Taliban ta hana mata zuwa wuraren shan iska da wasanni

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyar Taliban ta haramta wa mata zuwa wuraren shan iska da wasanni a babban birnin ƙasar Kabul, lamarin da ya zama sake ware mata daga duk wata cuɗanya da mutane a Afghanistan.
Wani mai magana da Ma'aikatar Kula da Ɗa'a ya shaida wa BBC cewa an gaya wa masu kula da wuraren shaƙatawa cewa kar su sake barin mata shiga.
Ƙungiyar ta ce ba a bin dokokin Musulunci a wuraren shaƙatawar.
Tun bayan da ƙungiyar ta ƙwace iko da ƙasar a watan Agustan 2021 aka sake tsaurara matakai kan ƴanci da walwalar mata.
A ƙarƙashin mulkin Taliban na nuna wariya ga wani jinsi, an bai wa mata izinin zuwa wuraren shaƙatawa ne kawai sau uku a sati - daga Lahadi da Litinin sai Talata -su kuma mata sau huɗu a mako.
A yanzu kuwa ba za a yarda mata su shiga wajen ba ko da ƙarƙashin rakiyar muharramansu maza.
"Mun yi hakan ne saboda cikin wata 15 da suka wauce ɗin nan duk da ƙoƙarinmu, to mutane ba sa bin dokokin Shari'ar Musulunci a ƙasar," in ji Mohammed Akif, mai magana da Ma'aikatar Kula da Ɗa'a, kamar yadda ya cewa BBC.
"Wannan mataki ya shafi dukkan mata ne, ko sun je su kaɗai ko tare da muharrami."

Asalin hoton, Getty Images
Haramcin ya haɗa har da wuraren wasanni da ake hawa ƙananan motoci da iyalai ke zuwa da yara.
Zuwa yanzu dai kamar dokar a babban birnin kawai ta fara aiki, amma a baya irin waɗannan dokoki sun shafi baki ɗayan sassan ƙasar.
Kamfanin dillancin labarai na reuters ya ga lokacin da wata mata ta je shiga waje wasannin amma sai aka hana ta.
Masooma wacce ba ta yarda an bayyana cikakken sunanta ba ta ce: "KAmata ya yi idan uwa ta je wajen da ƴaƴanta to a bar su su shiga, saboda yaran nan ba su ga wani abu mai kyau ba... don haka suna buƙatar su yi nishaɗi da wasanni.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana yawan tauye wa mata haƙƙoƙinsu a ƙarƙashin mulkin Taliban.
Mata da dama sun sha duka a ƙoƙrinsu na neman ƴancinsu.
An haramta wa mata yin bulaguro mai tsawo ba tare da muharrami ba.
Sannan har yanzu ba a bar ƴan mata da dama sun koma makaranta ba a ƙasar, duk da alkawarin da Taliban ta yi cewa ba za ta hana su ba.
A yayin da har yanzu akwai matan da ke aiki a fannoni kamar na lafiya da ilimi, da yawansu an hana su komawa bakin aikin bayan da Taliban ta ƙwace mulki.
A watan Mayu, an gabatar da wata doka da ke bai wa mata damar yin shiga irin ta Musulunci tare da niƙabin rufe fuska, duk da dai akwai waɗanda ba sa bin dokar.
Taliban dai ta sha alwashin ba za ta takurawa mata da matsa musu ba kamar yadda ta yi a shekarun 1990 da ta yi mulki.
Sun ce a yanzu suna girmama ƴancin mata a ƙarƙashin tsarin Shari'a, kuma ba sa adawa da karatun mata.
Amma jami'an diflomasiyya na ƙasashen yamma sun ce ci gaba da bai wa ƙasar tallafi don ayyukan ci gaba ya ta'allaka ne kan yadda aka tafiyar da inganta rayuwar mata.










