Haaland ya ci Bayern a wasansa na farko a Manchester City

Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images

Sabon dan kwallon da Manchester City ta saya a bana, Erling Haaland ya fara ci mata kwallo a wasan da ta doke Bayern Munich 1-0 a Amurka.

Kungiyoyin biyu sun buga wasan sada zumunta a tsakaninsu domin gwada sabbin 'yan kwallon da suka saya, don shirin tunkarar kakar da za a fara cikin Agusta.

Sau biyu ana dakatar da wasan, sakamakon karar tsawa da ta auku a lokacin tsaka da fafatawar a Wisconsin.

Haaland, wanda ya koma City kan fam miliyan 51.2 daga Borussia Dortmund, ya ci kwallon a minti na 12 da fara karawar ta sada zumunta.

Mai shekara 22, bai buga wa City wasan farko da ta yi da Club America ba, bayan jinya da ya yi.

Haaland ya ci kwallon ne, bayan da Jack Grealish, wanda shi ne yafi taka rawar gani a fafatawar ya bugo tamaula, shi kuwa dan wasan Norway ya sa kafa ta fada raga.

City za ta koma Ingila, domin shirye-shiryen fuskantar Liverpool a karawar Community Shield da za su yi ranar Asabar a filin Leicester City, wato King Power.

Erling Haaland

Asalin hoton, Getty Images