'Baba-kere da son mulkin shugabanni ke tunzura zanga-zangar bayan zabe a Afirka'

Masu sharhi kan al'amuran da suka shafi harkokin zabe a Afirka sun fara tsokaci a kan yadda ake fuskantar zanga-zangar ƙin amincewa da sakamakon zaɓen da aka gudanar a wasu ƙasashe kamar Tanzania da kuma Kamaru.
Masanan sun ce tsananin son mulki na daga cikin dalilan da suke janyo zanga zangar kin amincewa da sakamakon zaɓen da aka gudanar a wasu kasashen.
Farfesa Muhammad Tukur Abdulkadir, Malami ne a shashen kimiyyar siyasa a jami'ar jihar Kaduna da ke Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, son rai na masu mulki da babakere da kuma mutu-ka-raba, ne ke janyo a samu tashin hankali a kasa bayan zabe.
Ya ce,"Kamar Tanzania, ita matsalarta ba iri daya ce da ta Kamaru da Ivory Coast ba, a Tanzania 'yar takarar kasar wato Samia Suluhu Hassan, yanzu ne zata yi takara ta farko, saboda karbar mulkin ta yi bayan shugaban kasar ya mutu."
Ya ce," Abubuwan da ke faruwa a Tanzania abubuwa ne masu ban mamaki sannan kuma kalubale ne ga masu jin cewa idan mata na da yawa a siyasa to abubuwa da yawa za su sauya."
Farfesa Tukur Abdulkadir, ya ce, "A kasashen Kamaru da kuma Ivory Coast kuwa batu ne na son mulki da kuma halin mutu-ka-raba, sannan kuma cutar da ke addabar irin wadannan kasashe masu tasowa ita cutar mutu-ka-raba a mulki."
Ya ce," Kamar misali a shugaban Kamaru wanda an yi zabe kuma shi ne ya sake samun nasara, kasa kamar Kamaru a ce an yi zabe har kusan mako uku ba a bayyana sakamako ba, to wannan manuniyace na irin yadda al'amura ke lalacewa da kuma rashin sahihanci da halaccin irin zaben da ake yi a irin wadannan kasashe."
Masanin kimiyyar siyasar, ya ce," Misali shugaban kasar Kamaru ya shafe shekaru 43 yana mulki, sannan kuma shekarun 92 a duniya, to amma saboda masifar son mulki irin na 'yan Afirka, yanzu ma shugaban zai kara wasu shekaru biyar yana mulki."
Ya ce," Wannan babban bala'ine a siyasar Afirka kuma babu alamar kawo karshen irin wannan abu na son mulki da babakere."
Farfesa Tukur Abdulkadir, ya ce,"Wani lokaci rarrabuwar kawuna da ke addabar kasashe masu tasowa musamman na Afirka na daya daga cikin abin da ke yiwa duk wani tsari ko yunkuri na yin juyin-juya-hali kafar ungulu."
"Kasassun shugabanni 'yan mutu ka raba akan mulki na amfani da irin rarrabuwar kawunan wajen kara raba kawunan mutane, manufar hakan ita ce su tabbatar da cewa jama'a basu samu hadin kai ba wajen 'yantar da kansu da kuma tunkurar masu musu yi musu zalunci da mulkin kama-karya."











