Dalilaina na cewa ni ne na lashe zaɓen Kamaru - Issa Tchiroma

Asalin hoton, Anadolu Agency via Getty Images
Madugun adawa a jamhuriyar Kamaru, Issa Tchiroma Bakary ya tattauna da wakilin BBC a Kamaru, Paul Njie dangane da iƙrarin da ya yi cewa shi ne ya lashe zaɓen ranar 12 ga watan Okotoban 2025.
Ga yadda tattaunawar ta kaya tsakanin Paul Njie da Issa Tchiroma Bakary.
Paul Njie:
Me ya sa ka ayyana kanka a matsayin mutumin da ya yi nasarar a zaɓen shugaban ƙasa tun ba a kammala ƙidaya ƙuri'a ba?
Issa Tchiroma:
Mun zaɓi mazaɓu da suka fi muhimmanci a ƙasar – guda 18. Mun karɓi dukkan takardun sakamakon zaɓen da aka tattara a mazaɓu bisa doka da oda. Bayan mun kammala hadawa, sai muka fahimci cewa mun sami fiye da kaso 60, inda shi kuma mai biye mana yake bayanmu da kaso 30. Mun yi abun a buɗe kuma mun bai wa kowa dama idan yana son ya ƙalubalanci abin da muka yi sannan a shirye muke idan sakamakon namu na da matsala sai um gyara abin da muka yi. E, haka ne, ni ne na lashe zaɓen idan kuma akwai wanda zai kalubalance ni, to a shirye nake.
Paul Njie:
Jam'iyyar CPDM mai Mulki ta ce sakamakon da ka fito da shi na da matsala kuma bay a nuna gaskiyar ƙuri'un da aka kaɗa. Me za ka ce?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Issa Tchiroma:
Me kake zaton za su faɗi bayan sun riga sun sha ƙasa? Abun da aka saba ne ayi iƙrarin cewa bayananmu ba daidai suke ba. Babu wanda zai iya yi saboda mun kashe lokacin da ya kamata; mun tattara dukkan ƙwararru domin taimakon mu wajen tabbatar da cewa alƙalumanmu ba kuskure a ciki. Ka ga hakan ne ya sa a yau muke samu nutsuwa. Kuma muna da tabbacin cewa idan sakakamakon da shugaban Mjalaisar Tsarin Mulki ya sanar shi ne abin da jama'a suka zaɓa, babu wata tantama. Babu wanda za iya ƙalubalantar mu.
Paul Njie:
Me ya sa ba ka jira Majalisar Tsarin Mulki ta sanar da sakamakon a hukumance kamar yadda doka ta tanada? Me ya sa ka yi gaban kanka ka ayyana kanka a matsayin wannan da ya yi nasara?
Issa Tchiroma:
Doka ba ta hana mu yin abin da muka yi ba. Dokar zaɓe ta bai wa malaman zaɓe su bayyana sakamakon rumfunansu. Abin da muka yi kenan kuma mun yi hakan ne bisa dokar. Dokar ba ta hana mu yin hakan ba.
Paul Njie:
Kuma dai wannan dokar ce ta amince da kwanaki 15 mafi tsayin lokacin da Majalisar Tsarin Mulkin ƙasar ke da wajen sanar da sakamakon zaɓen. Me ya sa ka yi zumudin ayyanawar kwana biyu bayan kaɗa ƙuri'a?
Issa Tchiroma:
Kamar yadda na faɗa, doka ba ta hana mu yin hakan ba. Baby mutum da zai iya zargin mu a yau saboda mun yi hakan.
Paul Njie:
Gwamnati ta ce abin da ka y iya saɓa doka. Kana tsoron cewa nan da wasu ƴan kwanaki za a iya kama ka?
Issa Tchiroma:
A tsare ni? Za su iya tsare ni idan sun ga dama. Kafin zaɓen ma sun yi min gargaɗi. Tun ma kafin zaɓen lokacin da na yi murabus daga muƙamina, shugaban ƙasa ya sa na fahimci cewa za a iya kama ni. Za a saka ni a kurkuku. Ya gamsu cewa bayan watanni biyu zan iya mutuwa ne idan ban sami maganin cutukan da nake fama da su ba. Amma na faɗa cewa to shi kenan duka bin da ka ga ya yi maka . Mutane za su zamar min kariya sannan Allah zai kare ni. Ban yi komai ba da ya saɓa doka ba. Na san abin da suke cewa ina nan gida kuma a shirye nake. Su zo su ɗauke ni su saka ni a kurkuku amma na san na riga na lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Paul Njie:
Idan aka bayyana wani daban ba kai ba a matsayin wanda ya yi ansara, za ka hakura ka taya shi murna?
Issa Tchiroma:
Domin ƙaunar mulkin dimokraɗiyya, zan iya yarda da kai amma idan dai har Majalisar Tsarin Mulki ta sanar da sakamakon daidai da abin da al'umma suka zaɓa ba mahuɗi ba.
Paul Njie:
Wasu ƙwararru da masu sharhi sun yi gargaɗi cewa rikicin da muke gani a ƙasar nan ka iya ruruwa idan aka saki sakamakon zaɓen nan. Amma kuma kai ga shi kana neman jama'a su hau kan tituna.
Issa Tchiroma:
Na nemi mutanen su kare ƙuri'unsu. Ba za taɓa amincewa da ƙwace ƙuri'un da jama'a suka zaɓa ba. Ƴan ƙasar sun sani kamar yadda duniya ta sani ita ma cewa mun kayar da jam'iyyar CPDM. Babu tababa ko kaɗan cewa mu ne muka yi nasara.
Sakamakon zaɓen shiyyoyin Kamaru a taswira
Ku taɓa kan yanki ko shiyyar da kuke son sanin samakonsa a wannan taswira. BBC tana sabunta sakamakon zaɓen na shiyya-shiyya da zarar hukumar zaɓe ta sake shi.
Sai dai kuma Majalisar tsarin mulkin jamhuriyar Kamaru ce kawai ke da damar sanar da sakamakon ƙarshe na zaɓen.











