ma'ana yakin ya kusa zuwa karshe to akan bayar da dama ga masu tayar da kayar bayan da ke son mika wuya a karbe su."

"A yanzu kusan za a iya cewa an riga an ci karfin 'yan bindigar jihar Zamfara sosai don mafi yawancinsu ma sun tarwatse wasunsu sun gudu sun bar iyali da ma abubuwan da suka tara, to irin wadannan za a iya basu dama su zo Tudun Mun Tsira domin su mika wuya."In ji shi.

Sulaiman Bala Idris, ya ce mutane za su yi mamakin ko sulhu ake nema da 'yan bindigar, ba maganar sulhu bane, magana ake ta an fi karfinsu don haka suma neman ta kai suke.

Ya ce, "Wadanda za a basu dama su zauna a Tudun Mun Tsira, irin 'yan fashin dajin nan ne da ke da mata da yara, saboda ko yaki ake ba a kashe mata da yara saboda ire-irensu ne za a bawa dama, ba wai gaggan 'yan bindigar ba."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

"Ba irin Turji zamu dauko mu ajiye a Tudun MunTsira ba, yakamata mutane su fahimci haka, akwai manyan 'yan fashin dajin da ko sun zo su mika wuya ba lallai a karbe su ba."

Shirin Tudun Mun Tsira dai shiri ne na gwamnatin tarayya da hadin gwamnatin Zamfara da kuma gwamnatocin jihohin Arewa maso yamma.

Kuma an samar da wannan shiri ne ga'yan bindiga da 'yan fashin dajin da suka gaji suna neman mafita don su kawo kansu su ajiye makamai a basu waje su zauna su da iyalansu ba tare da wani sharadi ba.

Matsalar tsaro dai matsala ce da ta addabi jihohin Najeriya da dama musamman jihohin da ke fama da 'yan fashin daji.

Hukumomi a Najeriya dai na ikirarin suna kokari wajen ganin an kawo karshen matsalar musamman matsalar 'yan bindiga a jihohin yankin arewa maso yammacin Najeriya inda kusan a kullum sai an kai hari musamman a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna.

Jihar Zamfara dai na ɗaya daga cikin johohin da matsalar tsaro ta fi kamari a faɗin Najeriya, inda barayin daji ke afkawa garuruwa da kauyuka da kashe mutane da satar wasu domin neman kuɗin fansa, ga kuma sacewa ko kwace amfanin gonar da manoma suka shuka.