Abubuwa 10 da suka kamata ku sani kan wasan El Clasico

Asalin hoton, Getty Images
Real Madrid za ta karɓi bakuncin Barcelona a La Liga, wasan farko na hamayya da ake kira El Clasico a bana ranar Lahadi a Santiago Bernabeu.
Real Madrid mai masukin baki tana ta ɗaya a kan teburi da maki 24, bayan cin wasa takwas da rashin nasara ɗaya a karawa tara baya a gasar.
Itama Barcelona mai karawa tara tana ta biyun teburi da tazarar maki biyu tsakani da Real Madrid, sakamakon cin wasa bakwai da canajaras ɗaya aka doke ta fafatawa ɗaya.
Wasan da aka kara a bara tsakanin Real Madrid da Barcelona
2024/2025
Spanish La Liga Ranar Lahadi 11ga watan Mayun 2025
- Barcelona 4 - 3 Real Madrid
Copa del Rey Ranar Asabar 26 ga watan Afirilun 2025
- Barcelona 3 - 2 Real Madrid
Spanish Super Cup Ranar Lahadi 12 ga watan Janairun 2025
- Real Madrid 2 - 5 Barcelona
Spanish La Liga Ranar Asabar 26 ga watan Oktoban 2024
- Real Madrid 0 - 4 Barcelona
Wannan karawar za ta bayar da damar fayyace ta ɗaya a kan teburi ga duk wadda ta ci wasan da zarar an kammala gumurzun mako na 10.
Kodai Real Madrid ta bayar da tazarar maki biyar, ko kuma Barcelona ta bai wa RReal tazarar maki ɗaya a wasan da za a buga a Santiago Bernabeu.
Jerin abu 10 da ya kamata ku sani kan El Clasico
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
1. Watakila a yi kan-kan-kan a yawan samun nasara a El Clasico
Idan har Barcelona ta yi nasara hakan na nufin za ta yi kan-kan-kan da Real Madrid a yawan cin wasanni.
Real Madrid ta yi nasara 105 a fafarawar El Clasico, ita kuwa Barcelona tana da 104.
2. Ko Barcelona za ta doke Real Madrid karo biyar a jere?
A kakar da ta wuce da Barcelona ta lashe babban kofin tamaula na Sifaniya, ta yi nasara huɗu a kan Real Madrid a jere, inda ta doke ta gida da waje a La Liga da Copa del Rey da kuma Spanish Super Cup.
Da zarar Barcelona ta yi nasara ya zama karo na biyar a jere tana cin Real Madrid a El Clasico, Pep Guardiola ya taɓa yin wannan bajintar a Barcelona.
3.Za a kara tsakanin ƙungiyoyin da ke kan gaba a zura ƙwallaye a La Liga
Filin wasa na Santiago Bernabeu zai karɓi bakuncin ƙungiyoyin da suka fi zura ƙwallaye a raga a bana a La Liga.
Barcelona ta ci ƙwallo 24 a wasa tara, ita kuwa Real Madrid ta zura 20.
4. Watakila a samu sabbin ƴan wasan da za su fara buga La Liga a karon farko
Bayan da wasu suka dade suna buga El Clasico, wasu sai a ranar Lahadi za su samu damar buga wasan farko daga ɓangaren Real Madrid da na Barcelona.
Watakila ƴan wasa shida daga Barcelona su fara yi mata El Clasico da ya haɗa da Rashford da Roony da Marc Bernal da Jofre Torrents da Dro da kuma Toni Fernández.
A ɓangaren Real Madrid kuwa watakila ƴan wasa biyar su fara yi mata El Clasico ranar Lahadi da ya haɗa da Dean Huijsen da Álvaro Carreras da Franco Mastantuono da Gonzalo García da kuma Alexander-Arnold.
5. Lamine Yamal, haɗari ne ga Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images
Lamine Yamal haɗari ne ga Real Madrid matukar zai buga wasan kuma yana kan ganiya. Kawo yanzu ya ci Real Madrid ƙwallo uku ya bayar da biyu aka zura a raga a karawa huɗun da ya fuskanci ƙungiyar.
6. Special edition Ed Sheeran jersey
Barcelona za ta buga El Clasico sanye da riga mai ɗauke da tambarin Play daga mawaki, Ed Sheeran, wanda a lokutan baya aka nuna wasu masu fasahar waka kamar Coldplay da Travis Scott.
Kungiyar mata ta riga ta sanya rigar a makon da ya gabata kuma ta yi nasarar cin Granada 2-0.
7. Kylian Mbappe yana kan ganiya

Asalin hoton, Getty Images
Kylian Mbappe ne kan gaba a cin ƙwallaye a Real Madrid a kuma La Liga da Champions League, wanda ya ci 15 ya bayar da biyu aka zura a raga a wasa 12.
Haka kuma Mbappe ya ci Barcelona ƙwallo 11 a wasa takwas da ya fuskanci ƙungiyar a dukkan fafatawa a lokacin da yake Paris St Germain da kuma yanzu a Real Madrid, saboda baraza ne ga Barcelona.
8. Wadda take ta ɗaya a kan teburi za ta fuskanci ta biyu a La Liga
Wannan wasan da za a buga zai fayyace wadda za ta ci gaba da jan ragamar teburi da zarar ta ci wasan.
Real Madrid tana kan teburi da maki 24, bayan cin wasa bakwai da rashin nasara ɗaya.
Ita kuwa Barcelona mai maki 22 tana ta biyun teburi, bayan nasara bakawi da canjaras ɗaya da rashin nasara ɗaya.
9. Real Madrid tana kan ganiya a wasannin gida
Kawo yanzu Real Madrid ta yi nasara takwas a gasar La Liga a gida, sai dai ba ta taɓa cin karo tara a jere ba a gasar tun bayan Fabrairun 2015 karkashin kociya, Carlo Ancelotti.
10. Mbappe da Rashford ne kan gaba a yawan kai hare-hare a raga
Kylian Mbappe ne kan gaba a yawan kai hare-hare a raga, inda ɗan kasar Faransa yake da 47 na Real Madrid
Shi kuwa ɗan wasan tawagar Ingila mai taka leda a Barcelona, Marcus Rashford ya kai hare-hare zuwa raga sau 27.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan wasan Real Madrid
Real Madrid ta bayyana ƴan wasan da za su kece raini da Barcelona a wasan mako na 10 a La Liga a Santiago Bernabeu ranar Lahadi.
Masu tsare raga: Courtois, Lunin, Sergio Mestre.
Masu tsare baya: Carvajal, Militão, Trent, Asencio, Á. Carreras, Fran García, F. Mendy, Huijsen.
Masu buga tsakiya: Bellingham, Camavinga, Valverde, Tchouameni, Arda Güler, D. Ceballos.
Masu cin ƙwallaye: Vini Jr., Endrick, Mbappé, Rodrygo, Gonzalo, Brahim, Mastantuono.

Asalin hoton, Getty Images
Ƴan wasan Barcelona
Wannan karawa ce da duk wani ɗan ƙwallo zai yi fatan bugawa, kuma wannan karon a Santiago Bernabeu, filin da komai zai iya faruwa.
To sai dai Barcelona za ta kai ziyara ba tare da Ter Stegen da Joan Garcia da Gavi da Dani Olmo da Raphinha da kuma Robert Lewandowski, sakamakon jinya
Ƴan wasa 22 da Barcelona ta sanar: Szczesny, Kochen, Eder Aller, Balde, R. Araujo, Cubarsí, Gerard Martín, Kounde, Eric, Jofre, Xavi Espart, Pedri, Fermín, M. Casadó, F. De Jong, Bernal, Dro, Ferran, Lamine Yamal, Rashford, Roony da kuma A. Fernández.










