Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Dalilai uku da ke sa wasu ma'aikatan Najeriya cin kuɗin fanshonsu tun kafin ritaya
Bayanai na nuna cewa wasu ma'aikatan Najeriya da ba su kai shekarun ritaya ba na karɓar wani kaso daga kuɗaɗensu na fansho sakamakon matsin tattalin arziki.
Sabuwar dokar fansho ta 2014 dai ta bai wa ma'aikata damar cire kaso 25 na fanshonsu idan aka kore su ko suka bar aiki sannan suka kwashe watanni huɗu ba tare da samun wanin aikin ba, alhali shekarunsu na haihuwa ba su kai 50 ba.
Har wayau, dokar ta kuma bai wa ma'aikata damar karɓar wani kaso na kuɗaɗen fanshon nasu domin mallakar gidaje.
Hukumar fansho ta Najeriya ta ce ma'aikata 443,720 ne suka karɓi kuɗaɗen da suka kai yawan naira biliyan 182.19 tun lokacin da aka fara tsarin fanshon da ma'aikaci da ma'aikata kan biya wani kaso, a 2004, ya zuwa watan Disamban 2022.
Wani rahoto da hukumar Fansho ta Najeriya ta fitar ya nuna yadda ma'aikata 10,299 da suka rasa ayyukansu suka karɓi kuɗin da ya kai naira biliyan 7,688 a watanni huɗun farko na 2023.
Dalilan da ke sa ma'aikata karɓar wani kaso na kuɗin fansho
Wani masanin tsarin fansho a Najeriya wanda ba ya son a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa dalilai uku ne ke sa ma'aikatan da shekarunsu ba su kai na ritaya ba su karɓi wani kaso daga ajiyar tasu kamar haka:
- Matsin tattalin arziƙi: Akwai ma'aikata da dama da ke yanayin tsadar rayuwa da ake fuskanta yanzu haka a Najeriya ke tilasta su neman kaso 25 na abin da suke da shi musamman ma waɗanda suka rasa aiki ko su bar aikin.
- Masu son wadaƙa: Akwai ajin ma'aikatan da suke cire kaso 25 na kuɗaɗen nasu da sunan za su mallaki gidaje mma daga bisani sai su karɓe kuɗin nasu su yi wadaƙa da su ba wai don suna fuskantar matsin tattalin arziƙi ba.
- Masu yi wa tsarin fansho kallon takura: Akwai kuma ma'aikatan da dama can su ba su gamsu da tsarin fanshon ba kuma idan da za su samu dama to za su karɓe kuɗaɗensu. Saboda haka suke amfani da damar da suka samu ta amfani da kaso 25 na jimillar abin da suka tara.
Yadda wasu ke fakewa da sunan mallakar gidaje
Masanin tsarin fanshon wanda kuma ma'aikaci ne a ɗaya daga cikin kamfanonin da ke kula da tsarin na fansho ya ce " a yanzu haka a duk mutum 10 da ke zuwa wajenmu domin karɓar kaso 25, shida daga cikinsu masu neman bayar da kafin alƙalami ne domin mallakar gidaje."
"To sai dai binciken da muka yi mun gano cewa da dama daga cikin ma'aikatan da fakewa da ƙoƙarin mallakar gidajen ne amma daga baya sai karɓe kuɗaɗensu."
"Abin da suke yi shi ne suna haɗa baki da bankunan da ke samar da gidaje da ake kira PMI da masu gina rukunin gidaje, inda za su kawo mana takardun gidaje da duk abin da ake nema. Mu kuma sai mu sakar musu kuɗin tunda mun ga komai lafiya-lafiya. Amma daga baya sai su yi wani tsarin da zai ba su damar karɓe kuɗaɗensu." In ji masanin tsarin fanshon.
'Ni ma na karɓe nawa'
Wani ma'aikaci da ba ya son a ambaci sunansa ya shaida wa BBC cewa shi ma ya karɓi kaso 25 daga kuɗaɗen ajiyarsa na fansho.
"Tuni na karɓe nawa kuma na san akwai mutane da dama a ofis ɗinmu da su ma suna gab da karɓar kuɗin da sunan buƙatar biyan kuɗin gida.
Matsalar ita ce idan ka karɓa za ka iya juya su yadda za su samar maka alkairi musamman idan kana da tsarin yin kasuwanci." In ji ma'aikacin da ya karɓi kaso 25 na fanshonsa domin biyan buƙatun gabansa.
Illar cinye fansho kafin shekarun ritaya
Masanin ya ce duk da cewa dokar fanshon ta 2014 ta bai wa ma'aikatan Najeriya damar cire kaso 25 daga ajiyar tasu, "amma akwai babbar illa ga ma'aikaci."
"Babbar matsala da idan ba a magance ta ba to muradin gwamnati na ganin ta rage talauci da damuwa a tsakanin masu ritaya, zai zama ɓata lokaci saboda ma'aikaci ya riga ya cinye babban kaso daga ajiyar tasa." In ji masanin wanda kuma ke aiki a ɗaya daga cikin kamfanonin fansho na Najeriya.
Me ce mafita?
Masanin ya ce mafita ita ce "dole ne gwamnati ta sanya ido kan sahihanci ko rashinsa na buƙatar da ma'aikatan ke da ita wajen karɓar kuɗaden nasu."
Sai dai kuma ya ƙara da cewa gwamnatin ta tanadi horo mai tsanani ga ma'aikatan da ke karɓar kuɗin nasu da bamkunan da ke taimaka musu cimma hakan da ma su kamfanonin na fansho.
"Misali idan ma'aikaci ya karɓi kaso 25 na ajiyar tasa kuma aka gano cewa bai yi abin da ya ce zai yi da kuɗin ba kamar yadda ya nema ba. Idan ma'aikaci ya nemi kudin da sunan biyan kuɗin gida amma sai aka gano kashe kuɗinsa kawai ya yi. To ya kamata a yi masa hukunci yadda lokacin da zai yi ritaya sai a hana shi kudin sallama na farko."
"Dangane kuma da bankunan da ke samar da gidaje da kamfanonin fanshon su ma ya kamata idan aka same su da laifi a hukunta su domin ya zama izinina ga masu son yi irin haka a gaba." In ji masanin.