Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Matsalar tsaro ƙaruwa take yi ko raguwa a arewacin Najeriya?
A daidai lokacin ake magana kan hare-haren ƴabindiga a Kwara da sauran jihohi Najeriya, da ma barazanar shugaba Amurka Donald Trump, hankali ya fara komawa kan muhawarar shin matsalar tsaro ƙaruwa take yi ko raguwa?
A farkon watan Fabrairu ne sojojin Najeriya suka ce suna samun nasara a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin Boko Haram da ISWAP a jihar Borno.
Rundunar sojin ta yi wanna iƙirarin ne bayan ta ce sojojinta sun kashe Abu Khalid, "mutum na biyu mafi girman muƙami a Boko Haram a yankin dajin Sambisa," kamar yadda ta bayyana a wata sanarwa.
Sanarwar ta ƙara cewa bayan Abu Khalid, dakarun ƙasar sun samu nasarar kashe waus mayaƙansa 10.
Sojojin sun kashe jagoran na Boko Haram ne kwana ɗaya bayan sojoji sun kawar da wani gawurtacen kwamandan Boko Haram, da ake kira Julaibib a yankin Gujba.
Ƙungiyar Boko Haram dai ta kwashe shekaru tana ƙaddamar da hare-hare kan jami'an tsaro da fararen hula musamman a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Tun bayan fara rikicin na Boko Haram a shekarar 2009, shugabannin ƙungiyar da suka fi ƙaurin suna su ne Muhammad Yusuf da ya assa ta, sai kuma Abubakar Shekau wanda ya karɓi jagoranci jagorancin ƙungiyar, kafin ɓallewar tsagin ISWAP ƙarƙashin jagorancin Abu Mus'ab Al-Barnawi.
Sai dai tun bayan kisan shekau a 2021, Boko Haram da ISWAP sun ci gaba da gudanar da ayyukansu a ware, ƙarƙashin jagorancin sabbin shugabanni, waɗanda a mafi yawan lokuta ba kowa ne ya san su ba.
A daidai lokaci da ake tunanin an samu sauƙin Boko Haram ne aka fara samun ɓullar ƴanbindiga.
Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da kashe Buharin Daji jagoran barayin shanu da suka addabi jihar da hare-hare.
Wani babban Jami'an gwamnatin jihar ya shaidawa BBC cewa jami'an tsaro sun mika wa mahukunta gawar madugun 'yan fashin.
Masu satar shanun dai sun kwashe shekaru suna kisan rayuka da satar shanu a jihar.
A watan Maris na shekarar 2018 ne aka kashe gawurtaccen ɗanbindiga, Buhari Tsoho, wanda aka fi sani da Buharin Daji a wani farmaki da aka kai masa da taimakon wasu abokan fashinsa da suka raba gari.
Ana tunanin kashe Buharin Dajin ne ya ta'azzara matsalar, inda aka samu ɓullar wasu jagororin ƴanbindigar da dama da suka bazu a yankunan ƙasar, musamman arewacin Najeriya, inda suka ci gaba da aikatasa ta'asa.
Ƙaruwa ko raguwa?
A game da muhawarar da ake yi kan ko matsalar ƙaruwa take yi ko raguwa, masani harkokin tsaro, Kabiru Adamu ya ce a nazarin kamfaninsu na tsaro na Beacon security and consulting limited, matsalar ƙaruwa take yi.
"Ba za a ce matsalar na raguwa ba a arewacin Najeriya. Idan muka yi la'akari da alƙaluman da muke tattarawa daga shekara biyar zuwa yanzu, za mu ga cewa matsalar tsaro na ƙaruwa ne a yankin," in ji shi.
Masanin tsaron ya ƙara da cewa kashe-kashen da ake yi na ƙaruwa ne a arewacin Najeriya.
"Misali a shekarar 2025, mutum 10,504 aka kashe a Najeriya, sannan idan aka tattara alƙaluman mace-macen da aka samu a sassan Najeriya, kusan kashi 88 cikin ɗari na wannan adadin a arewacin Najeriya aka yi."
Kabiru ya ce kashi 88 na adadin na nufin kusan mutum 8,090 ne suka rasu a yankin na arewacin Najeriya.
Ya ƙara da cewa daga cikin waɗanda aka kashe ɗin, yankin arewa maso yamma ne matsalar ta fi ƙamari.
A ɓangare garkuwa da mutane ma Kabiru Adamu ya ce matsalar ƙaruwa ta yi, domin a cewarsa, kusan kashi 90 na garkuwa da mutane a arewacin Najeriya aka yi.
"Haka kuma daga cikin wannan adadin, kusan kashi 67.45 na waɗanda aka yi garkuwa da su a arewa maso yamma ne," in ji shi.
A shekarar 2024 kuwa, Kabiru Adamu ya ce idan aka kwatanta da 2025, raguwa aka yi.
A cewarsa, garkuwa ta mutane raguwa ta yi daga 9,679 zuwa 8,523, wato raguwar kashi 11.94, "sannan waɗanda aka kashe ma sun ragu ne daga 11,692 zuwa 10,504 wato ragin kashi 10.16.
Hare-haren baya-bayan nan
- Harin Woro a jihar Kwara a ranar Talata 3 ga watan Faburairun 2026, inda aka kashe mutane aƙalla 78.
- Harin Ƙauyen Doma na ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina, a ranar Talata 3 ga watan Faburairun 2026, inda ka kashe mutum 21.
- Harin Kurmin Wali a ƙaramar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, wanda ya faru a ranar Lahadi 18 ga watan Janairun 2026, inda aka sace mutane fiye da 160.
- Harin Papiri na jihar Neja, inda aka sace ɗalibai fiye da 250 a ranar Juma'a, 21 ga watan Nuwamba, lokacin da 'yanbindigar suka auka wa makarantar St. Mary.
- Harin garin Maga a yankin ƙaramar hukumar Danko/Wasagu a jihar Kebbi, inda aka sace ɗalubai 25 a wata makarantar Sakandiren Ƴanmata.