An yi wa mutum 12 bulala a bainar jama'a a Afghanistan

Taliban

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Sojojin Taliban rike da tutar Afghanistan

An yi wa mutane 12 bulala, ciki har da mata uku a gaban dubban mutane masu kallo a filin wasan kwallon kafa a Afghanistan.

Wani jami'in gwamnatin Taliban ya shaida wa BBC cewa ana zargin mutanen ne da laifukan da suka haɗa da zina, da sata da kuma luwaɗi.

Bayanai na cewa wannan ne karo na biyu a cikin wata guda da ƙungiyar ta masu kishin Islama ke yi wa mutane bulala a bainar jama’a.

Matakin na nuni da dawowar amfani da tsauraran dokoki a ƙasar, kamar yadda aka gani a lokacin mulkin Taliban na shekarun 1990.

Mai Magana da yawun kungiyar Taliban na yankin Logar da ke gabashin Afghanistan, Omar Mansoor Mujahid ya ce an saki mata ukun bayan da aka gama yi masu bulalar. Amma an tura wasu maza daga cikin waɗanda aka yi wa bulalan zuwa gidan yari, ba a san adadinsu ba.

An yi wa mutanen bulala tsakanin 21 zuwa 39.

Wani jami'i ya ce bulala mafi yawa da aka yi ma wani ita ce 39.

Ƙarin labarai

Rahotanni sun ce an kuma hukunta wasu mutanen 19 ta hanyar bulala a makon da ya gabata, a lardin Takhar da ke arewacin Afghanistan.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wannan hukunci da aka zartar a lardin Logar na zuwa ne mako daya bayan da shugaban kungiyar Taliban Hibatullah Akhundzada, ya umurci alkalai da su aiwatar hukunce-hukunce a kan laifuka daidai da shari’ar Musulunci.

Wannan tsarin na fassara dokokin addinin Musulunci, sun haɗa da zartar da hukunce-hukunce a bainar jama’a, kamar yanke wa mutane gaɓoɓibin da jefewa – duk kuwa da cewa gwamnati ba ta fayyace takamaiman hukunce-hukunce da za a yi a kan waɗanda suka aikata laifukan ba.

Umurnin babban jagora ƙungiyar na daga cikin alamu na baya-bayan nan da suka nuna cewa Taliban na ɗaukar tsauraran matakai na take hakkin bil'adama da taƙaita ƴancin al'umma, duk kuwa da alƙawarin da suka yi na cewa za su yi amfani da dokoki masu sauƙi, bayan karbar mulki a bara.

A lokacin mulkin ƙungiyar na shekarun 1996 zuwa 2001, an yi tir da matakin Taliban na yin hukunci a bainar jama’a, wanda ya haɗa da bulala da kisa a babban filin wasa na kasa da ke Kabul.

Gwamnatin ta kuma sha alwashin ba za ta maimaita danniyar da ta rinƙa nunawa kan mata ba a a baya, sai dai tun bayan kama mulki an rinƙa tauye wa mata hakki, sannan an sha yi wa matan bulala a bainar jama'a.