Yadda alƙalai suka yi watsi da zargin maguɗi a zaɓen Kamaru

Wani mutum bayan kaɗa ƙuri'a a rumfar zaɓe a birni Yaounde na Kamaru, a ranar 12 ga watan Oktoban 2025

Asalin hoton, AFP via Getty Images

Bayanan hoto, Lokacin da aka ɗauka ana jiran sakamakon zaɓen ya jefa fargaba a zukatan mutane
    • Marubuci, Paul Njie
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Yaoundé
  • Lokacin karatu: Minti 2

Alƙalai a Kamaru sun yi watsi da buƙatar da aka gabatar masu ta neman ko dai su soke wasu sakamakon zaɓen shugaban ƙasar ko kuma su soke zaɓen baki ɗaya, inda suka ce za su sanar da sakamako a ranar Litinin.

Zanga-zanga ta ɓarke a wasu manyan biranen ƙasar, inda ƴan adawa suka yi zargin an tafka kura-kure a zaɓen na ranar 12 ga watan Oktoba.

Alƙalan kotun tsarin mulki sun yi watsi da ƙorafi har takwas da aka gabatar masu, domin a cewar su babu cikakkiyar shaida mai tabbatar da su.

Ɗan takarar ƴan adawa, Issa Tchiroma Bakary ya bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaɓen, wani iƙirari da shugaba Paul Biya mai shekara 92 a duniya, wanda kuma ke neman wa'adin mulki na bakwai.

Shekaru 43 kenan Biya yana mulki a Kamaru, kuma sau ɗaya kacal ya bayyana a wajen yaƙin neman zaɓen bana.

Tchiroma Bakary, 76, is a former government spokesman who broke ranks with Biya to challenge him for power.

Tchiroma Bakary mai shekara 76 da haihuwa, tsohon kakakin gwamnatin Biya ne, wanda a yanzu yake neman ƙwace mulki a hannunsa.

Ya ƙi yarda ya tura nasa ƙorafi zuwa kotun kundin tsarin mulkin ƙasa, kuma ya zaɓi ayyana kansa a matsayin ''Halartacce shugaban ƙasa.

A wani saƙon shafukan sada zumunta da ya fitar, Tchiroma Bakary ya ce ya lashe zaɓen bayan samun kashi 55 cikin ɗari na jimillar ƙuri'un da aka kaɗa.

Ya ce ''Idan har majalisar kundin tsarin mulki ta gaza hukunta maguɗi ta kuma zaɓi goyon bayan maguɗi, to babu shakka ta kauce hanya''.

Tchiroma Bakary ya kuma yi gargaɗin cewa ''jama'a za su juya masu baya da kuma yi masu barazana.

Jam'iyyar shugaba Biya ma ta yi watsi da iƙirarin Tchiroma Bakary na samun nasara a zaɓen tana mai cewa majalisar kunɗin mulki ce kaɗai ke da ikon sanar da sakamako.

Zaman jiran sakamakon da ake ciki a Kamaru ya jefa tsoro da fargaba a zukatan jama'a.

Cocin Katolika ma ta shiga maganar a farkon makon nan, inda ta buƙaci alƙalan kotu su tabbata sun yi adalci.

A woman looking at her mobile phone and the graphic BBC News Africa

Asalin hoton, Getty Images/BBC

Go to BBCAfrica.com for more news from the African continent.

Follow us on Twitter @BBCAfrica, on Facebook at BBC Africa or on Instagram at bbcafrica