Mutanen da ke bai wa 'ya'yansu da ke jin yunwa kwaya don su yi barci

Ghulam

Mutanen Afghanistan na bai wa ‘ya’yansu magunguna barci don rashin abinci – wasu sun sayar da ‘ya’yansu mata da sassan jikinsu domin samun kudin abinci. A cikin hunturu na biyu, bayan da 'yan Taliban suka kwace mulki, aka dakatar da kudaden kasashen waje suke bai wa kasar, rayuwa ta fara wahala.

Abdul Wahab ya ce “'Ya'yanmu na ta kuka, kuma ba sa barci. Ba mu da abinci.”

"Don haka muke zuwa wuraren sayar da magunguna, mu sayi magani mu ba su don su ji jiri.”

Yana zaune ne a wajen Herat, birni na uku mafi girma a kasar, birni ne cike da masu gudun hijira da wadanda suka rasa muhallansu sanadin yaki inda suka zama a gidajen da aka yi da laka.

Abdul na daya daga cikin mutane da dama da suka ka taru a gabanmu. Sai muka tambaye su, shin mutane yawa ne ke ba wa 'ya'yansu magunguna don su yi barci?

Suka ce "dukkanmu."

Ghulam Hazrat ya sa hannu a cikin aljihunsa ya fito da magani. Sunan maganin ‘alprazolam’ – maganin da ake bai wa mutanen da ke cikin damuwa.

Afghanistan
Bayanan hoto, Afghanistan

Ghulam na da ‘ya’ya shida, ɗan auta daga cikinsu yana da shekara daya. Ya ce “har shi ma ina ba maganin.”

Sauran mutanen sun fito da kwalayen kwayoyin escitalopram da sertraline da suka ce suna bai wa ‘ya’yansu. Ana yawan ba wa masu larurar damuwa wadannan magungunan.

Likitoci sun ce bai wa yara wadanda ba su samun isasshen abinci mai gina jiki wadannan magungunan na iya lalata hantarsu, tare da wasu matsaloli kamar gajiya a kowane lokaci da kuma yawan barci da birkita halinsu.

Afghanistan
Bayanan hoto, Afghanistan

Mun gano cewa za ka iya sayen kwayar magungun biyar a kan kudin Afghanis 10 (naira 150 kenan) a wani kemis da ke birnin, kwatankwacin kudin ledar burodi daya.

Akasarin iyalai suna raba burodi daya a tsakaninsu a kullum. Wata mata ta fada mana cewa suna cin busassshen burodi da safe, da daddare kuma su tsoma shi cikin ruwa don ya yi laushi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce bala’in jin kai na faruwa a Afghanistan.

Yawancin mazan da ke zama a wajen Herat na aikin leburanci ne. Sun kwashe shekaru da dama cikin wahala.

Amma lokacin da Taliban ta karba mulki a watan Agustan bara, ba tare da amincewar kasashen duniya ba, an daina bai wa kasar tallafin kudade daga kasashen waje, lamarin da ya kawo tabarbarewar tattalin arziki da ya yi sanadin rashin aiki ga wasu mazan.

Duk ranar da suka samun aikin yi, suna samun kimanin kudin Afghanis 100 ko kuma sama da dala daya.

Duk inda muka je muna ganin yadda rayuwa ta tilasta wa iyalai daukar matsanancin mataki don ceto kansu da iyalansu daga yunwa.

Ammar (wanda aka sakaya sunansa) ya ce an yi masa tiyata wata uku da suka wuce don a cire masa koda kuma ya nuna mana wurare tara da aka sanya masa filasta.

"Na ji cewa mutum zai iya sayar da kodarsa a wani asibiti. Na je can kuma na gaya musu ina so na sayar da tawa. Makonni kadan bayan haka aka kira ni a wayar tarho aka ce na je asibiti," in ji shi.

"Sun yi min wasu gwaje-gwaje, sannan suka yi mini allura da ta sa na fita daga hayyacina. Na yi matukar jin tsoro amma ba ni da wani zabi idan ban da haka."

Afghanistan
Bayanan hoto, Afghanistan
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

An biya Ammar Afghan 270,000 (dala 3,100), kuma ya yi amfani da rabin kudin wajen biyan basukan da ake binsa lokacin da ya saya wa iyalansa abinci.

Ya ce “Idan muka ci abinci yau, gobe ba za mu samu abin da za mu ci ba. Bayan na sayar da kodata, ina ji kamar ba cikkaken mutum ba ne ni. Idan rayuwa ta ci gaba kamar haka, ina ji zan kashe kaina.”

Sayar da sassan jiki ba sabon abu ba ne a Afghanistan. Ana yin hakan tun kafin Taliban ta karbi mulki. Amma yanzu, duk da hukuncin da mutane ke yankewa na sayar da gabobin jikinsu, suna rasa kudin sayen abinci.

A wani gidan kuma mun hadu da wata uwa da ta ce ta sayar da kodarta wata bakwai da suka wuce. Su ma suna bukatar biyan bashi – da suka karba don sayen garken tumaki. Kuma tumakan ma sun mutu a wata ambaliyar ruwa da aka yi a shekarun baya.

A wani gidan kuma mun hadu da wata uwa da ta ce ta siyar da kodarta wata bakwai da suka wuce. Su ma suna bukatar biyar bashi – da suka karba don siyan garken tumaki. Kuma tumakan ma sun mutu a wani ambaliya da aka yi a shekarun baya.

Afghanis 240 (dala 2,700) da na samu a sayar da kodar tawa ma ba su isa ba.

Ta kuma ce “Yanzu dole ne mu sayar da ‘yarmu ‘yar shekara biyu don mutanen da muka karbi bashi a hannunsu na damunmu a kullum cewa mu ba su ‘yarmu idan ba za mu iya biyan su ba.”

Mijinta ya kara da cewa “Ina jin kunyar halin da muke ciki. Wani sa’in ina ji kamar gara na mutu.”

Sau da dama muna ji mutane na sayar da ‘ya’yansu mata," in ji Nizamuddin. “Na sayar da ‘yata kan kudin Afghanis 100,000.”

Mutuncin mutanen da ke zaune a nan ya zube saboda tsabar yunwa.

Abdul Ghafar, daya daga cikin manyan yankin ya ce “Mun fahimci cewa hakan ya saba wa ka’idojin addinin Musulunci, kuma mun san cewa muna sa rayukan ‘ya’yanmu cikin hadari, amma babu wata mafita.”

Afghanistan
Bayanan hoto, Afghanistan

A wani gidan kuma mun hadu da Nazia ‘yar shekara hudu, mai fara’a tana ta yin dariya yayin wasa da kaninta ɗan wata 18 mai suna Shamshullah.

Mahaifinta Hazratullah ya ce “Ba mu da kudi, haka ne ya sa na yi sanarwa a masallacin unguwarmu cewa ina so na sayar da ‘yata.”

An sayar da Nazia ga iyalan wani yaro da ke kudancin Kandahar. Idan ta cika shekara 14 za a tura ta can don ta auri yaron. Zuwa yanzu, Hazratullah ya karbi biya biyu kan ‘yarsa.

“Na yi amfani da yawancin kudin wajen sayen abinci da kuma magani ga ɗan autana don ba ya cin abinci mai gina jiki,” Hazratullah ya fada yayin da yake ɗaga rigar Shamsullah don nuna mana kumburarren cikinsa.

Ci gaba da samun matsalar rashin ingantaccen abinci manuniya ce kan yadda yunwa ke tasirin kan yara 'yan kasa da shekara biyar a Afghanistan.

Kungiyar Médecins Sans Frontières (MSF) ta ce adadin yaran da ake kawowa asibiti don rashin ingantaccen abinci ya karu da kashi 47 a wannan shekarar.

Reshen MSF da ke Herat ne kawai cibiya mai kayan aiki da ke ba wa mutanen Herat da makwabciyarta Ghor da Badghis abinci inda matsalar rashin ingantaccen abinci ta karu da kashi 55.

Tun shekarar da ya wuce, sun kara yawan gadaje da za su taimaka wajen kula da yara mara lafiya da suke kwantarwa. Duk da haka, cibiyar na cika da mutane fiye da yadda ake tsammanin. Yawancin yaran da ke zuwa na bukatar magani fiye da na cuta daya.

Omid na fama da matsalar rashin ingantaccen abinci kuma yana da gwaiwa da kuma cutar sepsis. Watansa 14 a duniya amma nauyinsa ya kai kilogiram hudu. Likitoci sun fada mana cewa ya kamata a ce jariri dan wata 14 ya yi nauyin kilomita 6.6. Sai da mahaifiyarsa Aamna ta karbi rancen kudi don zuwa asibiti da ya fara amai ba kakkautawa.

Afghanistan
Bayanan hoto, Afghanistan

Mun tambayi Hameedullah Motawakil, mai magana da yawun gwamnatin Taliban a Herat, abin da suke yi don magance matsalar yunwa.

“ Ana cikin wannan halin ne saboda takunkuman da kasashen duniya suka sanya wa Afghanistan da kuma kwace kadarorin mutanen kasar nan. Gwamnatinmu na kokarin gano mutane nawa ne ke bukatar abinci. Da yawansu na yin karya game da yanayin da suke ciki ganin cewa za su samu wani abu daga wajen gwamnati.” Abin da ya dage kansa kenan duk da ganin halin da mutane ke ciki.

Ya kuma ce Taliban na kokarin sama wa mutane aikin yi. “Muna kokarin buɗe ma’adinan karfe da bututun iskar gas.”

Da kyar idan hakan zai faru.

Mutane sun fada mana yadda suke ji kamar gwamnatin Taliban da kasashen duniya sun wulakanta su.

Yunwa na iya kashe mutum a hankali, kuma ba a ganin illarta nan take. Halin da mutanen Afghanistan ke ciki ba zai taba canzawa ba saboda babu wanda ya damu.