Me ya sa Liverpool ke fuskantar ƙalubale a bana?

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta yi rashin nasara huɗu a jere a dukkan fafatawa a bana, wanda hakan ya sa wannan kaka ta zama daga cikin mafi muni gare ta tun bayan watan Nuwamban 2014.
Tun farko ƙungiyar ta fara kakar ta bana da kafar dama, inda magoya baya suka yi fatan za ta kare kambinta na kofin Premier League da ta ɗauka, inda a farko ta lashe wasa biyar a jere a gasar tamaula ta Ingila.
Cikin waɗanda ta yi nasara a kai sun haɗa da Bournemouth da Newcastle, da Arsenal da Burnley da abokiyar hamayya Everton.
Haka kuma Liverpool ta yi nasara kan Atletico Madrid a Champions League da yin waje da Southampton a Carabao Cup.
Kafin fara kakar bana, Liverpool ta kashe sama da fam miliyan 400 wajen sayen sabbin ƴan wasa, domin ganin ta mamaye kakar bana, kamar yadda ta yi a bara.
To sai dai bayan fara kakar bana Liverpool kan ci ƙwallon da ke ba ta nasara ne daf da tashi, in banda karawar da ta doke Everton.
Ciki har da wanda Bournemouth ta farke ƙwallo biyu, daga baya Liverpool ta sa ƙwazo ta samu maki ukun da ta ke bukata.
Shi ma wasan da ta yi nasara a kan ƙungiyar Sifaniya a daf da za a tashi ta ci ƙwallon a gasar Zakarun Turai da na Newcastle United a Premier League.
Tun daga nan alamomi suka fara bayyana cewar akwai tarin matsaloli a Liverpool, wadda kowacce wasa ƙwallo ke shiga ragarta in banda wanda ta yi nasara a kan Arsenal 1-0 a Premier League cikin Agusta da wanda ta ci Burnley 1-0 a cikin watan Satumba a Premier League.
Ƴanwasan da Liverpool ta saya kafin fara kakar bana

Asalin hoton, Getty Images
- Giorgi Mamardashvili daga Valencia
- Jeremie Frimpong daga Bayern Leverkusen
- Florian Wirtz daga Bayern Leverkusen
- Milos Kerkez daga Bournemouth
- Hugo Ekitike daga Eintracht Frankfurt
- Alexander Isak daga Newcastle United
- Armin Pecsi daga Puskas Akademia
- Giovanni Leoni daga Parma
- Freddie Woodman daga Preston North
- Will Wright daga Salford
Bari mu duba abinda ya faru da Liverpool a 2014
Jurgen Kloop bai yi rashin nasara ba wasa huɗu a jere a dukkan karawa a Liverpool, amma an doke shi hudu a jere a Premier League.
Rabon da a yi nasara a kan ƙungiyar Anfield wasa huɗu a jere tun Nuwambar 2014 karkashin Brendan Rodgers, wanda ya sha kashi 1-0 a hannun Newcastle United a Premier League da wanda Real Madrid ta yi nasara a Champions League da wanda Chelsea ta ci 2-1 da 3-1 da Crystal Palace ta yi nasara a kan Liverpool.
Daga nan ta tashi 2-2 a wasan gaba da Ludogorets ta Bulgaria, sai ta fara cin Stoke City lokacin da Glen Johnson ya ci mata ƙwallo da kai.
Sai dai Klopp ya sha kashi a wasa huɗu a jere a Premier League a hannun Brighton da Manchester City da Leicester da kuma Everton a Fabrairun 2021, amma sai yi nasara a Champions League a kan RB Leipzig.
Matsalolin da Liverpool ke fuskanta a bana
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
1. Matsalar masu buga mata tsakiya
Ƙungiyar Anfield ta samu sauye-sauye da yawa a fannin masu taka mata leda daga tsakiya, bayan da wasu daga ciki suka bar ƙungiyar, ya dace a ce ta haɗa fitattun da za ta fuskanci kakar bana.
Liverpool ta dauki Florian Wirtz daga Bayern Leverkusen, amma har yanzu ɗan wasan bai nuna kansa ba, inda yake ta shan suka daga magoya bayan da suke ganin kwalliya ba za ta biya kuɗin sabulu ba.
2. Raunin ƴanwasa da ke jinya
Raunin da wasu ƴanwasan Liverpool suka ji sun taka rawar gani da ƙungiyar Liverpool ke kasa kokari a kakar nan.
Daga ciki mai tsaron baya, Giovanni Leoni ya ji rauni a wasansa na farko a ƙungiyar, wanda ake cewa yana doguwar jinya.
Mai tsaron baya Alisson Becker ya ji rauni a lokacin Champions League, wanda ake cewar zai yi jinya har cikin watan Oktoba, watakila ya wuce hakan.
Haka shi ma Jeremie Frimpong ya samu rauni a watan Agusta, inda shi ma ke fama da jinya.
3. Bayan Liverpool na yoyo
A kakar bara bayan Liverpool ya yi yoyo, duk da cewar ƙungiyar Anfield ce ta lashe kofin, amma dai an samu matsaloli da yawa a bayan.
Kungiyoyi da dama sun amfana da kurakuren Liverpool a bara daga ciki har da Nottingham Forest da Brighton da kuma Brentford.
Wasu lokutan da zarar Liverpool ta kai kora sai kaga wagegen gibi tsakanin masu tsare baya da ƴan tsakiya.
Haka kuma tun kafin fara kakar bana, Liverpool ta buga wasannin atisaye, kuma tun a lokacin gurbin masu tsare baya ya nuna matasalar da ƙungiyar za ta iya fuskanta da fara kakar nan.
4. Samun canji daga Jurgen Klopp zuwa Arne Slot
Salon da Jurgen Klopp ya horar a Liverpool na kai hare-hare ne ta ko ina da sa matsi a tsawon lokutan da ya horar - daga baya wasu ƙungiyoyin sun fahimci yadda za su ɓullo wa ƙungiyar idan suka hadu.
Saboda haka salon da Klopp ya yi amfani da shi duk ɗanwasan da ba ya kan ganiya, sai ka ga ya shafi ƙwazon ƙungiyar.
Arne Slot wanda ya gaji Klopp da tarin ƴanwasa da suke kan ganiya, ya ci gaba da tsarin, kuma ɗanwasa ɗaya ya saya shi ne Chiesa.
Hakan ya sa Slot ya lashe kofin Premier League a kakarsa ta farko, koda yake wasu tun farko sun ga ɓaraka daga kociyan kan salon da yake fuskantar wasanni.
A kakar da ta wuce Liverpool ta kasa ɗaukar kofin Carabao da FA, wadda aka yi waje da ita a zagaye na biyu a Champions League a zagaye na biyu a hannun Paris St Germain.
Saboda haka da aka fara kakar bana, Slot ya sayo sabbin ƴan wasa, kuma ya kawo tsarinsa da ya fi sani, kenan ya sauka daga kan wanda aka san Liverpool.
Ba a taɓa tunanin Liverpool za ta fitar da makudan kuɗi don sayen ƴanwasa ba, kuma gurbin da take da matsala ya kamata ta mayar da hankali ba cefane mai yawa ba.
5. Kalubale ya karu a gasa
Gasar Premier League ta kara samun daraja tsakanin ƙungiyoyin da ke buga wasannin - koda yaushe ƙungiyoyin da suke kalubalantar kofin sai karuwa suke.
Da can sai a yi maka maganar ƴan huɗu, amma yanzu batun ya wuce ƴan bakwai ma, domin kowanne mako za ka ga ana buga wasan hamayya gudu uku zuwa huɗu.
Yadda Manchester City ta mamaye gasar a baya-bayan nan lamarin ya canja, kullum Arsenal fatan lashe kofin take yi.
Za ka yi maganar Chelsea ga Manchester United ga Tottenham ga Aston Villa da Bournemouth da sauran ƙungiyoyi da yawa.
Kenan kowacce kakar gasar Premier na kara tsauri, manyan ƙungiyoyi na cefane da kuma karawar hamayya a duk mako da ake yi daga uku zuwa huɗu.

Asalin hoton, Getty Images
6. Akwai gajiya daga ƴanwasa
Ƴanwasa na ɗauke da tarin gajiya a jikinsu, kuma dalilin da ya sa suke jin rauni koda yaushe kenan.
A bara an buga wasannin da yawa da ya hada da na Premier League da Carabao Cup da FA Cup da Champions League.
Haka kuma wasu ƴanwasan na zuwa suna buga wa tawagogin ƙasashensu wasanni har aka kammala kakar da ta wuce.
Idan aka auna lokacin da aka yi hutu da komawa buga gasar bana ba a samu lokuta da yawa ba, kenan gajiyar bara ba ta kare ba, sannan an shiga kakar bana.
7. Rashin kokarin ƴanwasa
Rashin ƙwazon Mohammed Salah a bana ya shafi ƙwazon Liverpool sosai.
Salah ne ya lashe takalmin zinare a Premier League a matakin wanda ke kan gaba a cin ƙwallaye da tazarar guda shida, wato da 29, kuma shi ne kan gaba a bayar da ƙwallo a zura a raga.
Ɗan wasan tawagar Masar ya kammala kakar bara da ƙwallo 34 a raga da bayar da 23 aka zura a raga a wasa 52 a dukkan fafatawa.
Sai dai kuma a kakar nan ya zura uku kacal a raga a wasa 11 - kuma rabon da ya ci ƙwallo tun ranar 17 ga watan Satumba a kan Atletico.
Wasan da ya bayar da ƙwallo aka zura a raga kuwa tun da Everton, kwana uku tsakani a Premier League.
Alexander Isak ne na biyu a yawan cin ƙwallaye a bara a Newcastle United, haka shi ma Wirtz ya ci ƙwallaye da yawa a Bayer Leverkusen.
To sai dai dukkan ƴanwasan ba sa kan ganiya har da Ryan Gravenberch.
8. Yadda Liverpool ta sayi ƴan wasa
Bayan da Liverpool ta fitar da makudan kuɗi wajen sayen ƴanwasa, wasu na cewar ba ta magance matsalarta ba, musamman gurbin tsakiya da masu tsaron baya.
Haka kuma ya ci a ce Liverpool ta sayi ƴanwasa a gurbin da take bukata, hakan zai sa ta yi takarar kara lashe kofin Premier League na 21 jimilla, cikin ruwan sanyi.

Asalin hoton, Getty Images
Karin wasu matsalolin da suka jefa Liverpool cikin garari
Liverpool ta sayo ƴanwasa kafin fara kakar bana, hakan ya sa ta sayar da wasu da take da su da ake ganin bai kamata ta rabu da su ba.
1. Luis Díaz
Díaz ya koma Bayern Munich kan fam miliyan 65.5.
Ɗan wasa ne da ya taka rawar gani a bara a Liverpool, tafiyarsa ta sa ƙungiyar ta rage kai hare-hare masu hatsari a wasanninta.
2. Caoimhín Kelleher
Mai tsaron raga, Kelleher ya bar Liverpool zuwa Brentford kan sama da fam miliyan 12.5 har zuwa fam miliyan 18 da karin tsarabe-tsarabe.
Koda yake ba shi ne kan gaba a tsare ragar Liverpool ba, inda Alisson Becker ne na ɗaya a ƙungiyar.
3. Jarell Quansah
Matashi Quansah, mai tsaron baya daga tsakiya kadara ce ga Liverpool, amma ta sayar da shi ga Bayer Leverkusen kan fam miliyan 30.
Bai kamata a ce Liverpool ta rabu da matashin ba, domin shi ne zai maye gurbin waɗanda shekarunsu suka ja.
4. Trent Alexander‑Arnold
Bayan da Arnorld ya bar Liverpool ya koma Real Madrid, an ɗan samu koma baya kan yadda ƙungiyar ke kai hare-hare.
Kuma wanda ke buga gurbinsa har yanzu bai nuna kansa ba, watakila na bukatar karin lokaci.











