Muhimman abubuwa 10 da suka faru a duniya a 2019

    • Marubuci, Daga Badariyya Tijjani Kalarawi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Broadcast Journalist

Wannan shafi zai yi waiwaye kan abubuwan da suka faru a wasu kasashen duniya da ba za a manta da su ba, daga kasashen Turai da Afirka da yankin Asiya, har zuwa Gabas Ta Tsakiya.

Amurka

A ranar 31 da watan Oktoba ne majalisar wakilan Amurka ta kada kuri'a domin ci gaba da yunkurin tsige Shugaba Donald Trump.

Ana zargin Mista Trump da amfani da kujerarsa wajen sanya shugaban Ukraine Voladymyr Zelensky ya tuhumi dan abokin hamayyarsa Joe Biden.

Ranar 18 zuwa 19 ga watan Disamba 'yan majalisar wakilai a Amurka suka jefa kuri'ar da ta tabbatar da tsige Shugaba Trump, bisa wasu laifuka guda biyu.

Mista Trump dai shi ne shugaban Amurka na uku da aka taba tsigewa cikin sama da shekara 200.

A watan Junairun 2020 ake sa ran 'yan majalisar dattijan kasar za su yanke hukuncin karshe ko dai a tsige shi ko akasin haka.

Birtaniya

A ranar 24 ga watan Mayu ne Firai Ministar Birtaniya Theresa May ta sanar da yin murabus daga mukaminta a matsayin shugabar jam'iyyar Conservative mai mulki.

A jawabinta na bankwana cikin kuka Misis May ta ce: "Hakika abin alfahari ne da daukaka da na zamo mace ta uku da ta jagoranci kasar nan muna kuma fatan ba ta karshe ba. Ina yi bakin ciki da na gagara fitar da Birtaniya daga Tarayyar Turai."

Ranar 23 ga watan Yuli aka zabi Boris Johnson a matsayin wanda zai maye gurbinta. An gudanar da zabe a watan Disamba inda Boris Johnson ya yi nasara, yayin da Jam'iyyar Labour karkashin jagorancin Jeremy Corbin ta sha kaye.

China

Kasashen Amurka da China sun ci gaba da yakin kasuwanci tsakaninsu.

A cikin shekarar 2019 Amurka ta sanya wa kayan da China ke shiga da su kasarta harajin dala biliyan 550, yayin da China ta mayar da martani da sanya wa kayan Amurka harajin dala biliyan 185.

Sai kuma kama shugabar kamfanin Huwawei mallakar kasar China wato Meng Wanzhou da aka yi a kasar Canada. Ma'aikatar shari'ar Canada ta ce an tsare Meng Wanzhou ne a Vancouver, bisa umarnin Amurka kan zargin yin biris da takunkumin da Amurka ta kakaba wa Iran.

Koriya ta Arewa

Koriya ta Arewa ta yi gwajin makamai masu linzami a lokuta mabanbanta a shekarar 2019. Ta yi gwaji sau biyu a watan Mayu, sai watan Yuli da Agusta da Satumba da Oktoba da kuma Nuwamba.

Gwaji mafi girma da Koriya ta Arewa tayi shi ne na makami mai cin dogon zango da zai iya kaiwa har Amurka.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya gana da takwaransa Kim Jong-Un na Koriya ta Arewa a birnin Hanoin na Vietnam, batun gwajin makamai masu linzami da lalata cibiyar kera su ita ce a sahun gaba a tattaunawarsu.

Saudiyya

A ranar 30 ga watan Satumba ne aka fara samun muryar sirri da aka nada kan yadda aka kashe dan jarida kuma dan Saudiyya Jamal Khashoggi a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Santambul na kasar Turkiyya.

Wakilan Majalisar Dinkin Duniya da ke jagorantar binciken sun karkare kan cewa an kashe Khashoggi ba tare da shari'a ba.

Kafin zuwan wannan rana Saudiyya ta sha suka daga kasashen duniya kan yadda aka kashe Jamal da daddatsa sassan jikinsa da kasa bayyana inda gawar take ko yadda aka yi da ita.

Bayan zargin Yarima Muhammad bin Salman da hannu a kisan da ya musanta, an gurfanar da mutum 11 gaban shari'a.

A ranar 23 ga watan Disamba aka yanke wa mutane uku zaman shekaru a gidan kaso, tare da yanke wa wasu biyar hukuncin kisa.

A ranar 3 ga watan Yuli ne kuma hukumomin Saudiyya suka sanar da wasan casu na farko da za a yi a kasar, a wani bangare na sauye-sauye da yarima Muhammad bin Salman ke yi a kasar.

An sanar da cewa fitacciyar mawakiya Nicky Minaj za ta gwangwaje a kayataccen wurin da aka shirya a birnin Riyadh a ranar 18 ga watan Yulin, to amma wannan ya sha suka daga ciki da wajen kasar musamman wadanda ke ganin bai kamata kasa kamar Saudiyya ta amince da abin da mutane ke yi wa kallon badala ba.

Daga bisani a watan Agusta Nicky ta sanar da janye zuwa casun, inda mawakan salon kidan Solo na BTS 'yan Korea suka fara cashewa, sai kuma mawakan Amurka 50 Cent da Jannet Jackson da Chris Brown suka halarta.

Sai wani batun da ya ja hankali a kasar Saudiyya na bai wa 'yan yawon bude ido biza ba tare da muharrami ba, sai batun damben Boxing na mata da aka yi duk dai a cikin shekarar 2019.

Masar

A ranar 17 ga watan Yuli ne tsohon shugaban kasar Masar da aka hambarar da gwamnatinsa a shekarar 2013 wato Muhammad Morsi ya rasu a cikin kotu, a daidai lokacin da ake sauraren karar da ake zarginsa da hannu a kisan masu zanga-zanga, da taimaka wa kungiyoyin Hamas ta Falasdinu da Hezbolla ta Lebanon.

Marigayi Morsi mai shekara 67 bai jima da jawabi ba a cikin kotun ya yanke jiki ya fadi a cikin kejin da yake tsaye.

Su dai hukumomi sun ce ya mutu ne sanadiyyar bugun zuciya.Batun inda za a binne shi ma ya tayar da kura saboda gwamnatin Masar ba ta bari an kai shi makabartar iyalansa ba.

Isra'ila

A watan Afrilu aka gudanar da zabe a kasar Isra'ila inda Firai Minista Benyamin Netanyahu da Benny Ganzt suka fafata. Sakamakon kuri'un da aka kada sun nuna mutanen biyu sun yi kunnen doki.

Don haka dole aka tafi zagaye na biyu na zaben a watan Satumba, nan ma babu nasara, Netanyahu ya bazama zawarcin kananan jam'iyyun siyasar kasar da nufin kafa gwamnatin hadaka, daga bisani ya amince ya gaza sama wa jam'iyyarsa isasshen rinjayen da take bukata na kafa gwamnati

Kwatsam a ranar 22 ga watan Nuwamba babban mai shigar da kara a Isra'ila ya tuhumi Firai Minista Netanyahu da aikata laifukan cin hanci da rashawa da wawure dukiyar kasa da kuma zamba.

Duka wadannan tuhume-tuhumen na cikin wasu shari'u uku ne masu alaka da juna.

Ana tuhumar Mista Netanyahu da karbar kyaututtuka daga wasu attajiran 'yan kasuwa, kuma a dalilin haka ya rika yin watanda da dukiyar kasar domin kafofin yada labarai su rika yaba masa, amma ya musanta zarge-zargen.

Ita ma uwargidan Firai Ministan Sara Netanyahu ta bayyana gaban wata kotu a birnin Kudus don amsa tuhumar aikata ba daidai ba game da yin amfani da dukiyar kasa ba bisa ka'ida ba, ta hanyar bayar da odar abinci na sama da dala 12,000. An kuma bukaci ta dawo da kudin cikin gaggawa sanna aka yi mata tarar dala 3,000.

Wannan shari'a ta Sara ta kunyata Mista Netanyahu, da karfafa tunanin jama'a cewa ahalin gidansa na rayuwar kece raini da facaka da dukiyar kasa.

Myanmar

A ranar 10 ga watan Disamba ne aka fara zaman sauraren zargin kisan gillar da aka yi wa tsirarun Musulmai 'yan kabilar Rohingja a kasar Myanmar.

An zargi sojojin Myanmar da yin amfani da karfin da ya wuce kima kan tsirarun Musulman a shekarar 2015, lamarin da ya tilasta wa sama da mutum 742,000 gudun hijira zuwa makwabciyar kasar wato Bangaldesh.

Sudan

An gudanar da zanga-zangar da ba a taba ganin irinta ba a kasar Sudan. Zanga-zangar ta fara ne saboda tsadar kayan masarufi ciki har da burodi da rashin aikin yi ga matasa.

A watan Afirilu zanga-zangar da zaman dirshan din 'yan kasar a biranen Khartoum da Oumdurman ta rikide ta zama bukatar Shugaba Omar al-Bashir da ya shafe sama da shekara 30 a kan mulki ya yi murabus.

A wannan Disamba aka hambarar da mulkinsa tare da kai shi gidan kaso, kan zargin aikata laifukan yaki a Dafur da sace dukiyar kasa.

An kuma gurfanar da shi gaban kotu. A shari'ar farko da aka fara masa an yanke masa daurin shekara biyu a gidan kaso kan kisan masu zanga-zanga.

Zimbabwe

An wayi gari ranar 6 ga watan Satumba da rasuwar tsohon shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe a kasar Singapore bayan fama da rashin lafiya.

Mista Mugabe ya rasu yana da shekara 95, shi ne shugaban kasar na farko bayan karbar 'yancin kai daga turawan mulkin mallaka.

Ya shafe sama da shekara 30 a kan mulki, kuma shi ne jagaba a karbar 'yancin Zimbabwe. An yi fadi tashi da zazzafar zanga-zangar da ta sanya shi sauka daga mukami ba don ya shirya ba.

An yi takaddama kan inda za a binne Mista Mugabe, yayin da gwamnati ke son a binne shi a makabartar gwarazan kasar, iyalansa sun hana hakan.

Daga bisani an binne shi a mahaifarsa da ke garin Kutama, bayan mako uku da rasuwarsa.

Habasha

A ranar 10 ga watan Mayu jirgin Ethiopian Airlines mallakar kasar Habasha ya yi mummunan hatsari, jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin Addis Ababa zuwa Nairobin kasar Kenya.

Jirgin ya fadi a kusa da garin Bishoftu, dauke da fasinja da ma'aikata sama da 157 da suka fito daga kasa 30, kuma babu wanda ya tsira da rai.

Kawo yanzu babu wasu bayanai da aka fitar kan musabbabin faduwar jirgin. Sai dai akwai korafin samfurin jirgin na Boieng 737 yana da matsalar na'ura.