Darwin Nunez: Liverpool za ta dauki dan kwallon Uruguay daga Benfica

Darwin Nunez

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Darwin Nunez ya ci Liverpool a lokacin da kungiyar Anfield ta yi nasara 3-1, ya kuma ci kwallo a wasan da suka yi 3-3 a Champions League

Liverpool na daf da daukar dan kwallon tawagar Uruguay, Darwin Nunez daga Benfica ta Portugal.

Ana sa ran cinikin zai kai fam miliyan 64 da karin tsarabe-tsaraben da zai kai fam miliyan 21.

Nunez, mai shekara 22 ya ci kwallo 34 a wasa 41 da ya yi wa Benfica a dukkan karawar kakar da aka kammala.

Haka kuma ya ci Liverpool kwallo biyu a Champions League da kungiyar Anfield ta yi nasara a kan Benfica 6-4 gida da waje a kwata fainal.

Har yanzu ba a kai ga gwada lafiyar dan wasan ba, amma daraktan wasanni na Liverpool, Julian Ward yana Portugal don kammala cinikin.

Wasu rahotanni na cewar Manchester United tana son daukar Nunez, wanda Benfica ta saya daga Almeria a 2020 kan fam miliyan 20.5.

Dan wasan da Liverpool ta saya mafi tsada shi ne Virgil van Dijk daga Southampton a 2018, Nunez zai haura kudin da aka dauko dan kasar Netherlands, idan aka hada da kudin tsarabe-tsarabe.

Nunez ya ci wa Benfica kwallo 10 a Champions League, ya kuma jefa 26 a raga da bayar da hudu aka ci a karawa 28 a lik din Portugal da aka karkare a bana.

Ana hangen Nunez idan ya koma Anfield zai maye gurbin Sadio Mane, wanda ya ke kakar karshe a Liverpool, wanda Bayern Munich ke son dauka ruwa a jallo.

Tuni Liverpool ba ta sallama tayin fam miliyan 30 da Bayern Munich ta yi wa dan kasar Senegal, mai shekara 30.

Haka kuma kungiyoyi da yawa na fatan daukar Takumi Minamino, mai shekara 27, dan kasar Japan wanda ta yi wa Farashin fam miliyan 17.