Alassane Ouattara ya lashe zaɓen ƙasar Ivory Coast karo na huɗu

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Nicolas Negoce
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Aiko rahoto daga, Abidjan
- Marubuci, Chiagozie Nwonwu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
- Lokacin karatu: Minti 5
Shugaban ƙasar Ivory Coast mai ci Alassane Dramane Ouattara ya lashe zaɓen shugaban ƙasar a karo na huɗu. Hukumar zaɓen ƙasar ta ce Outtara ya samu kusan kaso 90 na yawan ƙuri'ar da aka kaɗa a zaɓen ranar Asabar.
Mai biye masa, matar tsohon shugaban ƙasa, Simone Gbagbo ta samu kaso biyu da ɗoriya.
Mista Ouattara mai shekaru 83 zai ci gaba da zama a karagar mulkin ƙasar har nan da shekaru biyar masu.
An dai hana abokan hamayyarsa guda biyu da suka haɗa da shugaba Laurent Gbagbo daga yin takara. Hakan ya sa suka yi watsi da zaɓen inda suka kuma ayyana da shi da juyin mulki.
Yadda aka fafata

Raye-raye ne suka fi mamaye harkokin yaƙin neman zaɓe a Ivory Coast ta yadda nishaɗi da zaƙuwa suka danne batun fargabar da ake nunawa game da siyasar ƙasar ta Afirka ta Yamma wadda ta fi kowacce arzikin cocoa a duniya.
Shugaba mai-ci Alassane Dramane Ouattara - wanda wasu ke yi wa kallon gwarzon da ya kawo sauyi cikin shekara 15 da suka wuce bayan yaƙin basasa - na fuskantar suka daga masu adawa.
'Yan'adawa na kallon takarar wa'adi na huɗu da shugaban mai shekara 83 yake nema cin fuska ne ga dimokuraɗiyya, duk da cewa kundin mulki ne ya ba shi damar yin hakan.
An hana babban ɗan'adawa Tidjane Thiam yin takara a watan Afrilu bayan wata kotu ta yanke hukuncin cewa ya haƙura da kasancewarsa ɗan ƙasar lokacin da ya zama ɗan Faransa a 1987 - abin da ya musanta.
Sai kuma tsohon Shugaban Ƙasa Laurent Gbagbo da aka hana shi shiga zaɓen saboda ɗaure shi da aka yi a 2018 saboda aikata laifi.
Ƙin amincewar da Gbagbo ya yi da shan kaye a hannun Oattara a zaɓen 2010 ne ya jawo tashin hankalin bayan zaɓen da haddasa kisan fiye da mutum 3,000, wanda kuma ya jawo alawar cakuleti a duniya.
Duk da haka Oauttara na fama da ƙalubale mai girma musamman daga tsohuwar matar Bagbo, da kuma ɗaya daga cikin mafiya arziki a ƙasar. Sai dai kan su ba haɗe yake ba.
'Yantakara huɗu ne fafatawa a zaɓen:
- Simone Gbagbo, mai shekara 76, tshohuwar matar shugaban ƙasa, ta auri tsohon Shugaban Ƙasa Lauren Gbagbo
- Jean-Louis Billon, mai shekara 60, tsohon minista kuma ɗaya daga cikin mafiya arziki a ƙasar da ya samu dukiya daga hada-hadar man ja
- Henriette Lagou Adjoua, mai shekara 66, tsohuwar minista a former minister and prominent women's rights campaigner
- Ahoua Don Mello, mai shekara 67, tsohon minista kuma tsohon abokin siyasar Shugaba Gbagbo.

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Duk da cigaban tattalin arziki da aka samu ƙarƙashin Oattara, 'yana'adawa na fatan amfani da damar ƙorafin da talakawa ke yi waɗanda ba su amfana da cigaban da aka samu.
"Tattalin arziki na bunƙasa, amma ba mu jin sa," a cewar ɗantakarar adawa Billon na jam'iyar Democratic Congress (Code).
"Matasa ba su samun aikin yi, sannan rayuwa na ƙara tsada." Ya yi imanin cewa idan ta kai ga zagaye na biyu tsakaninsa da Shugaba Oattara "zai yi masa ritaya".
A gefe guda kuma, Simone Gbagbo, shugabar Movement of Capable Generations (MGC), ta kafa kanta a matsayin mai fafutikar kare haƙƙin talakawa.

Asalin hoton, MGC
Mai yawan murmushi da kuma yin shiga irin ta gargajiya, takan ja hankalin magoya baya kamar wata mawaƙiya.
Tana cikin haɗakar 'yan'adawa ta CPA-CI da suka dunƙule a farkon shekarar nan domin ƙalubalantar Ouattara.
"Shugaba Ouattara ya yi wasu abubuwa masu kyawu, amma ya lalata ɓangaren ilimi," kamar yadda ta sha faɗa wa magoya bayanta.
Yaƙin neman zaɓenta ya fi mayar da hankali kan ilimi, da koyarwa, da kasuwanci saboda da ma abubuwan da ta fi sani kenan.
Waƙar nan ta Coup du marteau (mahangurɓa) da mawaƙin gambara Tam Paiya ya rera ta zama wani taken yaƙin neman zaɓen Shugaba Ouattara da jam'iyyarsa ta RHDP.
"Shugaban na cikin yanayi mai kyawu kuma a shirye yake ya ci gaba da hidimta wa ƙasa," a cewar mai mgana da yawun gwamnati Adama Coulibaly.

Asalin hoton, AFP/Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Duk da sauya kundin mulki a 2016 wanda ya bai wa Oattara damar neman wa'adi na uku da huɗu, takararsa ta ɓata wa wasu rai a wannan karon, inda gwamnatinsa ta ta dinga murƙushe masu adawa da ƙarfi a kwanan nan.
An kama masu zanga-zanga fiye da 700 a farkon watan nan bayan 'yan'adawa sun yi maci, sannan aka yanke wa wasu 50 hukuncin zaman gidan yari na shekara uku.
Saboda mutane da dama sun fara ɗaukar matakan kariya.
"Mun bar birnin Adbijan mako ɗaya kafin zaɓen," kamar yadda wata uwa mai suna Ahoua Diomande ta faɗa wa BBC.
"Duk lokacin zaɓe sai an yi kashe-kashe da faɗace-faɗace."
Amma kuma akwai masu kyakkyawan fata da ƙwarin gwiwa, kamar Charm Matuba, wadda ta je Adbijan daga ƙasar Congo.
"Na san komai zai tafi lafiya. 'Yan Ivory Coast ba za su sake kashe kan su saboda 'yansiyasa ba," in ji ta.
"Ina fatan mutane za su fita zaɓe. Duka abokaina na goyon bayan Simone ne. Shuagaba ce mai cike da ƙwarin gwiwa. Za ta iya bayar da mamaki."

Asalin hoton, Reuters
Ouattara na da dandazon magoya baya a arewacin ƙasar, inda ake magana da harshen Dioula.
Simone Gbagbo kuma na da magoya baya sosai a yammaci - da kuma kudu maso yammaci, inda tsohon mijinta ke da farin jini.
Shi kuwa Billon na da farin jini tsakanin mazauna birane, waɗanda yake yi wa alƙawarin zamanantar da tattalin arziki da kuma sauyi mai ɗorewa.
"Abokin matasa ne," in ji Salifou Sanogo mai shekara 19. "Wannan ne karon farko da zan kaɗa ƙuri'a kuma na san zai yi nasara. Ouattara ya tsufa sosai, ya gaji kuma bai yi mana komai ba. Muna buƙatar sauyi, muna buƙatar Billon."
Gbagbo da Thiam ba su goyi bayan kowane ɗantakara ba. Amma Simone Gbagbo na samun goyon bayan Charles Ble Gounde, wanda tsohon abokin siyasar tsohon mijinta, wanda bai shiga takarar ba.

Asalin hoton, RHDP











