Wuraren shakatawa: Halas ga maza, haram ga mata, in ji Taliban

wata yarinya tsaye a gaban wurin sayen tikiti na wani wurin shakatawa a Kabul

Asalin hoton, Reuters

Yara ne suke ta shewa yayin da suke wasa a manya-manyan lilo da motocin roba da kuma jirgin kasa na wasan yara a wani wurin wasan da ke tsakiyar Kabul, babban birnin Afghanistan.

Wasu daga cikin iyaye maza na tare da su a cikin motocin, wasu kuma suna gefe suna daukar hoto - daya daga cikin lokutan murna kalilan a kasar, inda mafi yawa aka fi samun munanan labarai.

To amma an haramta wa mata jin dadin kallon 'ya'yansu suna wasa a irin wadannan wurare. Gwamnatin Taliban mai tsattsauran ra'ayi ta haramta wa mata ziyartar wuraren shakatawa a Kabul.

A lokacin da muka kai ziyara, akwai 'ya'yan kungiyar da dama wadanda ke shakatawa a kan abubuwan wasan na yara.

Maza na iya zuwa wuraren shakatawa

Wuri mafi kusa da mata za su iya zuwa shi ne wurin cin abinci da ke kallon gurin wasan yaran.

A kwanan baya ne kuma aka haramta wa mata zuwa wuraren shakatawa da na motsa jiki a babban birnin.

Ana sa ran za a fadada dokokin zuwa daukacin fadin kasar.

Yayin da Taliban ke ci gaba da kakaba musu takunkumai, mata manya da yara na fargabar abin da zai faru nan gaba.

Wasu na cewa dokar ba ta shafi mutane da dama ba, domin a yanzu akasarin mutanen kasar na kallon fita zuwa wuraren shakatawa matsayin abu ne na masu hannu da shuni.

Ba tasirin da dokar za ta yi ne ya fi damun yara mata na Afghanistan ba, sai dai abin da hakan ke nufi - domin ya kara fitowa da aniyar kungiyar ta Taliban, tun bayan da suka karbe iko a watan Agustan 2021.

Wata daliba ta ce "a matsayinmu na yara mata a Afghanistan, kullum ana kakaba mana sabbin dokoki. Tamkar muna zaune ne muna jiran doka ta gaba."

"Na ci sa'a na kammala sakandare kafin Taliban ta kwace mulki. Amma ina jin tsoron watakila za a hana mata zuwa makaranta. An kashe min burina ke nan."

A kwanakin nan ne ta yi jarrabawar shiga jami'a, sai dai ta yi takaici, kasancewar an daina bai wa mata damar karantar kwas din da take so, wato aikin jarida.

Wannan daya ne daga cikin matakan da Taliban ta dauka a baya-bayan nan.

Ta ce "ba zan iya kwatanta irin takaicin da na ji ba. Wani lokaci sai ka ji kamar ka kwala ihu. Ina jin tamkar ba ni da amfani."

Mata a wani wurin wasan yara a Kabul a watan Maris, 2022

Asalin hoton, AFP

Yayin da Taliban ke ci gaba da takaita wuraren da mata ke iya zuwa, wasu na kokarin nemo mafita.

Wata 'yar fafutuka, Laila Basim, ta samar da wani dakin karatu na mata, tare da hadin gwiwar wasu matan. Akwai dubban litattafai wadanda aka rubuta da harsuna da dama.

Ta ce "muna son nuna wa Taliban cewa ba za a rufe wa matan Afghanistan baki ba, yanzu abin da muka sa a gaba shi ne fadada dabi'ar karatu a tsakanin mata, musamman yara mata wadanda aka aka hana su 'yancin yin karatu."

Laila Basim
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A makon nin da suka gabata ne aka tsare mai fafutuka Zarifa Yaghoubi da wasu daban. Duk da kiraye-kirayen da aka rinka na a sake su, ciki har da majalisar dinkin duniya, Taliban ba ta ce uffan ba.

A makon da ya gabata kuma mutum 12 ne, ciki har da mata uku aka yi wa bulala a gaban dubban mutane.

Wadannan abubuwa na nuna cewa Taliban na komawa irin tsarin mulkin da ta yi a shekarun 1990.

Gaba da dakin karatun kadan, za ka ga ofishin jami'an hisbah, wani wuri da aka haramta wa mata su shiga.

Mai magana da yawun dakarun hisban, Mohammad Akif Muhajer ya ce "mun ajiye akwatin da mata za su jefa koke-kokensu a ciki daga waje. Shugabanmu yakan je waje domin ganwa da mata, saboda girmama su."

Ya kare matakin gwamnatin Taliban na haramta wa mata zuwa wuraren shakatawa, inda ya ce shari'ar musulunci ce ta haramta.

Lokacin da aka tambaye shi ko me ya sa ake murkushe wadanda ke hankoron tabbatar da 'yancin mata, sai ya ce "a kowace kasa ana kama duk wanda ya saba wa umurnin gwamnati. A wasu kasashen ma kashe su ake yi."

Mohammad Akif Muhajer

Daga kalamansu da ayyukansu za ka ga cewa suna da tsauri a kan mata da kuma duk wanda ya yi kokarin jayayya da su.

Wadannan tsare-tsaren nasu na kalubalantar sassaucin ra'ayi, tun bayan da suka karbe mulki a bara.

Wata daliba ta ce "wata kila nan gaba mu wayi gari a ce an hana mata fita daga gidajensu. Komai ma zai iya faruwa a Afghanistan."

Haka nan za ka iya ganin damuwar da matan Afghanistan suka yi kan matakin kasashen duniya na kin daukan mataki.

Laila Basim ta ce "duniya ta juya mana baya. Manyan mutane na goyon bayan matan Iran, amma ba na Afghanistan ba."

"Ba a bai wa abin da ya faru da mu muhimmanci. An manta da mu."