Tun yana ƙarami burinsa shi ne ya yi fice - Mahaifin Elon Musk

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Maria Jevstafjeva
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Russian
- Lokacin karatu: Minti 5
Elon Musk shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a faɗin duniya, mutumin da ya zuba jari a fannin fasahar zamani, wanda kuma ke da dama ta musamman a ofishin shugaban Amurka.
BBC ta tattauna da mahaifinsa, Errol Musk domin jin yadda yaruntar hamshaƙin attajirin ta kasance, da yadda ta tallafa wa rayuwar mutumin da ake yi wa laƙabi da ''ɗan ƙaramin shugaban Amurka''.
"Ya aika min da wasu kuɗi domin sayen injin jirgin sama da nake son saya,'' in ji Errol, yayain da yake bayyana hulɗa ta baya-bayan nan tsakaninsa da ɗan nasa mai matuƙar tasiri.
''kuɗina ba su kai ba don haka ya aiko min da cikon kuɗin da zan saya. Don haka na ce na gode''.
Ya ce an yi hakan ne kwana guda kafin hirarmu da shi.
Mun yi hirar da Errol Musk ta hanyar mafani da manhajar Zoom daga ƙauyensa da ke kusa da gaɓar teku a kusa da Cape Town, inda ya bayyana a nutse cikin ƙwarin gwiwa.
Makonni da suka gabata muka buƙaci yin hira da shi, kan yaruntar ɗan nasa, kuma mun yi mamakin yadda ya ''amince'' kwana guda bayan aike masa da buƙatar.
Elon - wanda aka haifa a Pretoria, babban birnin Afirka ta Kudu a 1971 - ya taso ne a hannun mahaifinsa - wanda injiniya ne, da kuma mahaifiyarsa Maye mai tallar kayan ƙawa.
Bayan rabuwar auren iyayensa ya ci gaba da zama tare da mahaifinsa a Afirka ta Kudu, kafin komawarsa Canada a 1989.
Errol ya ce a lokacin tasowarsa ɗan nasa ''yaron kirki ne, da ba shi da fitina'', wanda a koyaushe ke samun abin da yake buƙata.
Ya ce ya sani babban burin Elon shi ne ya zama ''kan gaba''.
A yau Elon ya mallaki kamfanin Tesla da SpaceX da kuma X (Twitter a baya), sannan yanzu ya fara harkar ƙirƙirarriyar basira. A watan Fabrairu Mujallar Wall Street Journal ta ƙiyasta dukiyarsa da dala biliyan 419.4.
Ya kuma kasance ɗaya daga cikin mashawartan shugaban Amurka masu tasiri, kuma shugaban sabuwar hukumar kula da kashe kuɗaden gwamnati da Trump ya ƙirƙira.
Tashi cikin cuzgunawa
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Dangata tsakanin Elon da mahaifinsa ya jima da taɓarɓarewa, kuma ya bayyana wa marubucin tarihin rayuwarsam Ashlee Vance cewa yarintar ɗan nasa a matsayin maras daɗi.
"Ƴan daba su riƙa korarka daga makaranta, sannan su zo gida, abubuwa ne dai marasa daɗi a nan," kamar yadda ya bayyana.
Ɗaya daga cikin ƴan'uwan Elon, mai suna Kimbal ya shaida wa wani marubuci, Walter Isaacson cewa maihaifin nasu ya riƙa zaginsu a lokacin da suke yara.
"Zai yi ta yi muku hayaniya, ya kwashe sa'o'i yana muku jawabi, ya riƙa kiranku marasa amfani da sokaye tare da maganganu da ba su dace ba.''
A wata hira da ya yi a 2017, Elon Musk kiya mahaifinsa da ''mutumin banza''
Errol ya ce bai san me ya sa Elon zai faɗi haka ba. "Ina yin magana da shi sosai a yanzu. Na tabbata in ya tuna lokacin zai iya nadama."
"Ka tuna cewa waɗanan yara a wasu lokuta na gasa da iyayensu maza,'' in ji shi.
Errol ya yarda cewa aikin sojin ne ya yi tasiri a kansa
''An gaya muku cewa dole ne kuyi aiki. Ku kasance mazaje masu ƙarfi a ko'ina, ciki har da gida," in ji shi.
Errol da ɗan nasa, Elon na da wasu abubuwan da suka yi kamanceceniya: Dukkansu ƴan kasuwa ne, ana ɗaukar dukansu a matsayin masu janyo ce-ce-ku-ce, kuma dukkansu na da ƴaƴa. Errol na da ƴaƴa bakwai, yayin da aka yi amanna Elon na da 14.
Errol na sukar ɗan nasa kan watsi da wasu daga ciin ƴaƴan nasa, saboda aiki, amma shi ya ce yana ƙoƙarin ba su kulawa, ba tare da nuna bambanci ko wariya ba.
A lokacin hirar, Errol ya manta ɗaya daga cikin ƴaƴan nasa, ƴarsa ta huɗu - wadda mahaifiyarta ta kasance agola a gidansa, Jana Bezuidenhout. Jana ta shiga iyalan Musk a lokacin da take ƴar shekara huɗu, a lokacin da Errol ya auri mahaifiyarta Heidi.
Na yi mamakin lokacin da farko Errol ya ce yana da ƴaƴa mata uku, sai daga baya kuma ya gyara, inda ya ce yakan manta da ita (ƴar tasa ta huɗu).
Jana ta haifi ɗanta na farko a lokacin da take kusan shekara 30, yayin da Errol ya zarce 70, daga baya kuma ta haifi ɗanta na biyu, sai dai a yanzu ba sa tare.
An ce matsalarsu ce ta haifar da rigima tsakanin Errol da Elon Musk, duk da cewa Errol ya ce daga baya sun sansanta.
Siyasa da zage-zage

Asalin hoton, Getty Images
Mun tuna wa Errol lokacin da Elon ya fito fili ya zagi ministan harkokin wajen Poland, inda ya kira shi ''ƙaramin mutum''. Shi ya damu da ganin dan nasa na zagin mutane a fili?
"Ina matuƙar damuwa ga duk wata kalma da Elon ko wani daga cikin ƴaƴana ya furta saboda fargabar kada su jefa kansu cikin matsala,'' in ji Errol.
"Tun lokacin da yake ƙarami, na sha faɗa masa cewa kada ka yarda ka zagi manya ko ka ce musu banzaye,'' in ji mahaifin attajirin.
"Kuma yakan tambayeni dalili yana mai cewa ''banzayen ne ai''. Sai na ce masa ''e banzayen ne, amma ba za ka gaya musu ba.''
Amma Errol ya yi imanin cewa akwai irin haka a siyasar duniya: ''Mutane za su iya sukar junansu a yau, gobe kuma su ƙulla ƙawance.''
Duk da hujjar tasirin Elon a fagen mulkin Amurka, Errol ya yi amanna cewa siyasa ba ta dace da ɗan nasa ba.
"Shi ƙwararren mai fasaha ne, kuma mutane masu fasaha, sun fi son abubuwa masu amfani,'' in ji shi, yana mai cewa Elon na ƙoƙarin aiki da kowaɗanne irin mutane. "Dole ka yi aiki da fitattun mutane , amma za su iya zama cikakkun sokaye.''
Amma wannan ba shi ne ra'ayin Errol ga duka ƴansiyasa ba. Akwai wasu da yake yabawa shi da iyalansa - daga ciki akwai Shugaban Rasha Vladimir Putin.
"Ida ka kali Putin a matsayinsa na mutum - ba a matsayin siyasar duniya ba - za ka girmama shi,'' a cewar Errol.
"Yakan yi magana mai hankali, don haka zai yi wahala bai burgeka ba."
Da aka tambaye shi ko Elon na ba shi shawara kan abubuwansa, Errol ya tabbatar da cewa ɗan nasa ba ya tuntuɓarsa.
A lokacin da aka bayyana masa mamayar da Putin ya yi wa Ukraine, Errol ya dage cewa ''Lokaci ne kawai zai bayyana wanda ya fara'', duk kuwa da hujja ƙarara da ake da ita na hare-haren Rasha.
A lokacin hirar, na sha dariya har da hawaye, musamman a lokacin da na ƙalubalance shi kan ra'ayinsa na siyasa.
Errol ya yarda cewa kai ayyukan kamfanin Starlink mai samar da intanet zuwa Ukraine a farkon yaƙin, mataki ne mai kyau, amma yayin da yaƙin ya tsananta, ra'ayin Elon ya sauya.
Ya yi watsi da iƙirarin cewa Elon ya sauya matsaya kan kuɗi, yana mai cewa ''Danginmu na da komai - babu wasu kuɗi da muke buƙata, muna da komai.''
Yayin kammala hiriar na tambayi, Errol ko akwai wani abu game da Elon da mutane ba su sani ba, sai ya ce ɗan nasa ba shi da ƙwarin gwiwar magana a bainar jama'a.
"Yakan ji kunya'', har yanzu yana koyon yadda zai yi magana a gaban dandazonjama'a,'' in ji shi.
"Duk abin da zai ce, yakan faɗe shi da sauri."











