Paul Biya: Yadda shugaba mafi tsufa a duniya ya sake lashe zaɓen shugaban Kamaru

Paul Biya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Shugaban ƙasar Kamaru Paul Biya
Lokacin karatu: Minti 4

Shugaban ƙasar Kamaru mai shekara 92 a duniya ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar a karo na takwas, bayan da Majalisar Kundin Tsarin Mulkin ƙasar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 12 ga watan Oktoba.

Biya ya lashe zaɓen ne bayan ya samu kashi 53.66% na ƙuri'un da aka kaɗa, yayin da babban abokin hamayyarsa Issa Tchiroma Bakary ya zo na biyu da kashi 35.19%, kamar yadda Majalisar ta bayyana.

"Paul Biya ya zama zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, bayan ya samu mafi yawa na ƙuri'un da aka kaɗa," in ji Clement Aatanga, shugaban Majalisar Kundin Tsarin Mulki ta ƙasar.

Kashi 57.76% ne na waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri'a suka fita domin yin zaɓen, inda kashi 42.24% suka ƙaurace.

Kimanin mutum miliyan hudu ne suka kaɗa ƙuri'a a zaɓen.

Ƴantakar 10 ne suka fafata a zaɓen na shugaban ƙasar Kamaru na 2025, inda Biya, wanda bai taɓa rashin nasara ba a zaɓe ya lashe.

Sai dai gabanin ayyana sakamakon zaɓen, babban ɗan takara na hamayya Issa Tchiroma Bakary ya bayyana cewa shi ne ya lashe zaɓen.

A wata tattaunawa da BBC, Bakary ya ce ba zai bari "a danne wa al'ummar Kamaru hakkinsu ba."

Manyan ƴantakara biyu na zaɓen Kamaru

Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty Images

Zaman ɗarɗar

An dai tsaurara tsaro a ƙasar a wani shirin ko ta kwana, yayin da harkokin kasuwanci suka tsaya cak gabanin fara sanar da sakamakon zaɓen.

Tun da farko an tsara sanar da sakamakon zaɓen a ranar Alhamis da ta gabata, sai dai majalisar tsarin mulkin ƙasar mai alhakin sanar da sakamakon zaɓen ta ɗage zuwa yau Litinin.

Zaɓen ya fi zafi ne tsakanin Shugaba Paul Biya da ya shafe shekara 43 yana jagorancin ƙasar da kuma jagoran adawa Issa Tchiroma Bakary.

Wane ne Paul Biya?

An haifi Paul Biya ne a ranar 13 ga watan Fabrailun 1933, kuma shi ne shugaban ƙasar Kamaru tun daga shekarar 1982.

Kafin na ya kasance firaministan ƙasar daga shekarar 1978 zuwa 1982 a zamanin mulkin shugaban ƙasar Ahmadou Ajidjo.

Shi ne shugaban ƙasa na biyu da ya fi daɗewa a mulki a nahiyar Afirka bayan tsohon shugaban Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, sannan a yanzu shi ne wada ya fi daɗewa yana mulki a jere a duniya idan an cire ƙasashen da ke mulkin sarauta, sannan kuma shi ne shugaban ƙasa mafi tsufa a duniya a yanzu.

Shugaban mai shekara 92 a yanzu ya sake lashe zaɓen shugaban ƙasar wanda aka yi a ranar 12 ga watan Oktoba.

Wannan shi ne karo na takwas da ya yi takara kuma ya samu nasara, kuma zuwa yanzu ya shafe shekaru 43 a karagar mulki.

Shugaba Paul Biya ya ce ya yanke shawarar tsayawa takara ne bayan kiraye-kirayen hakan da ake ta yi masa a ciki da wajen ƙasar.

Zanga-zangar bayan zaɓe

An dai samu ɓarkewar zanga-zanga a biranen Garuoa da Doula, lamarin da ya kai ga mutuwar aƙalla mutum huɗu, kamar yadda hukumomin ƙasar suka tabbatar.

Ɗaruruwan magoya bayan ɗantakarar adawa, Issa Tchiroma Bakari ne suka fito zanga-zangar.

Hukumomi sun ce an kai wa ƴansanda da jami'an tsaro hari ne, dalilin da ya sa suka kare kansu.

Tchiroma Bakary ya ƙalubalanci shugaba Paul Biya - wanda ya shafe shekara 43 yana shugabanci a ƙasar.

Tuni jagoran adawar ya ayyana cewa shi ne ya yi nasara a zaɓen, duk da cewa a yau Litinin ne ake sa ran sanar da sakamakon a hukumance.

Ba za mu yarda a danne wa al'ummar Kamaru hakkinsu ba - Bakary

Tuni dai jagoran adawar ƙasar, Issa Tchiroma Bakary ya ayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen na ranar 12 ga watan Oktoba.

A wata hira da BBC, Tchiroma Bakary ya ce ba zai amince da maguɗi ba a sakamakon zaɓen da ake shirin sanarwa ranar Litinin.

Ya ce tawagarsa ta tattara bayananta ne daga alƙaluman da ta haɗa daga rumfunan zaɓe, saboda haka babu tantama game da su.

Tchiroma Bakary, mai shekara 76, tsohon minista ne wanda ya raba gari da shugaba Paul Biya, mai shekara 92 a duniya.

Sai dai jam'iyya mai mulki ta yi watsi da iƙirarin samun nasarar da Tchiroma Bakary ya yi kuma jami'an gwamnati da dama sun bayyana matakin nasa a matsayin abin da ya saɓa wa doka, domin Majalisar Kundin Tsarin mulki ce kawai za ta iya bayyana sakamako a hukumance.