An kirkiro manhajar gano kalaman ta'addanci

Asalin hoton, PA
Gwamnatin birtaniya ta ce ta taimaka wajen kirkiro wani sabon manhaja wacce za ta iya gano abubuwan da su ka kunshi ta'addanci a shafikan yanar gizo sannan ta goge su a take.
Ministar harkokin cikin gidan Birtaniya Amber Rudd, ta je Amurka domin tattauna batun manhajar da kamfanonin fasaha tare kuma da yunkurin rage ta'addanci.
Sabuwar manhajar wacce wani kamfanin fasaha a Landan ya kirkiro na amfani ne da wata ma'ajiya mai girma wacce ta kunshi abubuwan da kungiyar IS su ke sawa a shafukan intanet.
Amber Rudd ta bayyana cewa manhajar na iya gano kashi casa'in da hudu cikin dari na harkokin IS, kuma a na sa ran nan gaba za a kafa dokar da za ta tilastawa kamfanoni amfani da wannan manhaja.







