Me ya sa ƴanbindiga ke yawan kai wa jami'an tsaron Najeriya hare-hare?

Wani jami'in soja rike da bindiga a kusa da wata motar soji da hari ya ona
Lokacin karatu: Minti 5

Hare-haren ƴanbindiga kan jami'an tsaron Najeriya na ci gaba da ɗaukar hankalin masana tsaro da ma ƴan ƙasar baki ɗaya.

A makon da ya gabata ne wasu mahara suka far wa jami'an tsaro da ke sintiri a ƙaramar hukumar Katsina-Ala da ke jihar Binuwai tare da kashe jami'an tsaro aƙalla 10, kodayake daga bisani hukumomi sun ce jami'ai uku ne suka mutu.

Bayanai sun ce maharan riƙe da muggan makamai, sun buɗe wa jami'an sibil difens wuta a lokacin da suke sintiri a yankin.

Hare-haren ƴanbindiga kan jami'an tsaro ba baƙon al'amari ba ne a Najeriya, musamman yankunan da ke fama da rikice-rikice.

A lokuta da dama mayaƙan Boko Haram riƙa kai wa sojoji hare-hare har cikin sansanoninsu tare da kashe dakaru masu yawa.

Haka ma a wasu yankunan kudu maso gabashin ƙasar, ƴan IPOB sun riƙa far wa ofissoshin ƴansanda hate da cinna musu wuta a baya.

Wasu jami'an tsaron kuma sun gamu da ajalinsu ne a musayar wuta da ƴanbindiga ko dasa musu abin fashewa, ko buɗe musu wuta a shigayen bincike da sauransu.

Me ya sa ƴanbindiga ke far wa jami'an tsaro?

Dakta Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Security mai nazarin al'amuran tsaro a yankin Sahel ya ce babban dalilin da ya sa ƴanbindiga ke kai wa jami'an tsaro hari shi ne dabarar yaƙi.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

''A duk lokacin da ake irin wannan yaƙi na sari-ka-noƙe buƙatar kowane ɓangare shi ne karya logon abokin faɗa, don haka kai wa jami'an tsaro hari tamkar rage musu dama da ƙarfi ne'', in ji shi.

Ya ce abu na farko shi ne kai wa jami'an tsaro hari na karya musu gwiwa da ƙarfinsu, sannan kuma hakan na karya ƙarfin gwiwa da jama'a ke da shi kan jami'an tsaron.

''Kuma hakan na rage wa jami'an tsaron goyon bayan da suke samu daga jama'ar gari, kuma hakan na tasiri sosai a yaƙin da jami'an tsaron ke yi'', in ji Dakta Kabiru Adamu.

Masanin tsaron ya ƙara da cewa wani abu da ke sa ƴanbindiga kai wa jami'an tsaro hare-hare shi ne neman ɗaukaka tsakanin takwarorinsu ƴanbindiga.

''Musamman ƙungiyoyi masu alaƙa da wasu na ƙetare kamar Boko Haram mai alaƙa da ƙungiyar Al-qaeda, da kuma ISWAP mai alaƙa da ISIS, to irin waɗannan hare-haren na ɗaga darajar ƙungiyoyin a idanun uwayen nasu'', in ji shi.

Shugaban kamfanin Beacon Security ya ce hare-haren kan jami'an tsaro zai sa shugabannin waɗannan ƙungiyoyi su samu karɓuwa da ɗaukaka a wajen manyan ƙungiyoyin uwayen nasu.

Me hakan ke nufi ga tsaron Najeriya?

Sojojin Najeriya

Asalin hoton, Nigerian Army

Dakta Kabiru Adamu ya ce hari kan jami'an tsaro babbar barazana ce ga tsaron kowace ƙasa.

Musamman idan sojoji a ka kai wa harin , kamar yadda ya yi ƙarin haske.

''Sojoji su ne ƙololuwa a fannin tsaron kowace ƙasa, ma'ana idan sauran fannonin tsaro suka gaza sojoji ake kai wa don magance kowace irin barazana''.

Ya kuma ƙara da cewa a duk lokacin da aka kai wa cibiyoyin soji hari , to tamkar ƙasa ce gaba ɗaya aka kai wa hari.

''Kuma hakan zai fito da raunin martabar ƙasa na kare kanta daga barazana'', kamar yadda ya bayyana.

Shugaban na Beacon Security ya ce tsaron Najeriya na buƙatar gyara, kasancewa ƴanbindiga na iya kai wa sojoji - waɗanda su ne ƙokaluwa a fannin tsaro - hari har a sansanoninsu.

Ya ƙara da cewa matsawar jami'an tsaro - da ke da makamai - ba su tsara da hare-haren ƴanbindiga ba, to ina ga sauran fararen hula, waɗanda ba su da makaman kare kai.

Me ya kamata jami'an tsaron su yi?

Wasu sojojin Najeriya

Asalin hoton, Nigerian Army

Akwai buƙatar jami'an tsaron su ɗauki matakan daƙile wannan barazana, domin karya logon ƴanbindigar.

Shugaban kamfanin Beacon Security ya zayyano wasu matakai da ya ce ya kamata jami'an tsaro su ɗauka don magance kai musu hare-hare da sua haɗa da:

  • Inganta tsaro sanya idanu da bibiya.

Dakta Kabiru Adamu ya ce ya kamata jami'an tsaro su ingatan tsarin sanya idanu dabibiya.

Ya ci gaba da cewa a wasu lokuta ƴanbidigar kan taso daga wani wuri su yi doguwar tafiya aƙalla kilomita 10, don haka za iya ganinsu.

''Akwai ma wani hari da sai da ƴanbindigar suka yi tafiyar kilomita 70 kafin su isa wurin jami'an taron da suka kai wa hari, sannan suka koma tafiyar kilomita 70'', kamar yadda ya yi ƙarin bayani.

''Inda akwai daburun sa idanu da bibiya a ire-iren waɗannan wurare hakan zai bai wa jami'an tsaron damar daƙile harin tare da kama na kamawa da kuma kashe na kashewa'', in ji shi.

  • Haɗin kai tsakanin jami'an tsaro

Masanin tsaron ya ce wani abu da ya kamata jami'an tsaron Najeriya su inganta shi ne haɗin kai tsakanin duka ɓangarorin tsaron ƙasar.

''A tsarin tsaron ƙasa akwai ɓangarori guda 29 masu ruwa da tsaki a fannin, sai kuma wasu 13 ko 14 da ke taimaka musu, to yana da kyau a samu kyakkyawar fahimta tsakaninsu, ta yadda za su yi aiki tare don cimma abin da ake buƙata.''

Dr Kabiru Adamu

Asalin hoton, Beacon Consulting

Bayanan hoto, Dr Kabiru Adamu, shugaban kamfanin Beacon Security, mai nazarin tsaro a yankin Sahel
  • Haɗa kai da jama'ar gari

Dakta Kabiru Adamu ya ce yana da kyau jami'an tsaro su sanya jama'ar gari cikin waɗanda ke taimaka wa inganta tsaro domin su bayar da gudunmawarsu.

''A duk lokacin da ƴanbindiga suka yi doguwar tafiya, dole za su wuce garuruwan mutane, kuma inda da haɗin kan jama'a, an sanya su ciki za su sanar da jami'an tsaro halin da ake ciki'', in ji shi.

  • Amfani da fasahar zamani

Masanin tsaron ya ce yana da kyau jami'an tsaro su riƙa amfani da sabbin abubuwa fasaha na zamani a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyi ƴanbindiga a ƙasar.

''Yanzu misali akwai wata sabuwar fasahar da aka girke a jihar Legas mai suna ''Falcon eye'' da ke sanya idanu kan matsalar tsaro, ita wannan fasaha daga Legas za ta iya hango jihar Borno da ma kan iyakar Najeriya''.

''Sai dai na rasa dalili da ya sa ba a amfani da wannan fasaha ko ire-iren waɗannan na'urorin a yankunan da ake fama da matsalar tsaro'', in Dakta Kabiru Adamu.

Ya ce waɗannan su ne manyan matakan da ya kamata jami'an tsaron su ɗauka don daƙile kai musu hare-hare a sansanoninsu.

Haka kuma ya lissafo wasu abubuwan da ya kira ƙananan dalilai da suka haɗa da:

  • Bai wa jami'an tsaro wadatattun kuɗi
  • ba su wadatattun makamai na zamani
  • Kula da walwalarsa
  • Inganta tsaron sansanonsi
  • Sabbin jirage na zamani/marasa matuƙa
  • Sabbin ababen hawa na zamani