Tasirin da yawan ƙarin kuɗin ruwa ke yi ga masu masana'antu a Najeriya

Lokacin karatu: Minti 3

A ranar Talata ne Babban Bankin Najeriya CBN ya sake ƙara kuɗin ruwa zuwa kashi 27.50 cikin 100, yana mai cewa domin a daƙile hauhawar farashi.

Matakin ya zo ne bayan taron babban kwamatin CBN mai kula da harkokin kuɗi na Monetary Policy Committee (MPC), inda aka ɗaga kuɗin ruwan daga kashi 27.25 cikin 100.

Matakin na nufin duk wanda ya karɓi bashin kuɗi daga bankunan kasuwanci sai ya biya kashi 27.50 na kuɗin da ya karɓa a matsayin kuɗin ruwa.

Sai dai masu masana'antu da 'yankasuwa da sauran masu ruwa da tsaki sun koka kan ƙarin da cewa zai ƙara jefa masana'antu da harkokin kasuwanci cikin mawuyacin hali da kuma durƙusar da su.

Wannan ne karo na shida da CBN ke ƙara kuɗin ruwan tun daga watan Fabrairun 2024. A watan Satumba ne bankin ya mayar da kuɗin kashi 27.25 jim kaɗan bayan raguwar hauhawar farashi a watan Agustan 2024.

A farkon watan nan kuma hukumar ƙididdiga ta ƙasa ta (NBS) ta ce hauhawar farashi a Najeriya ta kai kashi 33.88 cikin 100 a watan Oktoba, inda aka samu ƙari kan 32.7 ta watan Satumba.

Gyaran tattalin arziki na cikin abubuwan da Shugaba Bola Tinubu ya sha yin alƙawari a lokacin yaƙin neman zaɓe. Sai dai gyare-gyaren nasa sun haifar da tsadar rayuwa, da hauhawar farashi - waɗanda ya ce yana sane da su kuma na ɗan lokaci ne.

'An mayar da masu masana'antu 'yan tireda'

Matakin da Babban Bankin Najeriya ke ɗauka na musamman ne, saboda ba a saba ganin irinsa ba a ƙasashen duniya, wanda ya fi shafar masu masana'antu.

Sai dai CBN ɗin na cewa yana yin hakan ne domin daƙile hauhawar farashi ta hanyar taƙaita tsabar kuɗi a hannun ɗaiɗaikun mutane.

Sani Hussaini Saleh, mamba a majalisar ƙoli ta masu masana'antu ta Naajeriya, ya ce ƙare-ƙaren sun sa da yawan masu masana'antu sun daina karɓar bashin.

"Yana dakushe mana ayyuka saboda da ma ba mu iya karɓar bashi daga bankunan kasuwanci," in ji shi.

"Babu yadda za a yi ka karɓi bashi mai kuɗin ruwa na kashi 27 cikin 100, ka sarrafa kaya, ka biya albashi, ka biya kuɗin wuta, ina tabbatar maka da wuya a ce an samu riba."

Ya ƙara da cewa matakin ya fara mayar da masu masana'antu masu sayen kaya kawai suna sayarwa.

"Mataki ne da ke rugurguza masana'antu. Yawanci an mayar da mutane 'yan tireda kawai, ya fi wa mutum sauƙi ya karɓo kayan kawai ya sayar ya zuba ribarsa a aljihu."

Shi ma Abubakar Kantoma, mataimakin shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin arewacin Najeriya, na ganin ƙara kuɗin ruwan zai fi shafar masana'antu a yankin arewacin Najeriya.

"Yanzu wane kasuwanci mutum zai yi a Arewa da har za su samu ribar da za su biya wannan bashin?" kamar yadda ya tambaya.

"Abin da muke faɗa wa masu masana'antu shi ne su je su tattauna da bankuna da kansu, amma babbar matsalar da muke fuskanta ita ce akasarin bankunan ba na Arewa ba ne, saboda haka ko mutum ya je ba sauraronsa suke yi ba.

"Da ma can kuɗin ruwan ya hana mutanenmu zuwa karɓar bashin saboda ya yi tsada. To yanzu kuma an sake ƙarawa, wanda zai bai wa bankunan damar ɗaga kuɗin a wajensu har zuwa 32 cikin 100."

Ko mece ce mafita a wannan yanayi?

Sani Hussaini Saleh na ganin ya kamata Najeriya ta yi koyi da ƙasashe kamar China, inda kuɗin ruwan nasu ba shi wuce kashi ɗaya cikin 100.

Sai dai akasarin waɗannan ƙasashen ba su da hauhawar farashi irin ta Najeriya.

"Galibin ƙasashe masu tasowa kamar Indiya, da China, da wuya ka ga an karɓi kuɗin ruwa da ya wuce kashi ɗaya ko biyu," a cewarsa.