Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Binciken Gaskiya: Da gaske ne sojojin Najeriya da Nijar sun ƙwace ɗaruruwan 'Ak 47' daga ƴan bindiga?
Sashen binciken gaskiya na BBC ya gano cewa wasu hotuna da aka rinƙa yaɗawa a shafukan sada zumunta na gwamman bindigogi ƙirar AK47 da aka tara a wani ɗaki ba daga Najeriya ko Nijar suke ba, kamar yadda aka rinƙa yaɗawa.
Hotunan waɗanda suka karaɗe shafukan sada zumunta musamman WhatsApp, an yi rubutu da ikirarin cewa gamayyar sojojin Najeriya da Nijar ne suka kama makaman.
Haka ma akwai wani shafi na Zinariya a Facebook da ya wallafa wannan labarin a ranar 18 ga watan Agustan 2022 da misalin 10:42 na dare.
Duk da cewa mutum bakwai ne suka rarraba hotunan haka kuma biyar suka tofa albarkacin bakinsu, amma duk da haka sai da wannan labari ya karaɗe WhatssApp inda mutane suka rinƙa yaɗa labarin suna cewa wannan alama ce da ke nuna irin nasarar da ake samu kan ƴan bindiga a arewa maso yammacin Najeriya.
A 2021 ne dai gwamnatin Najeriya ta ayyana ƴan bindiga a matsayin ƴan ta'adda.
Sai dai BBC ta yi amfani da manhajar Google Lens inda ta bi diddigin hoton kuma wani shafin intanet na Olympia ne tun asali ya wallafa hotunan a ranar 27 ga watan Maris ɗin 2022.
Mayaƙan Rasha ne suka ƙwace bindigogin na'uin AK47 a birnin Zaporizhzhia, kamar yadda shafin Olympia ya bayyana.
Rasha ta ƙwace iko da birnin Zaporizhzhia kuma a nan ne tashar nukiliya mafi girma ta Turai take.
Haka kuma wani saƙo da aka wallafa a Twitter a ranar 29 ga watan Afrilun 2022 kuma a cikin saƙon an saka hoton bindigogin.