Ƴan mata ƴan ƙwallo da suka tsere wa Taliban amma suka rasa tudun dafawa

The scene at Kabul airport's east gate on 25 August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Filin jirgin saman Kabul ya ga duniya a watan Agustan 2021
    • Marubuci, Daga Mani Djazmi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport

Filin jirgin sama na Kabul ya kasance cikin ruɗu da hananiya. An yi ta harbe-harbe, mutane sun yi ta turmutsutsu cikin rikicewa. Dubban mutane sun yi ta ƙoƙarin tserewa daga Taliban, kuma Fati na daga ckinsu.

Fati gola da ta ƙware a jin Turanci ta hanyar kallon shirye-shirye masu dogon zango na talabijin da fina-finai. Mun ɓoye cikakken sunanta da na iyayenta don ba ta kariya.

A lokacin da a hankali Taliban ta ƙwace iko da ƙasar a watan Agustan 2021, Fati ta yi gaggawar yanke hukuncin cewa ita da ƴan tawagarta za su bar ƙasar, su bar iyayensu da danginsu.

Sun shafe shekaru suna wasa tare, a tawagar ƙwallon ƙafar da ke wakiltar Afghanistan da ke neman bai wa mata ƴanci.

A yanzu tunanin mutane ya karkata kan yanke hukuncin kisa da sauran tsauraran dokoki da za su iya faruwa a ƙarƙashin mulkin Taliban din, kamar yadda ya faru a shekarar 1996 zuwa 2001.

Da farko Fati ba ta yarda cewa Taliban za ta koma kan mulki ba. Amma daga baya fatan nata bai kai gaci ba. Dole ta bar ƙasar.

"Na sa wa raina cewa ta Afghanistan ta ƙare," in ji ta.

People climb the boundary wall of Hamid Karzai International Airport

Asalin hoton, EPA

"Na yi tunanin cewa babu wata sauran dama ta rayuwa, ba ni da damar sake fita waje don neman haƙƙina. Babu makaranta, babu kafafen yaɗa labarai, babu wasanni, ba komai. Mun zama tamkar gawarwaki a cikin gidajenmu.

"Satina biyu ban yi barci ba. Ko yaushe wayata na hannuna, don neman waɗanda za su taimaka min. Dare da rana ba ni da aiki sai kiran waya da tura saƙon tes da shiga shafukan sada zumunta."

Daga baya Fati da ƴan tawagarta sun samu mafita. Wata ƙungiyar mata ta ƙasa da ƙasa ce ta taimake su don samun tsira.

Ga dai labarin tserewar tasu.

Labarin ya fara ne daga birnin Texas na jihar Houston ɗin Amurka, mai nisan kilomita 12,700 daga Afghanistan, inda wata tsohuwar ƴar ƙwallo a Amurka ta shirya kwashe mutane.

The scene at Kabul airport in August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Short presentational grey line

"Kamar wata ƴar ƙaramar cibiya ce aka buɗe a Whatsapp," in ji Haley Carter. "Kar ku taɓa raina wayon mata musamman ta wajen amfani da waya."

Carter, mai shekara 37, ita ma gola ce a da. Ta yi aikin soja har a Iraki. Ta yi aikin mataimakiyar koci a Afghanistan daga shekarar 2016 zuwa 2018.

'Bayanan sirri'

Duk da cewa ta yi nisa da Afghanistan, amma ta dinga aika bayanan sirri kan sauyin da ake samu a Kabul ta hanyar ma'aikatan hukumar tsaron ƙasa ta saƙonnin Whatsapp.

Ta ce a bisa tsari bai kamata a yaɗa irin waɗannan bayanan ba, sai dai da yake ya zo a yanayi na ceto.

"A gaskiya ban ma san abin zai yiwu ba. Idan na tuna ma sai na abu ne mai tsauri.

Former Afghanistan women's football captain Khalida Popal

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wata tsohuwar kyaftin ta Afghanistan Khalida Popal ma ta taka rawa a wajen taimakon ƴan wasan

Wata tsohuwar kaftin ɗin tawagar ƙwallon ƙafa a Afghanistan Khalida Popal ce, ta bayar da shawarar a nemi Carter.

A lokacin da take yarinya a zamanin mulkin Taliban, Popal kan yi wasan ƙwallo da ƙawayenta amma cikin sirri don kar Taliban su ji yo su.

Ta bar Afghanistan ne saboda barazanar kisa da ta fuskanta kan wasan ƙwallo da take yi, kuma tun 2011 ta koma ƙasar Denmark da zama.

Popal ta san cewa Fati da ƴan tawagarta za su faɗa tarkon Taliban saboda shahara da suka yi a ƙwallo. Kuma ta san cewa sojoji na zuwa gida-gida. Mata ƴan wasa da yawa a Kabul sun koma ɓuya. Da yawa na tsoron kar a kashe su.

Ta shaida wa Fati da sauran ƴan tawagar cewa su goge shafukansu a kafafen sada zumunta, su ƙona kayan ƙwallonsu, su kuma binne kyaututtukan da suka samu a ƙwallo.

"Sai dai hakan abu ne mai wahala don kuwa nasarorinmu ne," in ji Fati. Waye zai so ya ƙona rigunan jesi ɗinsa? Na sa a raina cewa idan har na rayu, to zan sake samun wasu nasarorin."

A hannu guda kuma, Carter na shirin yadda za ta samar musu jirgin sojoji don kwashe su daga ƙasar da wurwuri.

Ta san matsalar tsaron da Afghanistan ke ciki zai sake taɓarɓarewa. Ta haƙiƙance cewa gwamnatocin Birtaniya da na Amurka ba sa bin lamarin yadda ya kamata. Kuma Taliban suna ta saka shingayen bincike a kan hanyoyi.

Women and children throng the streets outside the Taliban-controlled check point near the entrance of the airport in Kabul, Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Mata da yara na tsammanin Warabbuka a ƙofar shiga filin jirgin saman Kabula

"Khalida ta aiko mana da saƙo dukkan cewa 'ƴan mata, ku kasance cikin shirin tafiya filin jirgi a tare, kowa jaka ɗaya kawai za ta ɗauka," in ji Fati.

"Ta ce: "Ba za mu iya gaya muku ko muna da tabbacin za ku iya isa cikin filin jirgin ba. Amma idan kuka dage, za ku kai labari."

Da lokacin ya iso sai Fati ta rubuta lambar wayar Carter a kan hannunta, ko da tsautsayi zai sa a sace wayarta. Carter ta kuma cewa Fati ta gaya wa ƴan wasan su dinga kashe wayoyinsu don gudun kar caji ya ƙare.

Fati ba ta ɗauki kaya da yawa ba a lokacin barin gida. Ta sa doguwar riga tare da rufe fuskarta.

Duk da gargaɗin da aka yi musu cewa kar su kwashi kaya da yawa sai masu muhimmanci sosai, sai da Fati ta ɗauki wani gajeren wando na kayan ƙwallo, duk da akwai haɗari a yin hakan.

A filin jirgi kuwa lamarin ya hargitse. Dubban mutane sun yi cincirindo don neman tafiya.

'Ƙoƙarin tsira'

"Mutane na ta marmatse juna don ƙoƙarin shiga ciki da sauri iya yadda za su iya," in ji Fati.

"Yanayi ne na ko a mutu ko a yi rai. Kowa na neman tsira.

Afghans try to enter Kabul airport, with a men pulling a child up the side of a wall while another man pulls a man nearby

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ƴan Afghanistan suna ƙoƙarin haura katanga don shiga filin jirgin Kabul

Mutane da yawa na cikin tsananin turmutsutsun.

"Idan har babu sunanka a jerin sunayen, ko kuma in ba wani ya fito daga cikin filin jirgin ya shigar da kai ba, to ba za ka samu shiga ba," in ji Carter.

"Don haka mun yi ƙoƙari sosai don tabbatar da cewa abokan aikinmu sojoji da ke ƙofar shiga wajen suna da bayanansu don su bar su su shiga da wuri.

Carter ta cewa Fati "akwai wani da zai jira su a ƙofar da ke arewaci."

Amma a ƙofar da ke arewan sai aka hana Fati da ƙawayenta shiga, don saƙon bai isa ba.

Mutumin da ke gadin wajen ya ce idan ba su da fasfo din Amurka ba za su shiga ba.

Taliban fighters at the airport

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Mayaƙan Taliban sun karɓi ragamar kula da wajen filin jirgin saman Kabul

Sake tsari

A can Houston kuwa, sai da Carter ta sauya tsarin.

Nan take ta ce su sake ba ta lokaci za ta yi magana da masu jiran ƙofar.

Babu abin da Fati da ƙawayenta suka iya sai dai su jira.

A Taliban Fateh fighter, a "special forces" unit, stands guard along a street in Kabul on 29 August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Wani sojan Taliban na tsaye riƙe da bindiga a watan Agustan 2021

"Mun shafe kusan awa 48 a waje, ga shi ana tsananin rana da zafi. Yara sai koke-koke suke yi, balle idan suka ji harbin bindiga.

Shingayen binciken Taliban

Fati ta yanke shawarar ita da sauran ƴan wasan su sake gwadawa amma ta ƙofar da ke kudu. Akwai shingayen binciken Taliban har biyu a hanyar.

Da fari an raba ta da ƙaninta aka yi masa duka. A karo na biyu kuma ita ma wasu mutane masu riƙe da bindiga sun dake ta suka tunkuɗa ta baya.

Da azaba ta ishe ta ga duka ga zafi ga ƙarar harbe-harben bindiga, sai ta ji ta gaza har za ta miƙa wuya.

Amma sai ta tuna da saƙon da Popla ta aika mata cewa lamari ne na "ko a mutu ko a yi rai."

Fati ta ce sai ta miƙe zumbur don ci gaba da fafutuka.

Sojojin Australiya

Sai ƴan wasan suka rabu biyu. Suka yi maza suka ɓatar da hankali masu gadin Taliban, suka yi gaggawar isa wajen sojojin Australiya da ke ƙofar kudancin filin jirgin saman.

Ta ce akwai mutane da dama a wajen amma a haka suka kutsa suka shiga. "Mun ga sojojin Australiya sai muka ce da ƙarfi, 'tawagar ƙwallon ƙafa ta ƙasa'.

Australiya da son ƙwallo, kawai sai suka bar mu muka wuce bayan duba takardunmu.

An air crew prepares to load evacuees at Kabul airport in August 2021

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Jirgi na shirin barin filin jirgin Kabul a watan Agustan 2021

A lokacin da Fati da ƴan tawagarta da wasu ƴan tseren Afghanistan suka shiga wani jirgin sojoji mai zuwa Australia, sai ta aika wa Carter hotonsu da saƙo cewar, "mun yi nasara, mun yi nasara."

Short presentational grey line

Atisaye a Australiya

A Australiya, Fati da tawagarta sun yi atisayen farko tare a Melvourne a watan Fabrairu, bayan da ƙungiyar Melbourne Victory ta samar musu da abubuwan da suke buƙata da kuma koci.

"Abin ya mana dadi sosai," in ji Fati.

"Na zaci mun samu duk abin da muka rasa, kuma tawagata ta samu ƙwarin gwiwa.

A watan Afrilu suka yi wata gagarumar nasara. Sun yi wasansu na farko bayan barin Kabul ƙarƙashin jagorancin wata koci ƴar Australiya, inda suka tashi 0-0 tsakaninsu da wata tawagar ƙasar.

Sai dai ƴan wasan na Afghanistan ba sa amfani da sunayensua jikin rigunansu na wasa sai dai lambobi - saboda tuna cewa ko da yake sun tsira, amma har yanzu iyalansu suna cikin haɗarin a kai musu hari a can ƙasarsu.

Amma ba su da wani tabbas na abin da za su fuskanta a gaba. Idan har suna so su fafata da wasu ƙasashen duniya, to dole su nemi goyon bayan Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Afghanistan (AFA), da kuma izinin Taliban, wacce kowa ya san ba za ta yarda ba.

A watan Satumba tawagar ta janye daga wasannin cancantar shiga Gasar Mata ta Cin Kofin yankin Asiya, wacce China ta yi nasarar lashewa.

The Afghanistan women's national team playing a non-official match in Australia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tawagar ƙwallo ta mata ta Afghanistan suna wasan sada zumunci a Australiya

Fifa

Fifa ta bayyana yanayin da ake ciki a Afghanistan a matsayin "mai sanya damuwa". Ta ce tana ci gaba da tuntuɓar hukumar AFA kuma ta sha alwashin ganin an bunƙasa wasan.

Amma ba za ta iya bayar da tabbas kan ko Fati da yan tawagarta za su iya sake wakiltar ƙasarsu ba.

Sai dai tawagar ƙwallo ta maza ta Afghanistan na ci gaba da wasanta, amma ba su yi wasan cancanta na Gasar Kofin Asiya na 2023 ba da aka yi kwanan nan. Shugaban hukumar AFA Mohammad Kargar bai ce komai ba da aka nemi yin hira da shi.

Gwiwar Fati ba ta sage ba.

A ƙarshe dai Carter ta gana da su Fati a Australiya a watan Afrilu.

Ta ce "Ƴan matan na da abin mamaki. Su ɗin gwarazana ne," in ji ta.