Masana sun gano katafaren ramin da ke haɗiye taurari a kullum a samaniya

...

Asalin hoton, Getty Images

Zuwa yanzu masana kimiyya sun kasa bayyana ainahin yadda wutar jahannama take.

Dalili kuwa shi ne watakila saboda ba wanda ya taba zuwa can ya kuma dawo ballanatan ya bayar da labarinta.

Abin dai da aka sani ko ake tunani a kanta a yanzu shi ne cewa, waje ne maras dadin zuwa ko kadan, mai ban tsoro wanda bai dace da mutum ba ko wata halitta ta rayu a ciki.

To a yanzu dai a iya cewa ta hanyar wani babban bincike na sararin samaniya, masana kimiyya sun iya gano yadda za a iya bayyana yadda jahannama take.

Wata sabuwar makala da aka wallafa a mujallar kimiyya ta Nature Astronomy, ta bayyana wani wawakeken bakin rami wanda tarkacen sararin samaniya da hayaki mai haske suka kewaye.

Masanan sun yi wa wannan wawakeken rami da cikinsa yake duhu baki kirin suna da J0529-4351, a matsayin abin da ya fi duk wani abu da aka taba gani haske a kewayen duniya da sararin samaniya.

...

Asalin hoton, Getty Images

Wawakeken bakin rami

Tuni masu bincike na sararin samaniya suka gano miliyoyin irin wadannan manya-manyan ramuka bakake, suna ta kara girma a fadin samaniya. Yawanci ana ganinsu a tsakiyar dandazon taurari.

Haka kuma an gano cewa wadannan bakaken ramuka sun ma fi biliyoyin rana girma idan da a ce za a dunkule biliyoyin rana waje daya.

Wadannan ramuka suna girma da sauri, inda suke zuke taurari da hayakin da ke kewaye da su, su fada cikinsu.

Kadan ne daga cikin abubuwan da suka fada wannan rami za su iya fitowa. Kuma karon da abubuwan da suka fada ramin suke yi na kara rura wuta da sanya ramin zafi.

Idan abubuwan da ramin ya zuke suka yi yawa sosai, zafin ya kai zafi sai a rika ganin hasken da ke fitowa daga ramin ya karu sosai ta yadda har za a ga ya ma fi dubban taurari da ke samaniya haske.

Wannan ne ma ya sa muke iya hangen irin wannan wawakeken bakin rami yana girma a can nesa da duniyarmu, nisan da za a yi tafiyar miliyoyin shekaru kuma tafiya ta gudu irin na haske ba a kai wajen da yake ba.

...

Asalin hoton, Getty Images

Wawakeken bakin ramin da ya fi girma a samaniya

Wannan wawakeken bakin rami da aka bayyana da jahannama da aka yi wa lakabi da suna J0529-4351 yana fitar da hasken da ya ninka na rana da muke gani har sau biliyan 50.

Saboda wannan haske mai yawan gaske da ramin ke fitarwa, masana na ganin cewa ba ta yadda zai iya samar da wannan haske idan ba yana hadiyar akalla rana da muke gani ba guda daya a kullum.

To idan har haka lamarin yake ramin na hadiyar rana guda daya a kullum to ashe kuwa yana da nawi da kuma karfi da zafi sosai a cikinsa. To amma fa babu wata fargabadangane da wannan rami.

Abin da ya sa aka ce haka shi ne hasken wannan rami zai dauki shekara sama da biliyan 12 kafin ya iso duniyarmu, wanda hakan ke nufi tuni da dadewa ya daina kara girma.

Ire-iren wadannan manyan bakaken ramuka da ake iya hange a kusa da duniyarmu a yanzu a iya cewa sun riga sun gama aiki.

Bakaken ramukan jahannama da suka daina aiki

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A yanzu wadannan manya-manyan bakaken ramuka sun daina girma da kuma hadiye duk wani abu da ya je kusa da su.

Saboda hayakin da ke fita ko ratsawa a tsakanin dandazon taurari shi ma yawanci ya zama taurarin, kamar yadda nazarai ya nuna.

Bayan wani dogon lokaci na biliyoyin shekaru, wadannan taurari sukan shirya kansu a waje, su zama da wani kamanni a wajen.

Wadannan taurari na yin dogon layi kuma su kewaye wadannan bakaken manyan ramuka da a yanzu kusan a ce ba sa aiki kamar yadda aka san su a baya.

Kuma ko da ma ace wata tauraruwa ta kama hanyar fadawa wannan wawakeken rami, galibi takan baude daga ramin.

Hakan na faruwa a sararin samaniya inda taurarin kan je wajen da yake da wuyar zuwa ta irin wannan hanya a sararin na samaniya.

To amma kuma idan har ya kasance akwai abubuwa da yawa a sararin, inda tauraron da ya baude ya je ya yi karo da wani za su fashe nan da nan daga nan kuma sai su fada sararin tauraro mafi girma wanda kuma shi ne na biyar a rukunin taurarin da ke kusa da rana, da ake kira Jufita (Jupiter)

Irin wannan karo na taurari yakan faru sosai a farkon samuwar sararin samaniya, kuma wadannan manyan bakaken ramuka, wadanda a nan muke kwatanta su da jahannama su suke amfana da karon.

Da'irar jahannama - Wurin da 'yan sama jannati ba za su iya zuwa ba

Wannan waje ne da ke zaman kamar da'ira ga harabar wannan wawakeken bakin rami. Waje ne mai zafin gaske, wanda duk abin da ya kai nan har ya shiga to fa ba zai dawo ba.

Waje ne da yake da tarin gajimare, kuma gajimaren na saurari sosai idan ya tunkari ramin.

Wannan gajimare yana sauri ko gudun kilomita dubu 100 a cikin dakika daya.

Wannan na nufin a cikin dakika daya gajimaren na cin nisan da duniya za ta iya kaiwa a cikin sa'a daya.

Me ya sa har yanzu ba a gano wannan rami na jahannama ba?

To idan har wannan rami shi ne ya fi komai haske a sararin samaniya, me ya sa har yanzu ba a gano shi ba?

Dalili shi ne akwai irin wadannan manya-manyan ramuka bakake masu haske da yawa a sararin na samaniya.

Ana ganin abubuwa da dama a sararin samaniya daga na'urorin hangen nesa na duniya saboda haka dole ne masu bincike su yi amfani da kayan aiki na zamani da za a iya cewa masu gani-har-hanji domin su tantance abu.

Na'urorin da ake amfani da su, suna iya hango manya-manyan bakaken ramukan na gama-gari, amma ba su kai ingancin da za su iya gano ramukan da muka bayyana a baya ba, da aka yi wa lakabi da jahannama ba.

A shekara ta 2015, wani rukunin masana na Chana, ya gano irin wannan rami da ke ta girma cikin sauri, to amma kiris ya rage su kuskure ganin ramin saboda tsarin da suka yi amfani da shi wajen binciken.

Burinsu shi ne su gano tauraro ko duk wani abin da ya fi tsanani da haske da kuma saurin girma a tsakanin irin wadannan manyan ramuka bakake.

Mu a namu bangaren mun yi amfani da hanyoyi irin na zamanin da inda muka samu sabbin bayanai.

Bincikenmu ya dogara ne da aikin hadin gwiwa na shekara goma da aka yi tsakanin masana na Australiya da na Turai, wadanda suke da kayan binciken samaniya masu yawa.

*Christian Wolff karamin Farfesa ne a fannin binciken sararin samaniya a jami'ar National University ta Australiya.