Ban san golan da zai buga mana wasan Tottenham ba - Arteta

Asalin hoton, Getty Images
Mikel Arteta ya ce ya fahimci damuwar da Aaron Ramsdale ya shiga, bayan da David Raya ya maye gurbinsa a wasannin Arsenal biyu na ƙarshe.
Raya - wanda Arsenal ta ɗauko a wannan bazara - ya fara buga wasansa na farko a wasan da ƙungiyar ta yi nasara kan Everton a ƙarshen makon da ya gabata, sannan ya buga wasan da Gunners ɗin ta doke PSV Eindhoven a gasar zakarun Turai ta ƙungiyar ta buga cikin tsakiyar mako.
Har yanzu Arteta bai yanke shawarar wanda zai fara wasa da Tottenham a ranar Lahadi ba.
Golan Ingila Ramsdale ya fara buga wa Arsenal wasanni 52 a jere kafin Raya wanda ya zo aro a bazara daga Brentford ya maye gurbinsa a Goodison Park a ranar Lahadin da ta gabata.
Arteta ya ce bai damu ya riƙa sauya masu tsaron gida kamar yadda zai yi wa duk wani dan wasa ba.
Da aka tambaye shi ko Ramsdale, wanda ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi na dogon lokaci a watan Mayu, zai dawo taka leda a wasan hamayyar arewacin Landan na ƙarshen mako, Arteta ya ce: "Ban yanke shawarar wanda zai fara wasan ba."






