Yadda Lakurawa suka kashe yansanda uku a Kebbi

Asalin hoton, Getty Images
Rundunar ƴansandan Najeriya ta ce ta tsaurara matakan tsaro a garin Zogirma na yankin ƙaramar hukumar Bunza ta jihar Kebbi, bayan wani hari da wasu da ake zargin ƴan ƙungiyar Lakurawa ne suka kaddamar, inda suka kashe jami'an ƴansanda uku.
Rundunar ta ce bayan ƴansanda uku da aka kashe a yayin harin, akwai kuma wasu fararen hula biyu da suka samu rauni.
Kakakin rundunar ƴansandan jihar Kebbi, CSP Nafi'u Abubakar ya ce ''Jami'an mu da aka girke a Zogirma zuwa Tilli sun samu hari daga wasu da ake zargin ƴan ta'addan Lakurawa ne, inda suka yi musayar wuta kuma sanadiyyar haka su jami'an mu uku sun rasa rayukan su.''
CSP Nafi'u Abubakar ya ce itama rundunar ƴansandan ta yi wa maharan mummunar illar a lokacin arangamar.
''Su kan kwase mutanensu da aka illata ko aka kashe, amma dai mun tabbatar da in shaa Allahu wasu daga cikin su, su ma sun rasa rai wasu kuma sun gudu da raunuka,'' in ji CSP Nafi'u Abubakar
Kakakin rundunar ƴansandan ya ce tuni rundunar ta tura ƙarin jami'anta na kwantar da tarzoma zuwa yankin domin kwantar da hankalin jama'a da kuma daƙile duk wani yunƙuri na kai masu hari.
Ya ce: ''Kwamishinan ƴansanda na Jihar Kebbi CP Muhammed Sani ya ziyarci wannan yanki kuma ya tattauna da al'umma domin ganin cewa an inganta tsaro a yankin.''
Wani mazaunin Zogirma ya shaidawa BBC cewa ''Ƴan bindiga ne kawai suka shigo mana, suka sami Mobile Police a nan check point ɗinsu kawai suka buɗa masu wuta, har ya yi sandiyyar mutuwar mutum uku a cikin Mobile Police ɗin.
''Jama'a gari da suka ji ƙarar bindigogin to nan ne wasu suka tashi su je can su duba, to da suka ga alamun su ne kuma ana harbe-harbe sai kowa ya dawo gida, mata suka shiga gida, maza kuma wasu suka je daji irin a je a ɗan samu inda za su laɓe don tunanin ko za su shigo gari.''
Ya kuma tabbatar da cewa gwamnan jihar da kuma kwamishinan ƴansanda duk sun ziyarci mutanen garin, inda suka yi jaje da kuma bayar da tabbacin ɗaukar matakan da ya kamata a ɗauka don samar da tsaro.
Fatan al'ummar garin na Zogirma dai bai wuce ganin an cika alƙawarin da aka yi, na samar masu ƙwararan matakan tsaro masu dorewa ba, domin daƙile ci gaban aukuwar irin wannan matsala a nan gaba.











